← Book details Budurwar Wawa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 19

Sashe 3

Budurwar Wawa Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dattijuwar ta riƙe haɓa tana mai bin Mama da kallo kafin ta ce,
   "Lallai ne Hajara wata kam wuyanki ya isa yanka,ya yi kaurin da wuƙa za ta iya ratsa shi, har kike faɗamin irin waɗannan maganganun. Har kin manta matsayina gareki,kin mata ko ni ɗin wace ce ko, ko ba komai ai uwa na ke gareki mai son ci-gabanki ke da 'yarki, ki sani yin hakan da nake nufi bai nuna cewar ya ba ki damar cin zarfina ba, kada ki manta wannan abin da kika ɗakko ya kaucewa shari'a, kin san babban kuskuren da kike aikatawa kuwa Hajara?"

Da hanzari Mama ta tareta da faɗin,
  "Ai ni daman na riga na san tatsuniyar gizo ba ta wuce ta ƙoƙi wallahi, matsalata da dattawa irinku kenan maimaita magana, sai ku tsaya ku cije ku kafe akan magana ɗaya kullum babu sauyi, kullum ganinki ba alheri ba ne kekam."

  "Ki faɗi duk abin da kike so Hajara, ki yi duk abin da kike so, amma ki sa ni lalata rayuwar 'yarki da kike shirin yi tabbas babban kuskure ne. Ki taimaki rayuwarku ki dawo da ita hanya mafi inganci domin tsiran gobenku, idan ba haka ba to tabbas gobenku ba za ta yi kyau ba."

***
Tun da ya shigo ya gama shaƙiyancinsa akanta ya fita bata sake jin motsi da ɗoriyarsa ba, sai dai kamar kodayaushe wanda ke kawo mata abinci zai shigo ya ajjiye mata kwano gabanta, idan ta ci sa'a ya fita ya barta haka ba tare da ya gargasa mata muggan kalamai ba, idan kuwa ta taki rashin sa'a ranar harta da kakannin kakanninta sai sun samo nasu rabon, gaba ɗaya duniyar ta sake yi mata zafi, komai ya daina burgeta, ji taki ina ma ana tariyo da agogo baya da babu abin da zai hanata dawo da tsinken bayan rayuwarta ko dan ta gyara kuskuren da ta tafka. Bata da masaniyar a yanzu haka a wani hali mutanen ukun da ta kauracewa suke, duk da wani sashe na zuciyarta na alamta ma ai sun hakura da ita sun sallamawa duniya ita. Idan ba ta manta ba yau take cika wata guda cif babu ɗori a wannan wajen acikin wannan duhun ɗakin wanda ya ci a kira shi da kurkukun azaba. A hankali ta jingina bayanta jikin bangon ɗakin, tare da zubawa rufin ɗakin idanu tamkar mai nazartar wasu al'amura, lokaci guda ƙwaƙwalwarta ta soma kiciniyar tariyo mata abubuwan da suka shuɗe a baya...

***
Garin Kano, yankin Kano ta Kudu, ƙauyen Kura ƙaramar hukumar Kura. Ƙauye ne da ya tara dubbannin mutane, maza da mata; manya da yara. Ƙaramar hukumar da take ƙunshe da makiyaya da manoma. Yawancinsu Manoma ne. Bisa duba da la'akari da cewar yawancin 'yan garin sana'arsu ce noma , su ne suke noma nau'ikan abinci kala-kala kamar su: Shinkafa, Wake, Masara, Barkono, Dankali, Maiwa da sauransu. Su ne ke noma su kuma  yi aikinsu daga nan kuma su fitar da shi ta yadda kayayyakin masarufan ke shigowa cikin birnin  Kano da ma wasu wajajen waɗanda yawancinsu ba mazauna karkara ba ne.
Da yawansu tsofaffin ƙauyen ne suke yin noman. Mutanen da sam ba sa gajiyawa da wannan aikin domin dai don su ga sun noma abincin da al'umma za ta ci.

