← Book details Budurwar Wawa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 19

Sashe 11

Budurwar Wawa Complete Hausa Novel · about 8 min read

Salisu kuwa jin irin yadda ciwon kan nasa ke sake ta'azzara ya saka shi shigewa ɗakinsu domin ya ɗan huta. Sai dai ko da ya shiga ɗakin ba hutawa yake yi ba tunani ne kawai ya cika kwanyar kansa ya tarar masa ya masa katutuwa ya hana shi runtsawa ko kaɗan.

  'Haƙurin dai Salisu! Ka ci gaba da haƙurƙurtar da zuciyarka. Ka ci gaba da dasa mata irin ban haƙuri da sannu za ka girbe shi wannan haƙurin za ka samu kyakkyawan sakamako daga jiran tsammanin warabbukan da ka jima kana yi. Ka sani mahaƙurci mawadaci. Kuma tilas ne wata rana ya dafa dutse har ya sha romansa.' Karatun da zuciyarsa ke ta biya masa ke nan. Gaba ɗaya ya takure kansa da ƙwaƙwalwarsa da tunanin samo mafitar da zai bi ya tseratar da rayukan mutanen ƙauyensu.
Ya jima yana kissime-kissime da tunanin abubuwan da zai yi don kuɓutar da ƙauyen da kuma gonakinsu. Bai san adadin mintuna ko awannin da ya kwasa ba yana fama da tunanin da ya dabaibaye shi. Jin ciwon kan nasa na sake tsanani da bunƙasa ya tilasta masa dafe kan. Tuni ya ji juwa na ɗibarsa, yana jin iska na jujjuya shi tamkar hajijiya, nan da nan idanuwansa suka soma lumshewa yayin da ya soma ganin dishi-dishi.

Sannu a hankali yake buɗe idanunsa tamkar mai koyo. Tas ya waresu kan fuskar Abubakar da ke zaune gefen gadon da yake kai a kwance. So yake yaga ya yinƙura ya miƙe zaune amma ya kasa domin ji ya yi wani abu ya ɗaure masa jijiyoyin jikinsa tamau.

  "Sannu ka tashi? Bari na kirawo likita." Abubakar ya ce, tare da miƙewa don kiran likita ba tare da ya jira jin amsar Salisu ba.
Sai a sa'ilin Salisu ya soma nazarin ɗakin da yake ciki. Ya ɗau lokaci mai tsawo tare da rarrabe ido kafin ya iya fahimtar in da yake. Kamar dai waccan rashin lafiyar da ya yi ya farka ya ganshi a kan gadon asibiti, sai dai ya lura da bambanci domin wannan karan bai fita daga cikin gidan kurkukun ba yana cikin kilinik(clinic) ɗin gidan yarin saboda a wancan karan likitan da yake duba marasa lafiya  ba ya nan shi ya sa har aka fita da shi asibitin waje. Ya kai idanunsa kan hannunshi da ya ji shi tamkar a saƙale. Nan take ya yi arba da robar ƙarin ruwa a hannunsa da aka jona, wanda ga dukkan alamu ya kusa ƙarewa. Ƙoƙarin cizge robar ruwan yake yi aka turo ƙofa. Abubakar da likita ne suka shigo, yayin da Abubakar ya yi hanzarin ƙarasawa wajen Salisu da yake kiciniyar son fizge robar ƙarin ruwan tare da faɗin,
  "Me kake yi ne haka?"

Ba tare da ya kalli Abubakar ba balle ya ba shi amsar tambayar da ya yi masa ya sake kaiwa robar cafka tamkar maye yaga abincinsa. Ganin haka ya saka likita zuƙulƙula masa allurar baccin da ya gama haɗata, cikin abin da bai fi sakan biyu ba zuwa uku ya soma lumshe idanunsa a hankali jikinsa ya saki.

  "Allurar bacci ka yi masa likita?" Abubakar ya tambaye shi.

  "I, ita ce, domin yana da buƙatar ya samu wadataccen bacci duk da banso na biyo ta wannan hanyar ba."

