← Book details Budurwar Wawa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 19

Sashe 10

Budurwar Wawa Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yini ya yi yana tunani a kan bauɗaɗɗen mafarkin da ya yi jiya da daddare. Wai ga shi dab da zai shiga ƙauyensu, sai kawai wasu ƙarti tamkar ƙirar samudawa suka rirriƙe shi, in da wasu daga cikinsu suka shiga tuttulawa bakin shiga ƙauyen nasu fetur suka cinna ashana. Take ƙauyen ya kama ci da wuta, nan muryoyi mabambanta suka soma yi masa amsa kuwwa cikin mazirarin bututun kunnuwansa, suka shiga neman ɗauki da agajinsa, yayin da ya hango fuskar mahaifinsa da ta Lawisa sun nufo shi jikinsu na ci da wuta suna ɗago masa hannu alamar ya kamasu, in da shi kuma nan take ya soma ihu da kururuwa yana kiran sunayensu.
Ya ja dogon numfashi ta mazirain hancinsa bayan ya tuno irin bahagon mafarkin da ya yi. Yanzu mece ce mafita a gare shi? Ta wace hanya ce zai iya tunkarar ƙauyensu domin ganin halin da suke ciki?"
   "Kai wa kake ma? Salisu kake ko wa?"
Maganar da ta dawo da shi daga tambayar da yake gindayawa kansa ke nan. Ba tare da ya ɗago da kansa ya dubi wanda ke tsaye gabansa yana maganar ba ya miƙe tare da son barin wajen. Duk da yana da yaƙinin cewa ba zai wuce dattijon nan ba.
  "Kai Salisu!" Ya jiyo kira da muryar mutumin cikin wata iriyar siga, al'amarin da ya tilasta masa juyowa ke nan.
Ya tsare Salisu da wani irin kallo kafin ya tuntsire da dariya ya shiga nuna Salisu da yatsa ya ce,
  "Ta yaro kyau ta ke ba ta ƙarko. Kai a tunaninka samun mafitar ƙauyenku ne ya kawoka nan? Kana tunanin za ka iya tsere wa mai gida ne? Ko kana tunanin za ka iya kare wannan ɗan ƙaramin akurkin ƙauyen naku?"
Salisu ya yi wani guntun murmushi tare da daidaita tsayuwarsa sosai yana mai fuskantar dattijon kana ya ce,
   "Tun farkon ganin take-takenka na soma zargin haka a raina da tunani cewa lallai akwai wata a ƙasa. Duk da ko kusa na kasa samun katangar da zan jingina jikinta ta zamo mini mafakar da zan iya inganta hasashena, ashe dai ba mafarki nake yi ba? Ashe dai ban yi ɓatan kai ba? Ina so ka je ka sanar da shi wannan mai gidan naka cewa Salisu ya fi ƙarfinsa, shi da mutanen ƙauyensu. Ka gaya masa Salisu turmin tsakar gida ne, sha lugun mahassada. Hakazalika murucin kan dutse ne bai fito ba sai da ya shirya. Ka sanar masa da yardar Allah sai ƙauyenmu ya kuɓuta daga sharrinsa. Ka gaya masa shi sharri ɗan aike ne, da sannu zai dawo masa har in da yake. Ka gaya masa a shirye nake da na tseratar da rayuwata da ta 'yan ƙauyenmu daga faɗawa rijiya gaba dubu!"
   "Hhh!" Dattijon ya ɓarke da dariya kafin ya sake furta, "Har yau ba ka san waye mai gida ba ko?"
  "Waye shi kuwa? Idan ba mutum ba kamar kowa? Sai me kuma?" Salisu ya ce.
"Tabbas kana wasa da wuta a hannunka, ka sani da sannu kuma za ta babbakeka," cewar dattijo.
Salisu ya yi dariyar gefen baki kana ya ce,
  "Ka sake tuna mini anjima sai na yi dariya," yana gama faɗin haka ya soma tattakawa don barin wajen. Yana jiyo muryar dattijo na sukiburoɗinsa.
Ji yake zuciyarsa na sake tafarfasa, wani hucin baƙinciki na fitowa daga bakinsa. Ya rasa me ya tokarewa mutumin nan da har yake bibiyarsa yake neman hana su shan iskar gaban hantsi? Wani irin kukan zuci ya kufce masa take ya shiga rera shi cikin zuciyarsa. Wani abu ya ji yana nuƙurƙusar zuciyarsa, duk abin da suke yi masa bai dame shi ko ɗaɗara shi da ƙasa ba face irin yadda suka sakawa ƙauyensu ido, kowanne ƙazamin baki da ya tashi furta magana sai ya ce 'ƙauyensu'. Me ya sa sai su? Me ya sa ba za su ƙyalesu haka ba? Ya jima yana karɓar karatun da zuciyarsa ke biya masa kafin ya haye kan gadonsa ya kwanta ba wai don yana jin bacci ba.
   "Ba ka fita ba ne?" Ya jiyo muryar Abubakar na tambayar shi.
Ya miƙe daga kwancen da yake zuwa zaune kafin ya amsa masa da,
  "Ban jima da shigowa ba."
  Abubakar ya durƙusa kusa da shi zucuyarsa fal cike da tausayin Salisu kafin ya ce,
   "Har yanzu baka sanar da ni labarinka ba?" Cewar Abubakar.
  "Na lura ba za ka taɓa iya kwantar da hankalinka ba matsawar ba ka ji ko ni waye ba? Sai dai ina boye sanin ko ni waye ɗin ne saboda sanin waye ni ba zai amfanar da mai sauraro komai ba. Amma ina roƙo da ka bayyanar mini da ko da tausayin ƙarya ne idan ka ji ko ni ɗin wane ne? Ba don komai ba sai don wataƙila haka ya sa ka ji ko ɗan ɗigon tausayina."
  "Me ya sa kake roƙona haka? Me ya sa kake son wani ya tausaya maka bayan ya saurari labarinka? kodayake ban sani ba wataƙila abin da za ka sanar mini mai ɗimautarwa ne shi ya sa kake roƙona, ni kuma ga shi na zaƙu da na ji ko kai ɗin wane ne?" Abubakar ya ce.

