← Book details Budurwar Wawa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 19

Sashe 7

Budurwar Wawa Complete Hausa Novel · about 8 min read

  "A matuƙar takure nake, a matuƙar dame nake, a matuƙar matsuwa nake, bana jin zan iya kaiwa har cikar waɗannan ranakun. Kwana bakwan nan jinsu nake tamkar kwanakin da zasu tafi da numfashina, jinsu nake yi tamkar kacar da za ta tsinke da sauran rayuwata." Cewar Salisu.

   "Babu yadda za muyi haka dole za mu haƙura har zuwa cikar kwanakin da aka ƙayyadewa kowannenmu."

Bai ce masa komai ba ya koma gefe ya jingina da jikin bangon ɗakin. Ganin haka ya sanya Abubakar furta maganar da ta jima tana yi masa yawo a saman harshensa amma ya gaza bayyanata ga Salisun.

  "Ba ka bani labarin kai wane ne ba? Shin ba za ka bani labarin mutanen da suka zamo silar yankewar farincikinka ba? Shin ba za ka bani labarin mutanen da suka zamo silar tarwatsa rayuwarka ba? Shin ba za ka bani labarin abin da ya zama sababin zuwanka nan ba?"

Salisu ya kalle shi ta gefen ido, tare da yin wani murmushin gefen baki mai cin rai kafin ya ce,
  "Ba yanzu ba, ka bari mu dawo daga wajen cin abinci." Hayewa ya yi kan gadonsa ya kwanta tare da lumshe idanunsa take rayuwarsa ta soma barazanar dawo masa daki-daki, babi bayan babi, haka nan shafi bayan shafi.

"Baba ni ina jin tsoron abin da za su aikatawa Salisu! Zuciyata na yi mini shakku a kan kullen da suka yi masa, tsorona kullum sake yawaita yake yi domin sharrinsu yafi dafin maciji sau dubu"

  "In sha Allahu babu abin da za su iya yi masa. Kuma ai kwanakin da aka ƙayyade masa ya kusa fitowa, mu jirayi zuwan cikar wa'adin kwanakin" Cewar Baba Haldu kenan cikin raunin murya.

"To amma Baba ba ka ganin hakan tamkar..."

"Ya isa haka Lawisa!" Ya faɗa tare da ɗaga mata hannu.

  "Maza ki tafi aikinki. Da yardar Allah Salisu ɗana yana cikin kulawar Ubangiji. Ni damuwata ɗaya yadda mutanen nan suka sanya mu a gaba da jarabarsu"

Ba tare da ta musa masa ba ta miƙe daga tsugunan da take kai gami da numfasawa. Daman zuwa ta yi ta gaishe da shi da kuma jin ta bakinsa a kan lamarin Salisun, ta yadda za ta shigar da kokenta wajen Baba Haladun ko ya taimaki zuciyarta yaje ya gano mata halin da Salisun ke ciki. Sai dai ga shi ba ta yi nasara ba, guiwarta a sare ta bar Baba Haladu. Allah ya sani tana matuƙar kewar Salisunta, tana kuma tsananin tausaya masa musamman yadda ya tsaya kai da fata wajen ganin ya samarwa da ƙauyen na su farinciki. Da ace ita ɗin wata ce da babu ko shakka da kanta, da kuma hannunta za ta hukunta mutanen da suka tarwatsa rayuwarsu da farincikinsu, suka kuma garƙame Salisunta akan abin da bai ji ba bai gani ba saboda tsabagen mugunta da soyayyar kawunansu da ta yi musu zabari ta turkesu.

Kowannensu riƙe yake da tasar abinci. Dogon layi ne da shi  zai sadaka da inda za ka karɓarwa kanka abin sanyawa a cikinka.

  Tamkar walƙiya haka Salisu ya ji ya fice daga cikin jerin gwanun layin karɓar abincin har ya yi sanadin da ya ganshi kwance ƙasa wanwar yayin da tasar abincin dake hannunsa ta yi nata wuri.