   "Ko me ya sa?" Abubakar ya sake kai masa wata tambayar.
Likita bai ba shi amsa ba, sai ma gyara wa Salisu robar ruwan da ya yi, kana ya juya da nufin fita yana mai furta,
   "Biyo ni muje ofis."

Ba tare da ya musawa likita ba ya miƙe ya mara masa baya.
Ɗaki ne ɗan ƙarami madaidaici a cikin falon ɗakin da aka kwantar da Salisu.

  "Likita meke damunsa ne?" Cewar Abubakar yana kallon likita.

Tsawon shuɗewar adadin sakanni zuwa mintuna kafin likita ya ajjiye biron da ke hannunsa  yana rubutu cikin wani fayal(file), kana ya kai fitilar ganinsa ga Abubakar ya ce,
  "Gab yake da kamuwa da cutar Depression wacca hausawa ke kira da 'Damuwa' duk da dai bai cancanci akira ita wannan cuta ta 'Depression' da kalmar 'Damuwa' ba, sai dai kasancewar hausawa sun kasa sanin yadda za su kira wannan cutar a hausance ya sa suka ba ta sunan 'Damuwa' a dunƙule dai a iya kiranta da 'Psychological Problem' wato 'cutar ƙwaƙwalwa' duba da yadda take raunata ƙwaƙwalwa har mutum yakan ji yana wasu abubuwan daban kamar: saurin fushi, saurin hasala, zafin rai, haka nan mutum yakan ji ya ƙosa da wannan rayuwar duniyar a ganinsa abu na ƙarshe da zai yi shi ne ya kashe kansa ya huta. Daɗin daɗawa kuma yana ɗauke da ciwon hawan jini wanda a yanzu haka jininsa ya hau abubuwan nan biyu su suka taru suka sabbaba masa halin da yake ciki. Uwa uba kuma yawan takure kansa da yake yi wajen yin tunani, da kuma rashin samun wadataccen bacci. Domin alal haƙiƙa bacci na da maruƙar muhimmanci ga rayuwar ɗan Adam, sai dai da yawa mutane kan wofantar da wannan muhimmancin nasa saboda rashin sanin darajarsa. Kamar yadda masana suke cewa 'Idan babu bacci rayuwa ba za ta cika ba'. Hakanan Hausawa na cewa, 'Dare mahutar bawa' kuma wannan yana da alaƙa da dare da Allah ya yi domin ayi bacci a huta."

Ya tsahiyarta ya gyara zama sannan ya ci gaba, "Bacci wani abinci ne da ɗan Adam kan bawa jikinsa, kuma wata hanya ce ta gina lafiyar ƙwaƙwalwa da samun ƙoshin lafiya. Rashin samun isasshen bacci kan sauya rayuwar mutum, ƙwaƙwalwarsa za ta sauya kuma aikinta zai canza, kamar yadda masana lafiyar ƙwaƙwalwa suka bayyana. Hukumar lafiya ta Birtaniya NHS a wani cikakken bayani da ta yi game da muhimmancin bacci, fa'idarsa da illolinsa. Ta ce 'Mutum ɗaya cikin uku suna fama da matsalar bacci tare da damuwa da kuma yin aiki ba hutu. Binciken ya ce 'bacci yana da muhimmanci ga lafiyar ɗan Adam domin yana warkarwa da gyara zuciya da jijiyoyin jini. Kuma rashinsa na da alaƙa da hatsarin manyan cututtuka da suka shafi zuciya da ƙoda da hawan jini da ciwon suga da kuma mutuwar jiki."

  "Ke nan mai fama da ciwon suga, ƙoda, hawan jini da mutuwar jiki duk dalilin rashin yin isasshen bacci na iya haddasa masa samuwarsu?" Abubakar ya yi tambayar cike da fuskar mamaki.