****

Sai da ta gama sharɓar kukanta sannan ta mike ta shige ɗan madaidaicin ɗakinta. Kana na kallonta ta yi banza da ita, don ta gaji da abin da ta ɗorawa kanta abin da ba zai haifar mata da komai ba wato son maso wani wanda hausawa ke wa lakabi da 'koshin wahala'

****
   Kano 2021

Ba ta farka ba sai wajejen azahar, bayan an samu likita yazo ya dubata har ma ya jona mata karin ruwa.

A firgice ta farka tana kiran sunan yayarta Asma'u, akan ta dawo bata mutu ba, gaba ɗaya ta zama wata iri duk rarrashin da ake yi mata ji take yi a banza wai agwagwa ta faɗa ruwa.

  "Wai kukan da kike yi shi ne zai sama miki salama Falmata?" Muryar momi mahaifiyarta ta ratsa maɗaukan sautinta, da ido ta soma bin mahaifiyar tasu da kallo, wasu zafafan hawaye na wanke mata fuska.

  "Da gaske momi aunty ta mutu? Da gaske ba zan sake sakata a cikin idanuwana ba?"

  "ƙwarai Falmata, Asma'u ta riga mu gidan gaskiya bamu da ikon da zamu dawo da ita, kuma bamu da ikon da zamu hana faruwar hakan, Allah ya nufa rayuwarta tazo karshe ta hanyar hatsarin da suka yi. Abu ɗaya nake so da ke shi ne ki sakawa zuciyarki salama ko ta wane hali ne, ki riki addu'a ki dinga yi mata domin ita tafi bujata a yanzu haka."

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Me ya sa? Me ya sa haka?" Ta shiga sumbatu wanda har sai da momi ta toshe mata baki, tana mai nusar da ita kuakuren da take son aikatawa.

