← Book details Budurwar Wawa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 19

Sashe 17

Budurwar Wawa Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Salisu wai me kake yi ne haka a ɗaki tun ɗazu ina ta kiranka kaƙi fitowa?"  Ya tsinkayo muryar mahaifinsa baba Haladu na koɗa masa kira. A gaggauce ya yi azamar fitowa daga ɗakin bayan ya ajjiye fartanyar da ke hannunsa.

     "Gani baba," ya ce yana mai ɗan rissinawa.

  Baba Haladu ya dube shi kana ya ce, "Yau ba za ka je cikin gari ba?"
Salisu ya yi ɗan jim kafin ya kai ga bawa mahaifin nasa amsa, "Baba na daina zuwa."

   "Ko me ya sa?"

    "Babu abin da yake kaini cikin gari face gararanba baba, shi ya sa na ce na dakatar da zuwa tunda banga amfanin shigarsa ba," Salisu ya ba shi amsa cikin nutsuwa.

   "Amma ai da ka kama sana'a a can ko? Kana ganin duk sa'o'inka wasu na cikin garin sun kama abin yi, wasu kuma ma ba sa gari gaba ɗaya sun je yawon neman kuɗi," faɗin baba Haladu.

  "Baba bana son wannan yawan sam. Gwara na zauna na yi nomata itama ai sana'a ce ba sai ta kai ga naje ga yin bara ko aikin bauta ga wasu ba sannan na sami abin rufawa kaina asiri ba."

    "Kayya dai! Ai ba sana'a ce wacca mutum zai ba ta duka amanna ba, su kuwa ai ba bara suke yi suke samun ɗan taronsu ba. Kana ganin dai yadda wani lokaci ma asarar abin da muka girɓe muke yi. Gwamnati ta wofantar da mu, ba ta wadata mu da isassun kayan aikin noma, idan mun girɓe kayan kuma wani sa'in a siyesu da ƙasƙanci ba a duba cewa muma mutane ne masu neman na kansu wannan ce sana'ar?" Ya ƙarasa cikin wani irin takaici da jefawa Salisu tambaya.

Ya sani rashin ba su muhimmanci ya jima yana dukan ran mahaifinsa, da sauran mutanen ƙauyenma to amma yaya za su yi? A hankali ya shiga mayarwa da baban nasa amsa,
   "Duk da haka baba noma ai tana da tarin albarkatai, domin Allah da kansa ya sanya mata albarka shi ya sa duk abin da ɗan Adam zai shuka na noma to sai ya yi albarka. Baba kaɗan fa yafi mai yawa, ni dai zan ci gaba da zamana a nan zan ci gaba da riƙe sana'ata ta noma."

  "Shi ke nan ai, Allah ya yi albarka. Sai ka zo ka wuce gonar ko? Da man yau ba na jin daɗi sosai."

  Da sauri Salisu ya matsa wajen mahaifin nasa tamkar zai kifa kansa ya ce, "Subhanallahi! Baba me yake damunka? Ya ƙarasa cikin kiɗima.

  "Babu komai fa, kada kadamu kawai jikin ne ba na jin daɗinsa sai zawo da nake yi," baba Haladu ya ba shi amsa.

"Sannu baba sannu! Bari na jiƙa maka magani ka sha ko?" Ya faɗa yana mai yi wa wajen sallama ba tare da baba ya ba shi amsa ba. Bai wani ɗau tsawon lokaci ba ya dawo hannunsa ɗauke da kwanon shan da ya jiƙa magani ciki, ya miƙawa baba Haladu.
Baba Haladu ya miƙa hannunsa ya amsa ya kai kwanon bakinsa ya kafa ya soma kwankwaɗa, sai da ya sha da ɗan yawa kana ya sauke kwanon tare da miƙawa Salisu, shi kuma ya amsa.

"Allah ya yi maka albarka, ya jiƙan gyatumarka(mahaifiya)"
Al'amarin da ya haifarwa da Salisu jin wani abu ya tsarga masa cikin zuciya ke nan, tuni ya ji kewar mahaifiyarsa ta dawo masa sabuwa dal kamar ma yanzu ne ya soma jinta. Yana da shekara bakwai mahaifiyarsa mai suna Atine ta mutu bayan ciwon cikin dare da ya turnuƙeta wanda ko asuba ba ta riska ba ta ce ga garinku nan. Yana tsananin son mahaifiyarsa sosai cikin ransa, domin sam ba ta nuna masa wani abu wai shi kunyar ɗan fari duk da kasancewarta bafulatana, ba ta wofantar da shi ba, haka ta ba shi kulawa daidai gwargwado a lokacin da tana raye. Duk abubuwan da take yi masa na ƙauna tsakanin ɗa da uwa yana jinsu cikin ransa tun yana da ƙarancin shekaru har kawo yanzu da ya girma ya mallaki hankalinsa. Baba Haladu kam ya kasa ƙara aure tun bayan rasuwarta, a cewarsa 'bai ga mace mai kirkinta ba da za ta iya zama da shi daɗi da akasin haka' tun mahaifinsa na raye yake fama da shi har ya ƙyale shi ya zuba masa ido, mahaifiyarsa kuwa tasha kawo masa tayin mata ya aura amma ya ce 'shi sam a'a gwara ya ƙare rayuwarsa a babu aure wataƙila hakan na nufin matarsa tana can aljanna tana jiransa'. Sai itama ta yada makamanta ta tarkata komai ta zuba masa na mujiya har lokacin da ajali ya yi kiranta.

"Amin baba," Salisu ya ce yana mai goge 'yar ƙwallar da ta zubo masa.

Bayan minti biyar
Salisu ya fito ɗauke da fartanya a hannu.

