← Book details Budurwar Wawa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 19

Sashe 6

Budurwar Wawa Complete Hausa Novel · about 8 min read

***
"Tabbas! Akwai abubuwan da suke ƙwarzanar rayuwarka. Ban sanka ba, ni ma baka sanni ba kawai ƙaddara ce ta gwama kawunanmu. Sai dai ni ina ji ajikina cewa lallai akwai wani alheri mai tarin yawa da zai gifto tsakaninmu."
Bai bawa Salisu damar yin magana ba, ya shaƙi iska kana ya ɗora da,
  "Suna na Abubakar Yusuf. Mazaunin garin Haɗeja wanda karatu ya kawo shi jihar Kano. Sai dai ban sani ba ashe ƙaddarata ce ke ɗawainiya da ni har ta farauto rayuwata izuwa wannan garin. Ƙaddarar da na gwammace sahhalewar numfashina a madadinta. Na kasance ɗalibi mai karantar ilimin abin da ya shafi tsirrai wanda a turance ake kiransa da Botany. Wanda ta zurfaffen nazari da bincike da nake na gano wani sinadari da idan har manoma za su yi amfani da shi za su amfana da shi sosai zai kuma sake inganta musu amfanin gonar ta su. Sai dai bayan na kammala zurfaffen binciken nawa na tattara bayanaina na damƙawa wani babban malaminmu da yake ɗaukarmu darasin. Ya matuƙar jinjinawa ƙwazona sai dai ya gargaɗeni kan da na tsuke bakina kada na yarda wani ya san da batun. Kamar yadda ya buƙata hakan na yi, inda na ja bakina na gumtse shi ban bari kowa ya san da zancen ba, yayin da agefe guda nake sake faɗaɗa binciken nawa tare da faɗawa zurfaffen tunanin samo hanyar da zan yi sinadarin ya isa ga manoma dake zaune a ƙauyuka domin su ingata nomansu.
  Abin da ban sani ba shi ne; Tuni malamin ya bayyana wannan binciken nawa da kuma sinadarin ga manyansa, manya masu faɗa a ji, waɗanda suke da ƙarfin iko. Inda ya kai musu bayanin komai filla-filla wanda take na gano lallai ya ci amanata ya siyarwa da manyan ƙasa shi domin su amfana da shi ba talakawa ba. Ganin haka ya sa na tunkareshi gaba da gaba na yi masa magana, nan take kuma ya bayyana mini shaiɗancinsa da mummunan ƙudurinsa dake narke cikin zuciyarsa abin da ya ci mini tuwo a ƙwarya kenan. Ke nan su talakawa ba mutane ba ne? Ke nan su ba halittun da za a ji tausayinsu da jin ƙansu ba? Me ya sa sam manya ba sa tausayin ƙananunsu? Me ya sa ake raina baiwa da fikirar manoma? Ya shaida mini da na dakatar da duk wani bincike nawa, na kuma ci gaba da gumtse bakina, idan har kuwa na kuskura na ce zan fitar da sirrin to fa na kwana da sanin cewa shayi ruwa ne wasu 'yan sinadarai ya samu ya sauya suna, kuma tabbas na lahira zai fini jin daɗi domin zan haƙawa kaina ramin mutuwa ta ne, dan haka na tuna da cewa jiki yana tsira ne idan kunnuwa suka kiyaye gargaɗi.
Tun daga lokacin na soma fafutukar ganin yadda zan kai wannan sirrina nawa ga manoma, kuma tun daga lokacin ne na soma fuskantar wasu barazanai. Duk inda na je mutanensu na biye da ni, saboda kawai ba sa so na bayyana wannan sirrin, saboda kawai ba sa so sirrin da na gano ya taimaki talakawa. Hatta da wajen kwanana sune zagaye da ni, makaranta da duk wani waje da zan tunkara suna biye da ni. Kowane motsina kan idanuwansu yake, kowane zancena cikin kunnuwansu yake. Kwatsam wata ranar Laraba, da misalin tara da rabi na daren ranar na kai izuwa ga wani ɗan ƙaramin ƙauye wanda na ɗauki sinadarin na damƙa musu tare da bayyana musu irin tarin alfanun da sinadarin yake da shi.
Sun amsa hannu bibbiyu, sun yi godiya sosai. Sai dai ashe ni ban sani ba na yi shuka a idon makwarwa ne domin ni da na sakankance cewar a wannan ranar sun yi balagoro babu wanda ke bina ashe busasshen hasashe na yi, ashe babban kuskure na tafka dan kuwa suna matuƙar ankare dani, wanda nan da nan suka sanarwa da manyansu waɗanda suke yiwa aikin. Ban san ta yaya aka yi ba? Ban san ta ina aka sauya sinadarin da na sha matuƙar wahala da tarin gwagwarmaya wajen samar da shi ba har na damƙashi ga mutanen ƙauyen. Suka sauya wannan haɗin sinadarin daga mai yiwuwa zuwa mara yiwuwa, domin manoman sun yi amfani da shi sai dai ya gurɓata musu amfanin gonartasu , nan suka shigar da ƙarata bisa jagorancin wani mutumi wanda nake kyautata zaton shi ne mai farautar rayuwata, aka ba su lauya wanda ya jajirce ya kuma tsaya musu, aka gabatar da shaidun ƙarya a kaina da kuma tabbatarwa da koto cewa sinadarin na bogi ne, tun farkon samar da shi da na yi aka umarce ni da na dakata amma na yi kunnen uwar shegu. Nan take koto ta yanke mini hukuncin zaman gidan kaso na tsawon wata biyu tare da tara mai tsananin gaske, da kuma dakatar da binciken abin da nake yi tun da ba shi da alfanu a cikin al'umma musamman ma su manoman da nake yi dan su.
Tik! Tik! Tik! Kamar ana dukan bayan ƙwarya da sillan kara, haka yaji labarin Abubakar na ratsa kowace kwanyar kansa. Domin ji ya yi labarin na masa kamanceceniya da wani al'amari da ya sani, wanda ya faru da ƙauyensu a lokacin da ya kasance ya nisanta da ƙauyen, bayan komawarsa ya ji mummunan labarin da kuma yadda komai ya wakana. Kaddai ace da gaske shi ne mutumin da suke magana a kansa? Kaddai a ce shi ne wanda ke son taimakawa ƙauyensu amma reshe ya juye da mujiya? Jin Abubakar ɗin ya yi shiru ya ba shi damar fuskantarshi sosai har yana mai tanƙwashe ƙafafuwansa, tare da zube duk wata nutsuwarshi gareshi kana ya ce,
  "Wane irin sindari ne haka? Yaya sunan ƙauyen da ka kaiwa sinadarin?" Ya jefa masa tambayoyin a lokaci guda.

