Sashe 13
Budurwar Wawa Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya ɗan numfasa kana ya sake cewa,
"Shi ke nan amma ina so ka sani shi cin hanci da rashawa da kake magana akansa ai sai wanda yake da zuciyar ci ne yake karɓa, idan ɗan Adam ya tsarkake zuciyarsa ga barin cin haram to babu abin da zai janyo shi ga cin abin da yafi ƙarfinsa ko abin da zai janyo masa baƙin jini a wajen Allah da ma mutanen duniya."
Shi dai Salisu bai ce masa komai ba, sai ma shimfiɗe gangar jikinsa da ya yi bisa saman gadonsa da yake kai a zaune. Ya runtse idanunsa wanda take suka soma hasko masa wasu kwanaki da suka shuɗe cikin rayuwarsa kafin zuwan wannan ranar.
Gari ya yi tsit sakamakon rana da ta daɗe da zuwa maɓoyarta, wata ya maye gurbinta, taurari sun yi wa sararin samaniya ƙawanya. kowane lafiyayyen bil'adama dare mahuta ne a gare shi, a lokacin da kowanne mahluƙi ke kwance ya yada haƙarƙarinsa yana bacci domin samawa ruhi da gangar jiki hutu. Shi kuma Salisu yana zaune ya haɗa kai da guiwa yana tunanin ko a wane hali ƙauyensu ke ciki a yanzu?
Wani tuƙuƙin baƙinciki ne ke nuƙurƙusar zuciyarsa, yayin da maƙwallaton da ke fatar wuyansa ke dukan sama da ƙasa yana tsalle tamkar zai keto fatar wuyansa ya fito saboda tsananin takaici, baƙinciki da ƙuncin da ke mamaye da ruhinsa. A kullum burinsa da fatansa bai wuce a ce yau ga shi ya bar wannan gidan ba, kodayake babu komai Allah yana tare da bayinsa masu haƙuri da taƙwa. Ya ingantarwa kansa cewa 'lallai wata rana sai labari' ya san dai ba zai taɓa dawwama a cikin gidan ba, ba kuma zai taɓa dawwama da ƙuncin cikin ruhinsa ba.
Ya rumtse idanuwansa da suka yi ficin-ficin da su saboda tsabagen baccin da ke cinsu amma an hana su runtsawa.
Da misalin ƙarfe takwas na safe, a ranar sha shida ga watan nuwamba, shekarar dubu biyu da ashirin da biyu.(16 November, 2022.) Suna cikin koto gaban alƙali, in da suke ƙarar wasu mutane kan gonakinsu, wanda cikin iko da ƙudurar Allah alƙali ya ƙwato musu gonakin da kuma shimfiɗawa waɗancan gargaɗi. Waɗannan kalamai na alƙali ba ƙaramin sanyaya zuƙatan mutanen ƙauyen suka yi ba, musamman ma shi da shi ne ya jagoranci ƙarar.
Suna tsaka da wannan farincikin ne na zama sakakku daga tarkon da aka yi musu, wani tashin hankali ya sake rufto musu in da 'yansanda suka yi musu dirar mikiya, aka ɗakko shi daga ƙauyensu aka shigar da shi ofishin 'yansanda wanda baya ƙarƙashin yankinsu, aka kuma gurfanar da shi gaban alƙali wanda a nan ne ya ji maganar da ta samar masa da giɓi gami da tarin baƙinciki a zuciyarsa. 'Ana tuhumarsa da karɓar maƙudan kuɗaɗe waɗanda aka sato su daga bankin Eco sati guda da ya wuce baya.' Tabbas ya san ya karɓi jakar kuɗin da suka nuna hoton karɓarta a matsayin hujja sai dai ko kaɗan bai san cewa gadar zare ce aka shirya masa ba. Kuɗin da an ba shi sune saboda a siye zuƙatan mutanen ƙauyensu akan su bar musu gonakin, ya ci alwashin mayar musu da kuɗin don suna nan ya ajjiye bai taɓa ko sisi ba amma sai ga shi an ƙulla masa zaren da bai san ta ina zai soma ƙoƙarin kwance shi ba. Ya sani yana da masaniya da kuma labarin irin ta'asar da aka yi wa bankin amma Allah ne shaidarsa shi ko hanya ma bai haɗa da su ba. Amma shi ne suke cewa 'shi ne shugaban ɓarayin, wai shi ne ya shirya ta'asar' Ya rushe da wani irin matsanancin kuka yana sake tuna ranar da abun ya kasance ma suna zaune shi da wani mutumi, in da mutumin ya kunna rediyo ke nan aka soma labarai wanda anan ne suka ji ta'asar da ɓarayin suka yi wa bankin. Ba tare da ya kula ruwan hawayen da suke ta saraftu kan kuncinsa ba ya ja dogon numfashi haɗi da zuƙe majinar da ta ziraro masa daga cikin mazirarin hancinsa.