  Tuni ya ji zuciyarsa na tafarfasa tamkar tafasar ruwa a kan wuta. Ba yau ne farkon al'amarin ba, ya kuma rasa dalilin da ya sa suke masa wannan cin kashin? A kan me? Me ya aikata musu? Me ya sa ba za su barshi ya ji da abin da ke addabar zuciyarsa ba? Da ido yake bin Dattijon dake tsaye cikin layin wajen da ya fitar da shi yana sakar masa wani ƙayataccen murmushi. Miƙewa ya yi tare kyakkyaɓe jikinsa gami da ɗaukar tasar abincin tasa ya dawo izuwa cikin layin, wanda tuni hargitsi ya so  ɓarkewa tsakanin Salisu da mutanen Dattijon.

Tuni ya ji kansa na juyawa saboda tsananin zafin da ya ziyare shi lokaci guda. Allah ya sani shaida ne gareshi shi ba masifafe ba ne, ba zai iya da wannan rikicin ba. Gefe guda kuma zuciyarsa na tunasar da shi cewa shi fa yanzu na ƙauyensu ne duk wani rikicinsa akan ƙauyensu zai yi wannan ya sa ya janye jikinsa a hankali ya bar wajen.

  Ji yayi sam abincin ma baya gabansa, ba ya jin zai iya sanyawa cikinsa komai duk kuwa da irin kukan yunwar da yake ji hanjin cikinsa na yi.
A hankali yake jefa sawayensa har ya kai kan wani teburi da kusan koyaushe nan yake zama shi kaɗai ya ci abincinsa ba tare da ya shiga sabgar kowa ba.

  Farauto mishi kwanon abincin da idanunsa suka yi ya tilastawa hankalinsa kaiwa ga wanda ya ajjiye masa abincin.

  "Ka ci wannan" Cewar Abubakar dake tsaye gabansa.

Binsa kawai  yake yi da kallo tamkar wani gaula kafin ya iya buɗe ɓakinsa da ya yi masa matuƙar nauyi ya ce,
  "A ƙoshe nake"

Abubakar na shirin yin magana ya yi hanzarin daƙilar da shi ta hanyar sake furta,
"Ni yanzu damuwata ɗaya na ganni a waje ina shaƙar iskar ƙauyenmu, na ganni ɗauke da sabon mukullin buɗe wata sabuwar ƙofar rayuwata da ta ƙauyena."

  "Ka yi haƙuri Salisu! Ka ci gaba da karanta ayoyin haƙuri ga zuciyarka. Tabbas wata rana za ka bar nan."

Cikin wata iriyar murya, cikin wani amo mara daɗi ya ce
"Da jini suke rubuta ƙaddararmu suke liƙeta Abubakar. Me ya sa sai mu? Me ya sa sai gonakinmu? Me ya sa sai ƙauyenmu? Mene ne duk wannan ɗin?" Me ya sa carbin rayuwarmu yake son tsinkewa?" Ya ƙarasa maganar fuskarsa damuwa bayyane ƙarara.

  "Ka ci abincin ina zuwa"
Abubakar ya ce yana mai juyawa ba tare da ya ba shi amsar tambayoyin da ya jera masa ba. Shi kam Salisu da ido kawai yake bin Abubakar ɗin.

Tsaye yake jikin wata katanga sai waiwaye-waiwaye yake yi da san tabbatar da babu wanda ke lura da shi. Waya ya ciro daga cikin wani ɗan rami dake jikin bangon da yake jingine. Ya soma sanya mata layin da ya zaro cikin tazuginsa. Ya kunnata bayan ya haɗata, gami da kai yatsansa kan wata lamba kana ya soma yin rubutu da nufin tura saƙo izuwa ga lambar.

"Komai yana tafiya daidai maigida yadda ka tsara" Ya tura tare da saurin wargaza wayar gami da mayar da ita ma'ajiyarta.

"Me kake a nan kuma Abubakar?"
Sautin muryar Salisu ta dake dodon kunnuwansa. Al'amarin da ya haifar masa da girgizar zuciya da jiki. Wani gumi ya shiga keto masa saman goshinsa, daman shi mara gaskiya ko a ruwa yake sai ya yi gumi.

Tamkar wani mara laka haka ya juyo da jikinsa ya fuskanci Salisu. Tsoro gami da fargaba suka ɗarsarwa zuciyarsa.
Tashin hankali, gobarar gemu! Bai san ma ta ina zai soma amsawa Salisu tambayar ba saboda gaba ɗaya ya rasa nutsuwarsa.

