← Book details Budurwar Wawa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 19

Sashe 5

Budurwar Wawa Complete Hausa Novel · about 5 min read

"To ƙafar yawo, sai kuma ga shi kina da exam ba. Duk da dai ni ma bana so ka kaɗan na ga mun yi nesa da juna."

Dariya Falmata ta saka, kafin ta iya furta,

  "Ashe dai ba ni ce kaɗai bana son muyi nesan ba, amma aunty ke da an kawo magana sai ki yi ta wani zizzillewa"

" To yaya zanyi amma dai na san tabbas zan yi kewarku."

  "Babu wata kewarmu da za ki yi hajiya, nan na ce inkaiki da kaina kika tubure ke dai za ki tafi a motar haya shi ne za a yi kewarmu alhalin tun yanzu an fara nuna mana wariyar launin fata?" Cewar Shahid ke nan hankalinsa na kan tuƙin da yake yi.

"Yo kai ko kwana zanyi ina maka bayani ai ba fahimta za ka yi ba, ni dai ka jamu a hankali kada ka janyo min takabar da babu shiri."

"Hoho wallahi aunty kina sonsa da yawa fa, to mene ne don ya tafi ya barki ba sai ki sake auren wani ba ga maza nan da yawa burjik a gari..."

Hannu Asma'u ta kai ta gwaɓe mata baki.

  "Ai ke da yake ba ki san darajar soyayya ba shi ya sa.

  "Ni kuwa na santa aunty, ni da nake da Hashim ɗina."

  "Zaki rufe min baki ko sai na tattakaki."

  "Yanzu Falmata da man ba kya sona kike min fatan mutuwa" ya katse musu hirar da jefa mata tambayar.

  "Ni fa bance ba yaya, kawai gani na yi duk ta bi ta wani damu, yo idan tafiyarce bata so gudun ta yi nesa da kai ta haƙura mana."

   "Ai shi ke nan, tun da dai yanzu kin nuna min matsayina."

   "Ni fa ba haka nake nudi ba, ai in sha Allahu sai ka yi shekaru ɗari a duniya."

  "Ki ce na takwarkwashe ke nan?"

  "Wai wayaganka a lokacin ka zama tamusasshe." Cewar Asma'u tana dariya.

Gabaɗayansu suka saki dariya, daidai lokacin da suka ƙaraso tasha. Tamkar karsu rabo ba su bar tashar ba sai da suka ga ɗagawar motar su Asma'u kasancewar kamar ita ake jira ta zo su tafi. A hanya suna tafe shi da Falmata suna kewar Asma'u, Falmata nata mitar wannan cikas ɗin da exam ɗinta ta kawo mata, shi kuwa mita yake yi akan aikin da ya sanya shi a gaba har ya ja masa katanga da bin Asma'u.

***
Yau saura kwanaki takwas ya bar magarƙamar da aka je aka ajjiye shi a can. Sai dai bayajin zai iya jurar cikar waɗannan kwanakin bai je yaga ahlinsa ba, bai je yaga ƙauyensa ba da yadda yake ciki. Kwata-kwata ma sai yaji duniyar da abin da ke cikinta sun gimshe shi.
Likita na fita ya sake miƙewa kan gudaduginsa, duk da cewa suna son bijirewa umarninsa amma haka ya tilasta musu har suka tsaya waje ɗaya. So yake kawai yaga ya kere, so yake kawai yaga ya bar asibitin koma ta halin ƙaƙane, sai dai shi akaran kansa ya san ba shi da wata dabara domin ganganci kawai yake son haifarwa da kansa.
Kwanansa guda a asibitin aka sallame shi. Wanda kai tsaye gidan yari suka zarce. Ko da wannan saurayin ya ganshi ya yi matuƙar jindaɗi duba da ya ganshi ya warke tas da shi, duk da idan ka kalli yanayinsa da fuskarsa za ka tabbatarwa da kanka cewa lallai yana cikin matsananciyar damuwa domin kuwa 'labarin zuciya a tambayi fuska'.
  "Don Allah meke damunka?" Saurayin ya jefa masa tambayar da sai da ta sanya Salisu kallon shi.
  "Meke damuna?" Salisu ya maimaita tambayar tare da yin nuni da kansa.
Maikosai
08130266650
[4/10, 12:20 PM] My number: https://chat.whatsapp.com/CodXIM9nLOXD1QDmW33svF

BUDURWAR WAWA

   FIRST CLASS WRITERS ASS.

©Mai kosai

04.

    Kano 2022

Zuhra ta jingina kanta jikin kujerar motar da take zaune ciki, tana mai fitar da hucin iska daga bakinta.

  "Bashir juya mu koma store ɗin nan, zan mayar da kayan nan su ba ni kuɗin."

Ta yi furucin tana lumshe idanuwanta biyu.

Bashir da ke wana kan sitiyarin motar ya juyo yana kallonta kana ya ce,
   "Me ya faru babyna? Me ya sa?"

  "Saboda buƙatar hakan ta taso ne da gaggawa."

  Ta ba shi amsa, har lokacin idanuwanta suna a rufe.

  "Zuhra baby, ba zai yiwu ba. Ko da ace mun koma ba za su amshi kayan ba, ka da ki manta store ne fa ke ko kasuwa ce ba za su amsa ba ciniki ya riga ya faɗa. Ki sanar da ni mece ce matsalarki? Me ce damuwar?"

Ta buɗe idanuwanta,tare da sakin numfashi, ta sake saita kanta dan kar shirin da take son yi ya kwance zani ta ce,

   "Yanzu wayar da ka ji ina yi , har ina cewa Mama me ya faru? To ba Mama ba ce ba, wata maƙociyarmu ce ke sanar da ni Mama ta yanke jiki ta faɗi, an kaita asibiti an ce ana buƙatar kuɗi masu ɗan yawa, ban san ya zan yi ba, ga shi ina son mahaifiyata ita kaɗai ce gareni sai kai. Shi yasa na ce maka mu juya."

Ya yi dariya sosai kafin ya ce,
  "Wannan ce kawai buƙtar ta ki shi ne za ki ɗaga hankalinki ki sa na daina ganin walwalar da ke shimfiɗe saman fuskarki?"

Ya ɗan nisa kana ya ci gaba da faɗin,
    "To kwantar da hankalinki ,domin kuwa kema kin san kina da ni. Har nawa ne kuɗi  da ake da buƙata haka?"

  "Ta ce min dubu hamsin ne, ban da kuɗin gado kuma."

Ya daki kan sitiyarin da yake wana shi haɗi da faɗin,

   "Oh shit! Yanzu fisabilillahi a kan wannan kika shiga damuwa? Mahaifiyarki ai ni ma mahaifiya ta ce, mu je banki na ciro miki kuɗin."

  Ta yi wani far da idanuwanta kana ta ce,
   "Na gode sosai babyna. Shi yasa kullum nake ƙara sonka, sonka sake nunkuwa yake cikin zuciyata domin kai ɗin na musamman ne daban kake da sauran maza. Domin kuwa in dai ina cikin damuwa to sai ka san yadda ka yi kaga na fice daga cikinta, na gode da kulawa my"

Murmusawa ya yi kafin ya ce,
  "No mind babyna, ai ke ɗin ruhina ce shi yasa, dan haka matsalarki matsalata ce."
Chapter 5 · 0% Book details