***
Tun da tabar gidan ranta ke sosuwa, tana jin wani ƙullutun abu na zagaye maƙwallatonta, ta rasa yadda zata ɓullowa da lamarin Hajara, ta rasa yadda zata fahimtar da ita kuskuren da take tafkawa, a haka har ta ƙarasa gida.

Tana shiga ta iske wata matashiyar budurwa zaune ta rafka uban tagumi, hawaye na sauka bisa kuncinta.

Sallamar dattijuwarce ya sata ɗago kanta tare da saurin sanya hannu ta soma ƙoƙarin goge hawayen saman fuskarta, sai dai tuni ta makaro domin datijuwar ta riga ta ga hawayen da kuma damuwar da take ciki.

  "Kaka sannu da zuwa" ta ce murya a ɗan raunace.

    "Yauwa sannu sarauniyar kuka da ɗorawa kai dala babu gammo" cewar kaka.

Cuno baki ta yi, kafin ta ce,

   "Kuka kuma kaka? Ni fa ba kukan da nake yi."

  "Ke tafi can ware, wai ke yaushe za ki yi zuciyane akan wani ɗa namiji ki zauna kina sharar hawaye wallahi kin yi asara dai."

   "Ni fa kaka ba kuka nake yi ba."

    "To mene ne? Na ce mene ne saman ƙundugugin fuskarki? Ba ga idanun naki nan sun sauya launi ba."

