← Book details Budurwar Wawa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 19

Sashe 14

Budurwar Wawa Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ya yi shiru na wasu sakanni kafin ya kai ga buɗe bakinsa gami da bawa Abubakar amsa, "Ko kaɗan, sam ba na jin zan iya ajjiye duk wasu kayan farauta ta wa abin da nake farautar. Ina so na sanar maka da cewa yanzu na fara, yanzu ne yaƙin zai soma domin na yi rantsuwa da girman zatin Allah matsawar wani abu ya sami  ahlina to ba zan bari zaluncin da aka yi musu ya tashi a tutar babu ba."

  "Kana ganin haka shi ne mafita?" Abubakar ya tambaye shi.

  Ko bai zama mafita ba, to tabbas zai zamo kariyarmu domin zan nuna musu ni ba na tsoron ta mutu balle ta yi rai. Ban kuma damu ba wai an yakushi kakkausa ga duk wani abin da zai same ni domin wutar ɗaukar fansa ce ke ruruwa a cikin zuciyata."

  "Ka yi haƙuri Salisu, ka mayar da komai ba komai ba, domin shi faɗan da yafi ƙarfinka wasa kake mayar da shi. Kar ka manta idan har ba ka ci naman kura ba, ita ta ci naka!"

Salisu ya kafe shi da idanuwansa ba tare da ya ce masa komai ba har na tsawon wasu daƙiƙu.

"Gobe wa'adina zai cika," Abubakar ya katse musu shirun tare da kawar da idanunsa daga cikin na Salisu.

"Na taya ka murna," Salisu ya ce.
"Na gode. Me kake tsarawa a game da yaƙin da kake son tunkara?" Abubakar ya ce.
  "Me ya sa kake son sani?" Salisu ya tambaye shi.

"Don na samu sanin da wani abu zan yi mana shiri na irin abubuwan da zamu tanada"

Salisu ya miƙe tsaye ya yi tattaki na wasu 'yan sakanni kafin ya koma bakin gado ya zauna yana haɗiye wani dunƙulallen yawu tare da sakin wani irin gauron numfashi. Ya daɗe a haka kafin ya iya furtawa Abubakar, "Za ka iya sama mini ɗan jarida? Za ka iya tanadar mini wayar salular da zan yi amfani da ita wajen tarwatsa rayuwar azzalumin can?"

Abubakar ya kalle shi duba na tsanaki yayin da fuskarsa ke ɗauki da mamaki kana ya ce, "Me za ka yi da su?"

  "Ina so na tarwatsa rayuwarsa kamar yadda ka ji na ambata a baya, ba ni da wani buri da ya wuce na ɗauki fansar halin ƙaƙaniyar da ya jefa ni, ina son na saka rayuwarsa cikin ƙunci na tarwatsa masa farincikinsa. Zan yi amfani da su wajen bankaɗo masa sirrinsa duniya ta san ko shi wane ne da kuma irin zaluncin da yake yi. Yadda bai ji kunyar lalata mana rayuwa ba saboda son abin duniyarsa ni ma ba zan ji nauyi da kunyar tona masa asiri ba, zan nuna masa cewa ni haifaffe ne kuma ɗan halak."

  Abubakar ya dube shi yana jinjina kafiya da na cinsa.

   "Ba zan hanaka ɗaukar fansar da kake son yi ba, domin ko hausawa na cewa 'rama cuta ga macuci ibada' amma ka sani ba kasafai mutum ke samun cikar muradinsa ga abin da yake so ba. Wai ma shin na tambayeka? Waye shi wannan mutumin da kake ta magana akansa? Shin za ka iya shaidawa duniya fuskarsa da kuma cikakken sunansa ne da har kake iƙirarin za ka gwabza da shi? Idan ban manta ba a labarinka ka sanar da ni ba ka san shi ba, ba ka ma taɓa cin karo da fuskarsa ba, to ta yaya za ka iya gayawa duniya cewa ga mutumin da ya yi wa rayuwarku kutse nan?" Ya ƙarasa yana kallon Salisu.

