← Book details Budurwar Wawa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 19

Sashe 18

Budurwar Wawa Complete Hausa Novel · about 8 min read

  "Ka yi haƙuri Abbas ba na jin zan iya barin mahaifata, na kuma bar iyayena da suka kawo ni duniya, waɗanda ta sanadinsu ya sa ka ganni da haƙorana talatin da biyu cif har ka nuna ƙauna da soyayyarka gareni, kamar dai yadda na sha faɗa maka mu ci gaba da addu'a wata rana za su amince."

   "Har zuwan wace rana? Sanin kanki ne yanzu mun shafe a ƙalla shekara guda har da watanni amma ana ta abu ɗaya, shawarata ita ce mafita Falmata, ita ce zata bamu damar rayuwa waje ɗaya, mu sake nunawa junanmu yadda muke ƙaunar junanmu, kizo mu gudu mu je mu yi rayuwa mai cike da 'yanci."

   "Ka yi haƙuri, amma wannan ba mafita..."

Shigowar Abbanta ta hanyar turo ɗan ƙaramin ƙyauren gidan da ke jikin babban ya haddasa katsewar kalamanta. Tun da ya hangesu tsaye ya ɗaure fuskarsa har ya ƙaraso inda suke tsaye cirko-cirko.

   "Barka da rana" cewar Abbas yana ɗan rissinawa kaɗan. Yayin da Falmata ke ta faman shafa fuskarta, tana diri-diri alamar mara gaskiya.

  "Ki same ni a ciki" Cewar Abbana yana barin wajen, ba tare da ya amsa gaisuwar Abbas ba.

Yana barin wajen Falmata ta yi wa Abbas sallama ta shige gida da hanzari.

Abbas kuwa taune yatsansa manuniya ya yi, yana mai ƙwafa kafin ya bar wajen.

Ko da ta iske Abban nata a falo ransa a ɓace sosai. Durusawa ta yi ba tare da ta ce uffan ba.

   "Falmata ashe kin yi ƙaurin da maganata za ta zama abar wofantarwa a wajenki?" Faɗin Abba yana kallon fuskar Falmata.

Cikin in-in ta soma magana,

  "Ka yi haƙuri Abba, in sha Allahu ba zan sake ba."

"Ai na fahimci soyayya tana neman rufe miki ido har kika kasa gane bambancin da ke tsakaninmu da shi wanda kike so ɗin. Sai dai ina so ki sani, ba wai ina ƙinki da shi ba ne, sai dai ina so in sama miki darajarki ta ɗiya mace, babu saurayin da zaka bari ya yi ta zuwa zance wajen 'yarka ba tare da manya sun shigo cikin maganar ba, sanin kanki ne tsawon shekara guda ana fama da shi ya turo yaƙi turowa."

  "Ba haka ba ne Abba, in sha Allahu zai turo yanzu ma maganar da muke yi da shi ke nan kuma ta ce idan ya koma gida zai sami..."

  "Ya isa ta shi ki je" ya katseta da faɗin haka.
A hankali ta miƙe ta shige ciki.

Maikosai
08130266650
[4/16, 6:25 AM] Maryam Abduul(Maikosai): BUDURWAR WAWA

©Maiƙosai

  FIRST CLASS WRITERS ASS.

012.

Bayan Sa'o'i Huɗu da suka shuɗewa Salisu a gona.

Aiki yake yi tuƙuru babu ji ba gani. Kamar saukar kwarankwatsa haka ya ji saukar kalmomin wanda ke isar masa da saƙon 'babansa ya yanke jiki ya faɗi' sun saukar masa cikin na'u'ar jinsa. Ya ajjiye fartanyar da sauri ya shuri takalmansa sai hanyar gida.

Yana shiga ya iske dandazon mutane sun kewaye mahaifin nasa tamkar wasu ƙudaje. Wasu na yi masa sannu, wasu kuma na yi masa firfita, yayin da wasu suka kasance 'yan kallo.

Ya kwashi sauri tamkar zai kifa ya kutsa kansa cikin mutanen da suka yanyame mahaifinsa. Daidai saitin kan baba Haladu ya ja tunga ya zauna da sauri ya ɗaga kansa ya aza bisa cinyarsa.