  Kamar kowacce shekara, cikin wannan shekarar da ake ciki, cikin lokacin da ya kasance na noman abubuwa kamar haka: Masara, Dankali Albasa da alayyahu. Duk da dai ƙauyen cike yake da matsananciyar tarin fargaba da tsananin tsoro da suka gwame zuƙatansu. Dalilin ƙarancin ruwa da kuma takin zamani domin yin nomansu cikin sauƙi. Ba kuma zai iya kaisu ga sun girbe abin da suka shuka ɗin cikin sauƙi ba. Uwa uba yadda zafi ya sake nunkuwa fiye da ƙima babban abin da yafi firgitasu shi ne; irin yadda tafkunan nasu ke ƙafewa. Wanda suna cikin wannan matsalar ce kuma wata gagrumar annoba ta sake yanko musu inda ta yiwa kafatanin ƙauyen dirar mikiya. Yayin da wani attajiri mai matuƙar faɗa aji a ƙasar ya diro musu daga ta sama ya yada zango a kan wasu gonakinsu da labari ya je wa kunnensa akwai yalwataccen ruwa a wajen wanda su kansu manoman ba su farga da haka ba.

Ranar da bin ya wakana, ya kasance ranar ashirin da tara ga watan october, shekarar dubu biyu da ashirin da biyu. Ƙauyen ya yi tsit ba ka jin motsin komai sai kukan tsuntsaye da kuma kaɗawar iska. Yayin da garin ya yi luf da shi, gajimare ya sauya launi ya yi duhu tamkar wanda ruwan sama zai sauka.

Siririya, dogowa kuma ruwan wankan tarwaɗa. A shekaru ba za ta rufa shekara ashirin da uku ba. Jikinta sanye da kaya  babambanta launi. Hakanan zaninta da rigar da kuma fatalar dake ɗaure a kanta duka daban-daban ne.

Tafe take tana 'yar waƙarta, yayin da take kutsa kanta cikin gonakin domin isa ga rafin da shi kaɗai ne ke samar musu da ruwa shi ma ba mai yawa ba. Sauri take kawai dan ta samu damar samun ruwa da za a ɗora musu sanwar abinci da shi. Tamkar wacca aka yiwa wahayi da duban gabanta, haka ta baje magananta kan gonar Baba Haladu, inda ta ci karo da ƙatun-ƙatun ɗin motoci suna haƙe gonar da bai jima da zuba mata irin Maiwa ba. A guje ta juya, sanadin da ya haifar mata da sakin tulun ruwan ƙasa.

  "Baba Haladu wasu na haƙe maka gona" Muryarta ta gauraye bututun kunnen dattawan dake zagaye da Baba Haladu suna masu zantawa game da matsalar da ta tunkarosu na rashin isassun kayan aikin nomar tasu musamman ƙarancin ruwan da ya ketowa ƙaddararsu.

A hanzarce suka miƙe zumbur! Tamkar waɗanda aka zungura da tsinin allura. Kallon kallo suke yiwa junansu tare da kaiwa matashiyar budurwar duba mai cike da tambaya.

"Haƙawa kuma? Su waye?"                           Baba Haladu ya tattaro ƙarfin da yake da shi wajen tambayarta.
  Ta sauke hucin gauron numfashi saboda gudun da ta shawo, kafin ta kai ga basu amsar da ta sanya su shurar takalmansu gami da nufar gonar domin ganewa idanunsu gaskiyar abin da take faɗi.

"Ban sansu ba, sun zo dai da gingimemiyar mota, ita ce ma take haƙe gonar."
Tun da suka isa bakin gonar suka fuskanci lallai akwai wata gagarumar matsala da takeson keto fatar ƙaddarar rayuwarsu.

  "Yallaɓai lafiya kuwa? Meke faruwa?"
Cewar Baba Haladu, yana mai kutsa kansa izuwa ga mutanen dake cikin gonar.

Ba tare da sun kulashi ba, balle har su ba shi amsar tambayar da ya nema suka ci gaba da sassaƙar aikinsu.

Shi kam bai yi ƙasa a guiwa ba domin ance 'durƙusawa wada ba gajiyawa ne ba' ya sake lalubo wata tambayar da ta tilastawa wani daga cikinsu duban shi tare da ba shi amsar,
  "Nan wajen Gwamnati ne, kuma ita ce ta aiko mu."

  "Gwamnati kuma?" Suka ambaya a tare.

"Ƙwarai kuwa" Ya ba  su amsa mai cike da tabbatar musu da haka.