    "Tun ran gini, tun ran zane na riga na gama yanke hukuncina, shi ya sa komai ka ga ina yi yake tafiyar mini daidai Abubakar, domin a shirye nake tsaf sa'ilin da zan fito gabzawata da abokin karawa. Tun lokacin da na soma ƙoƙarin gina tubalina na san in da na dosa, na riga na san wace wainar zan toya. Rashin saninsa da kuma sanin fuskarsa ba matsalata ba ce, domin ne iya fuskar da nake hangosa da shi cikin zuciyata ma kaɗai ya wadatar."

***
"Oh ni abu ni kam yau naga takaina, wai ba zaki fito daga ɗakin nan ba kin shige kin ƙunshe kai kamar wata daddawar ɗaka" cewar kaka tamkar zata tashi sama saboda faɗa.

Da ƙyar kalaman kaka suka ratsa kunuwan Fa'iza ta jiyo bambamin da take yi saboda tsabagen nutsewar da ta yi cikin kogin tunanin sahibul ƙalbinta, da sauri ta amsa,

  "Na'am kaka gani nan fitowa"

  "Karki fito ki zauna tunanin banza da wofi har yaje ya karki a banza wallahi babu ruwana ci gaba da rayuwata zanyi  kamar bamu taɓa rayuwa tare da ke ba."

  "Gani kaka" ta ce lokacin da ta iske kakar tsakar gida tana sake mitar shegewarta ɗaka da kuma halin da ta jefa kanta ciki, halin da ba shi da wani inganci.

   "Yo ai na ganki, kin san aikin ba sai na nanata ba, kin ga Fa'iza ki fita hancina karki ƙara cika min hanci da shirmenki wallahi akan na waccen watsattsiyar da bata san ciwon kanta ba."

Murmushi ta yi domin ta fahimci inda maganar kaka ta dosa, cikin sanyin jiki ta wuce kicin ta soma kiciniyar ɗora tuwon dare. Sai da ta tabbatar ta yi ruɗe sannan ta dawo kusa da kaka ta zauna tana ƙarasa tankaɗe sauran garin da zata yi amfani da shi wajen yin tuƙi.

   "Don Allah kaka ki fita al'amarinsu, tunda sunce basa sonmu ba sai mu ƙyalesu ba, duniya ce ta ishi kowa riga da wando."

"Hmm! Ke yarinya ce ba za ki gane abin da nake son yi ba, idan na tuna Habibullah nakan zubar da ƙwalla ba dan komai sai don takaicina ɗaya yau ɗiyarsa ce ke kan wata turba turbar da mutane ke alla wadai da ita."

"Na san da ciwo kaka, na san da zafi amma haka zaki daure ki fice a sabgarsu, ni dai wallahi karsu zo su haddasa miki hawan jini haka kawai su rabani da ke."

  "To na ji 'yar nema, za ki ci gaba da aikin gabanki ko kuwa?"

Dariya ta yi mai 'yar karamar sauti, ta ci gaba da tankaɗen tana tsokanar kaka, ganin Fa'iza na neman zautar da ita ya sa ta tattara komatsanta ta shige ɗaki ta bar mata wajen.

***
A kausashe Salisu ya shiga ba shi amsa da,

"Da fuskar azzaluman da suke tsintar kansu cikin wutar jahannama," Ya ɗan nisa kaɗan kana ya sake furta, "Shin za ka taimaka mini ko kuwa?"

   "Ba ni da burin da ya wuce na taimaka maka, don haka ka sa a ranka an gama komai. Zan tanadar maka su kamar yadda ka buƙata har zuwa ranar da za ka fito mu sake yin ido huɗu da juna," cewar Abubakar yana kallon Salisu.