"Ba ka kwanta ba har yanzu?" Ya tsinkayo muryar Abubakar cikin bututun kunnensa na tambayarsa.
A hankali ya ɗaga kansa, ya kai manyan idanunsa kan fuskar Abubakar ba tare da ya iya ba shi amsa ba.
"Me ya sa baka kwanta ba? Kamar kuka kake yi ko Salisu? Me ya sa?" Abubakar ya sake jera masa wasu tambayoyin ba tare da ya ji amsar Salisu ta farko ba.
Sai da ya nisa kaɗan kafin ya iya mayar masa da amsa,
"Bacci ya riga ya jima da ƙauracewa idanuwana. Ko kaɗan ba na jin zan iya sanya haƙarƙarina kan wannan ƙarfen gadon domin na kwanta na yi bacci da nufin hutu ko jin daɗi."
Abubakar ya matso kusa da shi a hankali, cikin maƙalalliyar murya ta mai bacci ya ce,
"Don Allah ka cire damuwa, ka kwantar da hankalinka da izinin Allah babu abin da zai same mutanen ƙauyenku."
"Da gaske kake?" Cewar Salisu har yana harɗe harshe wajen saurin faɗa.
"Ba ni da tabbaci, amma in sha Allahu ahlinka na tsare cikin kariyar Ubangiji mai kowa mai komai."
Bai san sanda ya saki wani gajeran murmushin farincikin jin zantukan Abubakar ba. Ya sake kafe idanun Abubakar da kallo yayin da Abubakar ya yi hanzarin sauke idanunsa ƙasa.
"Ka kwanta, bari naje na yi accawi(fitsari)," cewar Abubakar yana mai ƙoƙarin barin ɗakin. Cikin sanyin jiki Salisu ya kai haƙarƙarinsa kan saman gadon da yake zaune gefensa ya kwanta har yana mai yin matashi da sangalalan hannunsa tare da lumshe idanunsa. Sai dai sam baya jin bacci ko kaɗan, ba kuma ya jin cewar zai iya yin baccin ko da ace shi baccin ya ziyarce shi.
Yana jiyo motsin fitar Abubakar sai dai ba ya jin zai iya buɗe idanunsa ya hangi ficewarsa. Duk da cikin zuciyarsa na wassafo masa tambayoyi mabambanta a game da Abubakar ɗin, don ya lura kwana biyu kamar yana ɓoye masa wani abu, yana kuma yawan ganin shi a keɓantaccen wuri kamar mara gaskiya yana yi masa wasu abubuwa daban da ya kasa gane in da ya dosa.
Maikosai
08130266650
[4/15, 3:17 PM] Maryam Abduul(Maikosai): https://chat.whatsapp.com/CodXIM9nLOXD1QDmW33svF
BUDURWAR WAWA
©Maikosai
FCW
09.
A hargitse tamkar wata zautacciya ta shiga gidan sai cika take tana batsewa. Mama da ke zaune saman kujerar tsuguno ta yi azamar miƙewa tsaye tana bin Zuhra da kallo.
"Ke lafiya? kanki ƙalau kika shigo ko sallama?"
Kamar zata rufe maman da duka cike da hargowa ta soma faɗin,
"Mama wai me ya sa wasu mutanen ba su da zuciya a ƙirjinsu ne?"