  "Tsakuwa ce ta faɗa min a ido fa shi ne kika ga kamar ina kuka..."

  "Ke tafi can ki bani guri, ki zauna kina zubar masa da hawaye ya gano lagonki kin ga ya sake samun damar da zai sake wulaƙantaki." Faɗin kaka tana shigewa ɗaki, zuciyarta na sake cunkushewa, damuwa biyu na sake yi mata katutu.

****
   Kano 2021

Tun da motarsu ta tashi suke waya da Shahid, bini-bini ya tambayeta komai lafiya ko? Haka ma ɓangaren Falmata takan kirata jefi-jefi.

Kwananta biyu acan suka jiyo sai dawo tasowar dab da magrib suka yi, wanda kafin su iso zasu iya kaiwa dare sosai.

Kwance Falmata take tana danne-danne a wayarta, tana dariya wani lokacin kuma ta ja tsaki. Ji ta yi ana ƙwanƙwasa ƙofar ɗakinta, shiru tayi da tunanin waye a wannan farkon daren? Sai dai jin muryar Shahid ya sa ta ajjiye wayar ta miƙe da nufin tashi, kiran da ya shigo wayarta shi ya katse mata ƙoƙarin kaiwa bakin ƙofar ɗakin, da hanzari ta dawo da ɗau wayar wanda tuni tasa ta manta da wanda ke buga mata ƙofar. Ba ita ta gama wayar ba sai wajen sha biyu, nan ta soma ƙoƙarin kiran wayar yayarta ta ji ko ta shigo gidan sai dai taƙi tafiya, hakan yasa ta watsar da wayar gefe da faɗin da safe sa gana da juna, don ta gaji ga kuma dare yayi bazata iya fita yanzu ba hasalima bacci ne ke ɗawainiya da ita.

***
"Kamar yadda na shaida maka tun a baya, sinadari ne dake ingata kayan noma, yadda manoma za su girɓe abin da suka shuka cikin sauƙi kuma abin gwanin ban sha'awa. Idan ban manta ba sunan ƙauyen Kura"

Ɗii! Ɗii! Ɗii! ya ji ƙirjinsa ya bayar da sautin hakan tamkar kukan mashin. Tabbas ƙwarai shi ne. To amma ta yaya aka haihu a ragaya?  Idan kuwa haka ne tabbas matsalarsa ta zo ƙarshe domin kuwa yana ganin a yanzu ne zai ɗaura ɗamba wajen ƙwatowa ƙauyen nasu 'yancinsu. Haka kawai sai yaji ya aminta da shi, ya kalli Abubakar ɗin tare da furta,
  "Ka yi haƙuri a madadin mutanen wancan ƙauyen. Sannan ina so na nemi wani taimako a wajenka"

  "Uhm! Ina jinka mece ce matsalarka?" Cewar Abubakar.
  "Ina so mu haɗa hannu da kai mu ceto wancan ƙauyen daga hannun waɗancan azzaluman"
Sai da ya yi jim, tare da numfasawa gami da sunkuyar da kansa ƙasa kafin ya ɗago kana ya ce,
   "Babu komai yiwa kaine. To amma ta yaya zamu iya tserewa daga wannan wajen? Duk da cewa ni saura kwana uku na bar gidan" Ya ƙarasa cike da tambayarsa.

  "Ni ma tunanin da na jima yana cimin rai kenan, gaba ɗaya raina da lissafina a matuƙar dagule suke, ciwon rai kawai nake yi bisa zaluncin da aka yiwa ƙauyenmu, so nake ko ta halin ƙaƙa naga na bar wannan wajen amma na rasa mafita." ya ƙarasa faɗa tamkar zai fashe da kuka, zuciyarsa a cunkushe hakanan muryarsa a raunace.

  "Mafita ɗaya ce" cewar Abubakar.

"Mece ce mafitar?" Ya tambaye shi cike da zaƙuwar son jin amsar da zai ba shi.

     "Mu ajjiye duk wani makaminmu mu bari har zuwa ranar fitarmu" Abubakar ya ce.
Chapter 6 · 0% Book details