  "Me ya sa meka baba? Don Allah ka ta shi" Ya yi furucin cikin raunin murya.

Ji ya yi wata murya na shelanta masa 'kamar ya mutu baya numfashi' ai kuwa nan take kansa ya soma sara masa ya ɗago da kansa har idanunsa sun soma canza launi.

   "Bai mutu ba! Babana yana nan a raye duk wanda ya sake cewa ya mutu na rantse sai na kashe shi." Tamkar mahaukaci haka ya shiga yi musu sumbatu. Ya shiga cikin tsananin tashin hankalin da ya hana shi taɓuka komai, sai kawai jijjiga baba Haladu da kiran sunansa babu ƙaƙƙautawa.
Shigowar mai gari da liman ya sa mutanen da suka yi musu ƙawanya darewa. Mai gari da liman suka ƙarasa in da baba Haladu da Salisu suke wanda har lokacin yana manne da kan mahaifinsa kan cinyarsa.

   Jin ana ambatar 'a samo ruwa' ya ba shi damar miƙewa a gaggauce ya bazama neman ruwa, ko da ya samo miƙa hannunsa kawai ya yi don bai san wa zai bawa ba sai da liman ya amsa ya gane shi ya yi maganar.

"Bai mutu ba," ya ji maganar liman ta dawo da shi daga duniyar tunanin da ya shige. Ai kuwa sai ya durƙeshe gaban baban da ke shimfiɗe a ƙasa. Liman ya tsiyaya ruwa a cikin tafin hannunsa ya soma shafa fuskar baba haladu har izuwa wuyansa kana ya sake tsiyayawa ya yayyafa masa a fuskar. Ai kuwa cikin sakan ƙalilan da aukuwar haka  baba haladu ya ja dogon numfashi ya fesar. Yayin da Salisu ya cika da ɗumbin murnar ganin mahaifinsa ya dawo daga duniyar da ya tafi.

"Samo mini ruwa Lauwali," Salisu ya yi maganar a gaggauce yana miƙewa tsaye bayan ya dawo daga tunanin da ya cilla.
Cikin sauri Lauwali ya tashi ya kamfato ruwa ya miƙawa Salisu kamar yadda ya buƙata.

   Salisu ya amsa ya yi azamar tsiyaya ruwan cikin tafin hannunsa ya shiga shafawa fuskar baba, kana ya sake tsiyayawa ya yayyafa masa kamar dai yadda yaga liman ya yi wancan karan. Sai dai ga mamakinsa wai kare da tallan tsire ko gezau baba Haladu bai yi balle ma ya buɗe idanunsa. Ganin haka ya bawa Salisu damar sake aikata abin da ya yi da fari shi ma dai shiru kamar an aiki shirwa. Sai kawai ya kamfato ruwan da hannayensa biyu ya kwarawa fuskar baba Haladu  da tunanin zai farka nan ma sai ya ji shiru. Yana shirin ɗaga kwanon ya juye masa akai Lauwali ya riƙe masa hannu, sai jikinsa ya yi laƙwas ya dire kwanon a ƙasa tare da zube guiwoyinsa biyu ƙasa ya fashe da wani irin kuka, tamkar mahaukaci ya shiga sumbatu da yin fatali da kwanon da ke gabansa.

Lauwali ya yi saurin riƙo shi yana manna shi da jikinsa ya riƙe shi gam kana ya ce,
   "Don Allah Salisu ka daina, ka daina kukan nan domin ba zai amfanar da kai komai ba sai wahala,kamata ya yi ka soma nazari da tsinkayen hanyar da zamu bi mu tunkaresu ba wai ka zauna kana risgar kuka ba, ka sani babu maraya sai rago! Mene ne amfanin haka? Shin ka gaza ne?"

Kalaman Lauwali suka saka jikinsa yin sanyi laƙwas, sai Lauwali ya raba shi da jikinsa. Salisu kuwa ji ya yi ya haɗiye kukan da yake yi. Ya miƙe a hankali ya soma tattaki kafin ya tsaya tare da juyowa yana mai fuskantar Lauwali.