Da ƙyar ya iya kalato murmushin ƙarfin hali, muryarsa na barazanar san tona masa asiri ya ce,
  "Am babu komai Salis, muje ko?"
Salisu ya gyaɗa masa kai gami da yin gaba ta hanyar juyawa Abubakar ɗin baya. Shi kam gogan naka na ganin haka ya sauke wata wahalalliyar ɓoyayyiyar ajiyar zuciya.

  Maikosai
08130266650    
[4/12, 8:33 AM] My number: https://chat.whatsapp.com/CodXIM9nLOXD1QDmW33svF

BUDURWAR WAWA

©Maikosai

    FIRST CLASS WRITERS ASA.

05.

7:30am

Hayaniya ce ta tasheta, sai faman jan tsuka take yi, har ga Allah koke koken da suke shiga maɗaukan sautinta sun addabeta, sai kuma zargi da tunanin mai ke faruwa haka ya sa ta hanzarin ficewa daga ɗakin zuwa falo, turus ta yi ganin mutane zaune, ga mahaifiyarsu na sharar ƙwalla, tsakiya kuma gawa ce an lulluɓeta da zani. Ƙafafuwanta ne suka soma gaza ɗaukar nauyinta, da ƙyar da siɗin goshi ta ƙarasa tsakiya inda gawar take a hankali takai hannu ta soma yaye lullubin da ya rufe fuskar gawar, daram ta koma ta zauna hawaye suka soma malalo mata saman kuncinta. Hannu na rawa ta sake yaye mayafin take kukan da take riƙewa ya kufce mata ta shiga rerawa.

Kuka take yi kamar wata zautacciya, jikinta na sake mutuwa gabaɗaya ta yi rauni.

   "Me ya sa yaya? Me ya sa zaki min haka? Don Allah ki tashi ki faɗa musu baki mutu ba don Allah"

Wata matace ta riƙota ganin yadda ta soma jijjiga gawar Asma'u.

  "Ki yi haƙuri Falmata, kowace rai zata ɗanɗani mutuwa, muma duk zamu mutu ki yi mata addu'a ita kaɗai tafi buƙata daga gareki."

Ba ta san ma matar na yi ba, har aka zo ɗaukar gawar nan ta miƙe a zabure tamkar wata mai aljanu ta soma kiciniyar hana su fita da gawar, da ƙyar aka riƙota sai dai tuni ta zube numfashinta ya ɗauke.

****
Su Zuhra

Daidai wani banki motarsu ta samu matsaya. Bata bi shi ba illa shi kaɗai da ya fito daga motar ya tattaka ya nufi wajen ATM Machine ɗin don cirar kuɗin da yakeso.

Da sauri ta ciro wayarta ta turawa mama saon kar-ta-kwana. Tana ganin nufuwarsa ta gyara zamanta tare da mazewa tamkar mai gaskiya.

Ɗora mata damin kuɗin yayi saman cinyarta yana murmushi.

Waro idanuwanta tayi, kafin ta ce,

  "Dear wannan ai yafi yadda na ce."

  "Akan buƙatarki zan iya kashe ko nawa ne. Wannan ba komai ba ne masoyiya naira dubu ɗari biyar ne ki ɗau adadin kuɗin da aka ce ragowar ayi wata sabgar da su."

Waro idanu ta sake yi, kamar wacce kuɗin suka gigita nan kuwa duk cikin salo ne. Ta miƙa hannu ta ɗau kuɗin, ta zare wani abu daga ciki, ta soma ƙoƙarin maido masa da sauran.

  "A'a baby kar muyi haka da ke, muddin idan ba so kike yi na yi fushi da ke ba." yayi maganar cike da hanzari, yana tsuke fuska.

Rausayar da murya tayi, kafin ta ce,

  "Haba my bash, ashe zaka iya fushi da ni da man?"

  "Indai akan mama ne ba, ai hakan na so ki nuna min mahaifitarki ce ita kaɗai banda ni"

  "A'a ni bance ba." Tayi maganar da sauri.

   "To bana so karki kuma, muje in saukeki a asibitin ko?"

Nan take ta hau inda-inda, kasancewar da man mara gaskiya shi ko a ruwa yake sai ya yi gumi, da ƙyar ta iya saita kanta ta soma bin sa da wani gafalallen kallo mai kashe jiki ta ce.
Chapter 7 · 0% Book details