  "Amma nan ɗin fa mallakinmu ne. Shekara da shekaru muna noma a nan, babu wani mahaluƙi da ya taɓa bayyana a gabanmu ya ce mana wajensa ne, hatta da ita kanta gwamnatin. Sai yanzu da muka ji lafazin daga bakinku kuna ambata." Cewar Baba Haladu.

Duk yadda suka so jin gaskiyar al'amarin daga bakin mutanen abin ya ci tura wai kare da gudun layya. Gaba ɗaya ƙauyen cikin tashin tashina yake na tashin hankalin da ya auresu cikin wasu 'yan daƙiƙun mintuna da suka shuɗe. Wanda wannan shi ne sila da masomin abin da ya tarwatsa rayuwarsu da duka farincikinsu. Shi ne dalilin da ya tursasa kowane mahaluƙi dake cikin ƙauyen rungumar baƙar ƙaddararsa. Sun riga sun yardarwa kawunansu cewa 'ko yaushe ƙaddara ita ke yiwa fata zagi' kuma ita ce za ta ci gaba da wanzuwa a garesu har ta ƙarar da rayukansu ɗaya bayan ɗaya.

A hankali yake buɗe tulu-tulun manyan idanuwansa, waɗanda suka yi masa nauyi tamkar an sanya bulo inci tara ciki.
Kallon tsanakin da ya yiwa ɗakin shi ya tabbatar masa da cewa a asibiti yake.

"Ke nan suma na yi aka kawo ni nan?" ya shiga tambayar kansa.
  "Shi kenan kakata ta yanke saƙa." ya furta hakan can cikin ƙasan zuciyarsa.

A hankali ya miƙe daga kwancen da yake zuwa zaune. Ya sanya hannunsa guda ya cizge robar ƙarin ruwan dake saƙale a tsintsiyar hannunsa na dama. Ji ya yi jiri-jiri na barazanar doka shi da ƙasa, sai dai hakan bai hana shi tursasawa ƙafafunsa  ci gaba da rungumar ƙaddarar ɗaukar nauyin jikinsa ba. Take ya doshi hanyar ƙofar ɗakin domin arcewa daga asibitin. Sai dai wani abin mamaki wai kare da tallen tsire da ya dirar masa irin yadda jami'an tsaro suka mamaye ƙofar ɗakin tamkar wasu shazuma mun da suka baibaye sukari ko makamancin haka. Ya san ko giyar wake ya sha ba zai taɓa iya tsallake su ya fice daga cikin asibitin ba. Nan da nan farincikinsa ya sauya tare da komawa baƙin cikin da ya ɗar sar masa cikin maƙoshinsa ji ya yi tamkar ya haɗiye maɗaci. Komawa ya yi ya zauna bayan ya raba idanunsa daga jikin 'yar ƙaramar mahangar dake maƙale jikin ƙofar ɗakin.

Har likita ya shigo ya sake duba shi yana zaune bakin gadon. Duk da tarin tambayoyin da likitan ke yi masa a banza wai jefa agwagwa a ruwa, hakanan duk faɗan da yake yi masa bisa ɗanyen aikin da ya tafka na cire robar ƙarin ruwa bai ji shi ba, bai ma san yana yi ba. Babu abin da yake yi sai aikin tunani, ya gaza taɓuka komai jinsa yake wani soloɓiyo ba zai iya aikata duk wani abu da zuciyarsa ke gindaya masa ba. Gaba ɗaya karsashinsa da kuzarina sun bi iska.

Ya yi zurfi sosai kafin ya iya farauto saurarensa ya kaisu ga likita, wanda ya shiga amsawa likitan tambayoyin da yake aika masa da su sannu a hankali. Duk da cewa a baɗini cikin zuciyarsa yana ƙoƙarin harhaɗa makaman da zai yi amfani da su wajen samo bakin zaren matsalartasa ne.

****
"Yan-yan-yan"

Mama ta ce bayan Dattijuwar ta dire zancen ta.

   "Dan Allah a dinga sauya zance dai, idan kuma har kina da zuciya ba kare ne ya cinye ta ba to kada ki ƙara shigo mana gida."

Ta ƙarasa zancen tana yatsina baki.
Chapter 3 · 0% Book details