"Ƙwarai kuwa! Ai illolin rashin samun isasahen bacci na da yawa, domin rashin samun wadataccen bacci yana iya hana haihuwa. Domin binciken NHS ya ce, 'bacci na ƙara ƙarfin jima'i rashinsa kuma na hana haihuwa'. Don haka samun isasshen bacci yana da muhimmanci ga ɗorewar rayuwa cikin ƙoshin lafiya da kuma aiwatar da jin daɗin rayuwa." Likita ya ɗan tsahiyarta, wanda samuwar haka ya bawa Abubakar damar yi wa likita tambayar da ta zo masa.

  "To mene ne duk yake janyo haka likita?"

Likita ya muskuta kana ya ce, "Dalilai masu yawa ke janyo rashin samun bacci, domin dalilin yafi ƙarfin ace ɓacin rai ne kawai ko damuwa da kuma rashin mayar da hankali.  A wata tattaunawa da na gani a shafin BBC wacca aka yi da masanin lafiyar ƙwaƙwalwa Dr. Shehu Saleh shugaban asibitin masu fama da lalurar taɓin ƙwaƙwalwa ta Kware jihar Sokoto a Nijeriya in da ya yi bayani kan muhimmanci da illolin bacci ga lafiyar ɗan Adam. Ya ce,'Baccin da mutum yake buƙata ya danganta da shekarunsa, domin wasu suna buƙatar da yawa wasu kuma kaɗan ya wadatar da su. Kowane ɗan Adam akwai awannin da ya kamata ya samu isasshen bacci a kullum bisa ga shekarun haihuwarsa. Abin da yake da muhimmanci shi ne mutum ya gano adadin baccin da yake buƙata kuma ya yi ƙoƙarin samun baccin domin ƙoshin lafiyarsa. Kamar yara ƙanana suna bacci kusan awa ashirin(20) a yini daga cikin awa ashirin da huɗu(24) a kullum. Yaran da suka tasa suna iya baccin awa goma sha takwas(18), magidanta da waɗanda suka haura shekara goma sha takwas suna buƙatar aƙalla awa takwas(8) domin samun wadataccen bacci. Wanda kuma suka haura shekara sittin zuwa saba'in awa shida(6) zuwa huɗu(4) ya ishesu. Idan kowane rukuni na shekaru ya samu wadataccen bacci zai kasance sun ƙara samun ƙarfi da ƙoshin lafiya a washegari idan ba haka ba akwai sauyi da matsaloli da yawa da zasu fuskanta. Wanda idan mutum ya tashi daga bacci yana jin kasala kuma daga baya ya ji kamar yana jin bacci, haka alamu ne da ke nuna mutum bai samu isasshen bacci ba. Domin bacci magani ne na matsaloli da dama na lafiyar ɗan Adam, kuma akwai abubuwan da bacci ke ƙarawa kamar su: Inganta garkuwan jiki, ƙara lafiyar ƙwaƙwalwa, ƙara ƙarfin jima'i, riga kafi ga ciwon zuciya da suga, yana sa mutum ya samu nutsuwa, sannan yana gina tunanin mutum."

"Me ya sa ya zama bacci na iya haddasa rashin haihuwa da raunata ƙarfin jima'i kama yadda na ji kana ta ambata likita?" Abubakar ya sake wurga masa tambaya.

Likita ya muskuta gami da zare gilashin da ke manne saman fuskarsa kana ya ce,
  "A binciken lafiya ya nuna cewa 'rashin samun isasshen bacci yana ragewa maza da mata sha'awar jima'i da kuma rage ƙarfinsa.' Haka kuma rashin samun wadataccen bacci na ɗaya daga cikin illolin da ke janyo wahalar samun haihuwa ga maza da mata. Domin rashin samun wadataccen bacci na iya zama sanadin rashin haihuwa saboda yadda yake rage ƙwayoyin halitta na haihuwa."

"To kuma likita shin akwai wani abu da ke iya faruwa da mutum idan baya bacci? Duba da yadda za kaga wasu mutanen ba sa iya yin bacci kamar yadda ake da buƙata," cewar Abubakar cikin sigar tambaya.
Chapter 11 · 0% Book details