"Me ya faru? Ki sanar da ni kin sankani a duhu"
"Wancan ɗan iskan ne mana mama, me zan yi masa ya gane akwai bambanci tsakanina da shi"
"Waye ki faɗa min kina sake jefani a duhu fa."
Siririyar tsuka ta ja kafin ta ce,
"Waye kuwa ban da shashashancen Abdullatif yake ko talib"
Tsaki mama ta ja, tana kamo hannunta tare da zaunar da ita kan kujerar da ta tashi.
"Shi ne duk kika bi kika tayar da hankalinki akan wancen gaulan wanda bai da sanin duniya. Sau nawa zance ke daina barin damuwa na neman samun gurbi a zuciyarki."
"Mama na tsane shi bana sonsa ko kaɗan, ina jin tamkar na kashe shi har lahira."
***
Salisu ya jima kafin ya farka, don sai da ya kwashi awanni kusan goma kafin ya iya buɗe idanunsa. Lokacin da ya buɗe babu kowa a kusa da shi, domin Abubakar ya koma ɗakinsu.
A hankali ya miƙe zaune ya soma riƙe kansa da hannunsa na dama, duk da cewa wannan karan babu komai a jone a jikin hannun nasa. Ya ziro ƙafafuwansa tare da son miƙewa tsaye, a daidai nan ne likita ya turo ƙofar ɗakin ya shigo.
Ya ƙaraso in da yake cikin nutsuwa sai da ya buɗe fayal ɗinsa da ke ajjiye saman wata ƙaramar durowa kusa da gado kana ya kalle shi gami da furta,
"Sannu, yanzu me ke yi maka ciwo?" Ya tambayi Salisu.
Salisu ya sake dafe kansa da ke tsananin sara masa kamar mai koyan magana haka ya buɗe bakinsa da ƙyar ya furta,
"Kaina ne kawai ke ciwo, kuma shi ma na san zai daina."
Likita ya kalle shi kamar mai nazarin wani abu kafin ya kai ga furta, "Tabbas zai warke, to amma fa sai idan ka cire damuwa da yawan tunani sannan ne za ka iya rabuwa da shi. Sannan dole ne ka cire komai a ranka domin ka samu ka yi isasshen baccin da zai sakawa gangar jikinka ƙosasshiyar lafiya. Domin gab kake da iya kamuwa da ciwon damuwa, kuma hakan yana da matuƙar hatsari."
Sai kawai ya soma bin likita da kallo kamar wanda bai taɓa ganin shi ba ko wanda ya ga mahaukaci. Ji yake yi likita ya ba shi wani gagarumin aiki, domin sam ya san ba zai taɓa iya daina tunani a game a ƙauyensu ba. Zuciyarsa da komai nasa sun tsaya cak ne a kan ɗaukar fansar da zai yi kan mugayen mutanen da suka tarwatsa farincikinsu. Ta yaya ma likita zai ce ya daina tunani? Ina sam haka ma ba za taɓa saɓuwa ba.
"Kana ji na ko?" Likita ya ce cikin sigar tambaya, don ya lura da Salisu tamkar baya jinsa ya cilla duniyar tunani.
Kai kawai ya iya ɗaga masa ba tare da ya ce masa komai ba. Nan likita ya sake duba shi gami da sake ba shi magunguna kafin ya fita. Yana fita kuwa Salisu ya sake komawa gidan jiya, domin babu abin da ya zurma yi irin tunanin yadda zai samu ya je ga ƙauyensa. Ya ɗau tsawon lokaci yana tunanin da ya kasa samo mafitarsa, har sai da ya ji kansa na wani irin sarawa sannan ya koma kan gado ya kwanta tare da lumshe idanuwansa.
Alhamdulillah! Jikin Salisu da sauƙi, domin har likita ya sallame shi ya koma ɗakinsu. Duk da dai sai da ya sake gargaɗinsa akan lallai ya rage yawan tunani da saka damuwa a ransa, idan ba haka ba kuma ya janyowa kansa wasu matsalolin da za su saka ya yi ta yawaita kwanciya kan gadon asibiti.
"Ya kamata a ce ka watsar da makaman yaƙinka Salisu," cewar Abubakar yana mai zama kusa da shi.