  "Har abada ba zan taɓa gajiyawa ba. Kawai ban san ta ina zan faro ba ne shi ya sa. Zuciyata a raunace take, tarin ƙuncin da nake ciki gab suke da sakata ta fashe tamkar fashewar bam, zuciyata a tumbatse take da son ɗaukar fansa, rashin sanin mafita ya sa na kasa taɓuka komai ka ba ni shawara ta ina zan soma?" Ya ƙarasa yana mai zubewa gaban Lauwali tare da riƙo hannayensa.

   "Ban san ta in da zan ɗoraka akai ba Salisu! Amma ba ka ce mini kana da wanda kake da yaƙinin zai taimaka maka ba? To yana ina? A ina zamu same shi?"

  "Tabbas ina da shi, amma ban san in da zan soma nemansa ba"

    "A ina kuka haɗu da shi  Salisu da har kake jin zai iya taimakawa ƙaddarar rayuwarka da ta zabareka ta turkeka tamkar akuryar da aka ɗaure a turken awaki?" Liman ya watsowa Salisu tambaya jin tattaunawar da suke yi.

Salisu ya waigo yana mai bawa liman amsa, "A gidan ɗan kande"
  "Gidan ɗan kande kuma?" Liman ya yi tambayar cike da neman ƙarin bayani.

   "I gidan yarin da aka turani aka rufe ni a can," Salisu ya yi masa sharhi kan maganar.

  "Gidan yari kuma Salisu? A'a Salisu kada ma ka soma kada ka kuskura sam ina rabaka da kiwon kyalla kada ka ce mini sai kyalla ta haihu. kada ka sake jefa kanka in da za ka sake dulmiya, kada ka sake yayumowa kanka sarsarin da zai gitte sauran numfashinka."
Fahimtar in da maganganun liman suka dosa ya sa shi neman buɗe masa komai,

   "Ba yadda kake tunani da hasashe ba ne malam. Shi ɗin mutum ne na daban, mutumin kirki ne, hasalima abin da ya kaishi yana da alaƙa da mutanen ƙauyen nan. Mu ne sanadin shigarsa gidan ɗan kande, amma duk da haka ƙoƙarin taimaka mini yake yi, domin shi ne mutumin da ke taimaka mini wajen rage tunanin halin damuwar da nake ciki."

  "Kana nufin ka ce mini shi mutumin ƙwarai ne wanda yake zaune da kai da zuciya ɗaya?" Liman ya watsawa Salisu tambayar.

   "Ƙwarai kuwa malam! Domin shi ɗin mutumin ƙwarai ne fiye da ni, shi ne ya taimaka mini sosai a gidan yari, shi ne ya dinga faɗi-ta-shi da ƙoƙarin ganin ya share mini hawayena da son daƙilar da zubar hawayena, shi ne ya dinga haƙurƙurtar da zuciyata dare da rana. Ban san da wani irin suna zan kira shi da shi ba, domin ya wuce duk wani suna da zai zo mini."

'Tas ya kwashe abin da ke tsakaninsa da Abubakar ya shaidawa liman.' Liman ya ja wani numfashi kana ya ce,
   "Lallai ya canci da a kira shi da ɗan halak ba kaza mai ci ta goge bakinta ba. Yanzu a ina za mu same shi ko don mu nemi afuwarsa?"

"Ban sani malam domin ban san mazauninsa ba," Salisu ya ce.
  "Tirƙashi! Wannan shi ake kira da ga ƙoshi ga kwanan yunwa," faɗin liman.

  "Salisu ka tuno don Allah, ka yi ƙoƙari ka tuno ko ya taɓa gaya maka sunan in da yake? Ka yi ƙoƙarin tuno wani abu da zai sa mu gane in da yake," Lauwali ya ce da shi yana riƙo tsintsiyar hannunsa.

   "Na kasa, ba zan iya ba," Salisu ya faɗa yana mai ɗan dafe kansa.
   "Ka ga ƙyale shi Lauwali da sannu komai zai zo mana da sauƙi," faɗin liman.
Chapter 18 · 0% Book details