"Na gode," Salisu ya ce.
Tsawon mintuna biyu babu wanda ya sake magana cikinsu, haka ne ya bawa Abubakar damar miƙewa gami da ficewa daga ɗakin. In da Salisu ya jinginar da kansa jikin ƙarfen gado yana mai rufe idanunsa biyu. Take ya soma tuna wata tattaunawa da ta kutsa tsakaninsa da Lawisa sa'ilin da take roƙonsa akan ya daure ya yi karatu ko don ya samu ya barta ta yi saboda yadda take jin gidan rediyon da take saurara na faɗin muhimmancin neman ilimi. Ya tuna irin amsar da ya ba ta da 'ta yi haƙuri su ci gaba da nomansu wacca ita ce tushensu tunda idan an yi karatunma ba aiki ake samu ba'. Ya tuna amsar da ba shi da cewa 'shi ilimi ba don ayi aiki ake nemansa ba kamar dai yadda gidan rediyon ke faɗa'. Amma ya yi watsi da maganganunta. Lalle da ya sani ya ɗauki maganar Lawisa, yanzu ga shi rashin ilimin ya sa ya rasa wata dama da ta zo mi shi kodayake da man da na sani ƙeya ce wacce ke a baya' ya yi zancen duk cikin zuciyarsa.
Ɓangaren Abubakar kuwa yana fita ya zarce in da ya saba zuwa kusan koyaushe. 

Saƙo ya shiga rubutawa kamar haka: "Mai gida akwai matsala. Domin yana gab da ruguza duk wani lissafi naku, yana gab da rusa duk wani shiri naku, duk ƙoƙarin da kuke yi akai wajen ganin kun saka shi ya manta da matsalarsa domin ku mallaki abin da kuke da muradi to gab yake da ya rushe wannan ƙoƙarin naku. Idan ku a zaune kuke yin komai to shi a tafe yake. Domin yana gab da mayar muku da hannun agogo baya." Ya yi saurin turawa tare da wargaza wayar kamar yadda yake yi ya mayar da ita mazauninta, kana ya bar wajen.
Salisu kuwa ya jima a haka kafin ya shimfiɗe saman gado, kallon kowane motsi na mutanen da ke ɗakin yake yi, yana jin kowacce murya na faɗin son ranta. 'Kowa da kiwon da ya karɓe shi, inji mai akuya ya sayi Kura' Ya ayyana haka cikin ransa, shi kuma nasa irin kiwon ke nan ba irin na sauran mutanen ɗakin ba, ji yadda yake ta wulagigi, ji yadda irin tasa ƙaddarar ta zo masa take jijjiga shi tamkar ana jijjige jijiyar bishiya, kullum du'a'insa kada Allah ya sa ya mutu yana cikin wannan halin ba tare da duniya ta san irin baƙin zaluncin da aka ƙunsa musu ba.

  Washegari ya tashi da wata iriyar mutuwar jiki. Haka kawai yake jinsa wani iri, yayin da ƙirjinsa ke dukan uku-uku, bugun zuciyarsa na sake yawaita. Duk da yana danganta haka da rashin da ya yi na Abubakar, wanda ya tafi yau. 'Sabo turken wawa' ya ce yana sake jinjina irin yadda ya ji lokaci ɗaya ya kasa samun nutsuwa da tafiyar Abubakar, yana kuma jinjina irin yadda har suka yi sabon da bai ji daɗin nesan da ya yi masa ba. Mutumin da shi kaɗai ne ke ɗebe masa kewa, yake ɗebe masa kaso tamanin cikin ɗari na tarin damuwar da ta yi masa ƙatutu ta katange hasken rayuwarsa. Ya ji babu daɗi sosai musamman lokacin da Abubakar ke yi masa sallama, ya yi baƙinciki sosai ganin yadda idan ya rufe idanunsa ya buɗe baya saka Abubakar cikin maganansa, ya yi takaicin fitar Abubakar daga cikin gidan.

Maikosai
08130266650
[4/15, 3:19 PM] Maryam Abduul(Maikosai): https://chat.whatsapp.com/CodXIM9nLOXD1QDmW33svF
BUDURWAR WAWA

©Maikosai

   FIRST CLASS WRITERS ASS.

10.
Chapter 14 · 0% Book details