Maikosai
08130266650
[4/15, 3:12 PM] Maryam Abduul(Maikosai): https://chat.whatsapp.com/CodXIM9nLOXD1QDmW33svF

BUDURWAR WAWA

©Maikosai

08.

2022

Garam! Ta je an turo babban ƙyauren, abin da ya katse mata duniyar labarin rayuwarta da ta faɗa ke nan, bata bi mutumin da ya shigo da kallo ba saboda ta san kowane ne, domin ƙamshin jikinsa kaɗai ya alamta mata haka.

   "Falmata!" Ya kira sunanta da kakkausar murya, wacce ke nuna alamun babu wasu ko kaɗan a maganar da zai yi mata. Ita kuma hakan bai sa ko da kallonsa ta yi ba.

  "Falmata a karo na kusan huɗu zan sake maimaita miki cewa ko kaɗan bana ƙaunar ganinki, bana sonki na tsaneki kuma ba zaki taɓa kubce min ba domin yanzu wasan ya fara, a karo na huɗu ina sake jajjada miki da ki fito min da videon da kika ɗauka, idan ba haka ba wallahi na lahira sai ya fili jin daɗi."

Kallon tsana ta shiga jefa masa mai cike da zallar kiyayya, ba tare da ta ce masa kanzil ba, abin da ya ƙara hassala zuciyarsa ke nan, ya miƙe daga zaunen da yake ya dunfareta a fusace.

"Yau zan tanƙwarar miki da wannan iskancin naki, a yau zan shayar da ke giyar waken da ba ki yi tsammaninta ba."

Tuff! ta tofar da yawun bakinta cike da jin haushinsa ƙasan ranta ta ce,

  "Wane dare ne jemage bai gani ba Abbas? Me yayi saura wanda ba ka yi min ba, don Allah idan har ka cika haifaffe ka kashe ni a yau, a yanzu karka barni da raina."

Cikin fushi da sake hasalar zuciya ya damfareta gadan-gadan yana zuge tazugen wandon jikinsa, ganin haka ya sa wanda ke tsaye kusa da shi fita daga ɗakin, shi kuwa ido rufe ya haye kan ruwan cikinta duk irin yunƙurin da take yi wajen ganin ta ƙwaci kanta ta gaza saboda raunin da jikinta ya yi, haka ya hauta ya yi kiɗansa da rawarsa cike da mugunta kafin ya raba gangar jikinsa da tata. Ko motsi bata iya yi, tana jinsa yana kiran yaronsa.

  "Kar a sake bata abinci har tsawon kwana uku." Yana gama faɗin haka ya gyara wandonsa ya fice da sauri tamkar zai tashi sama.

Lamo ta yi tana jin wani ɗaci na mamaye ilahirin bakinta, bata san me ya sa ƙaddarar nan ke ɗawainiya da ita ba, kodayake ta tabbata kuskuren da ta tafka ne ke bibiyarta, abin da ta shuka ne take girba yanzu.

"Ya Allah!" tayi furucin can ƙasan maƙoshinta. Tana jin yaron nasa na ficewa daga ɗakin ta hanyar jan ƙyauren ya rufe, duhun da take gani ya sake gaurayewa da duhun ɗakin, tana nan kwance ko hannu ta gaza ɗagawa.

***
Washegari Salisu ya riga kowa tashi, dalilin ƙauracewa baccin da ya yi. Sai dai jefi-jefi yakan ji kansa na sara masa tamkar ana dukansa da guduma.
Duk na ci irin na Abubakar wajen son sanin meke damun Salisu ya gaza cim ma haka, haka ya tattara komatsan tambayoyinsa ya watsar gefe guda. Sai dai koyaushe, kowanne lokaci yana ankare da Salisu duk wani motsi na shi yana lura da shi. Ya kuma lura yau ɗin tamkar ba shi da wani kuzari a jikinsa ya rasa meke damun Salisun? Shi kuma kafiya da taurin kai ya hana shi sanar masa.
Chapter 10 · 0% Book details