   "Baba sai na dawo," Ya ce.
   "To Salisu, Allah ya tsare ya taimaka. Idan kaga garin da hadari ka tarkato kayanka ka dawo kasan har yanzu daminar ba ta ƙarasa wucewa ba kowane lokaci Allah kan saukar da ruwan sama."

  "To baba, in sha Allahu na tafi," Salisu ya ce.

   "To a sauka lafiya." Cewar baba.

***
  "Mama kinyi shiru baki ce komai ba"

Dariya maman ta yi kafin ta ce,

  "To ai na rasa me zan ce miki ne Zuhra, yo Allah na tuba ba sai ka damu da kasuwa kake bayar da sautinta ba, na sha faɗa miki ba tun yau ba ki tattara shi ki watsa kwandon shara, ko ya tareki a hanya kada ki saurare shi domin shi kansa sauraren tamkar kin ba shi wata dama ne, kuma hakan sam ba ajinki ne ba. Idan har ya sake tunkararki ni kizo ki sanar min zanje na yi wa waccen shegiyar matsiyaciyar uwartasa kashedi idan ta isa da shi kuma ta haife shi zata ɗau mataki ai."

Da hanzari Zuhra ta ce,

   "A'a mama ki ƙyale kawai, ni da kaina zan yi maganinsa faɗan nan ba na ki ba ne."

  "To takaina shi ke nan ai, amma ni bana so inga kina shiga damuwa fa"

  "Babu komai mamana ta kaina bayar da kanki a sare kije gida ki ce ya faɗi, komai ya wuce." ta yi maganar cikin sigar son basar da zancen.

  "Yauwa ko kefa tawan" ta ƙarasa tana yashe haƙora kamar gonar auduga, cike da jin daɗi  ganin yadda Zuhran ta saki ranta.

***
Ɗaki Fa'iza ta shige a guje, kan 'yar karamar katifarta ta yada zango, tare da fashewa da wani irin kuka. Tabbas sonsa a cikin zuciyarta yake bata jin zata iya yakice wannan soyayyar tasa ta yada kamar yadda kaka ke da bukata, so da kaunarsa sun riga sun gino cikin fadar zuciyarta, idan kuwa har ta ce zata cire wannan kaunar to sai dai ta zama gawa.

Cike da azama ta miƙe tare da nufar ma'ajiyar litattafanta, littafi ta zaro tare da ɗaukar biro ta zauna kan katifar ta yagi takarda ta soma rubutu a ciki, ta ɗau tsawon wasu mintuna kafin ta linke takardar ta ja jikinta ta kwanta, ta sake rushewa da kuka.

  "Ki yi haƙuri kaka ba zan iya ba, ba zan iya daina sonsa ba. Allah ma shaida ne an halicci ne don na so shi ne kaka, ki yafe min wallahi ina sonsa ina matuƙar ƙaunarsa."

Takardar da ta linke ta ɗakko tana jujjuyata tare da zuba mata na mujiya, kafin ta sake furta,

"Dole zan san yarda zanyi wannan takardar taje wajenka Sahibina."

Kaka na jingine jikin taga tana kallon ikon Allah, ita sam al'amarin Fa'iza ma mamaki yake bata, wannan wace iriyar soyayya ce? Dole ta yi wa tufkar hanci a gobe ba jibi ba zata mayar da ita ƙauye wanda take da tabbaci idan har ta yi nesa da nan ɗin to zata iya samun sa'adar abin da take wa so ɗin.

****
   17-02-2021

Yau sati uku da rasuwar Asma'u, sai dai har lokacin Falmata bata kammala wattsakewa ba, domin har kawo lokacin mutuwar na sake dukanta.

   "Hello ka iso" ta yi maganar bayan taaɗaga wayarta da ke ta faman tsiwa.

   "Ok to gani nan yanzu baby"

Miƙewa ta yi, ta zare mayafinta ta yafa tana mai fita daga ɗakin, a falo ta iske momi zauna tana jan casbaha.

   "Ina zuwa kuma?" cewar momi, tana kallon Falmata.

Murmushi ta yi kafin ta ce,

   "Momi zan je waje Abbas ne yazo yana jirana."

   "Kin san dai Abbanki bai son tsayuwarki da shi ko?"

Turo baki ta yi kafin ta iya furta,

  "Kai momi"

    "Mene ne wani kai momi, ni dai babu ruwana idan yazo ya iskeki tsaye da shi kya yi masa bayani, kuma ko kaɗan ban yarda a sako ni a cikin zancen ba na dai faɗa miki."

   "Ba ma zai zo ya iskemu ba in sha Allah"

  "A kula da kai, ban da giggiwa ga ɗa namiji"

     "To" ta amsa tana mai ficewa daga falon, kaitsaye harabar gidan ta nufa. Tun da ya hangota ya soma washe baki kamar mai tallan makilin.

   "Wow! What a beautiful?" yayi maganar yana kallon kyakkyawar fuskarta, duk da ba kwalliya ta yi ba amma ta yi kyau da ita.

  "To kallon ya isa haka ko"

Ta ce tana dariya.

   "Ina fa sweety da saura dai, ai babu wanda zai yi tozali da wannan kyakkyawar fuskartaki ya ce zai kawar da kansa never"

   "To na ji sarkin iya tsara zance." ta yi furucin tana yar dariya.

   "Au haka ma za ki ce."

     "Eh mana."

  "Shi ke nan ai. Ba wannan ba wai ya maganar aurenmu ne Falmata?"

  Nisawa ta ɗanyi, tare da sauke numfashi kafin ta ce da shi,

   "Ai yana hannunka, kai kawai nake jira"

Ɗan jim ya yi kafin ya iya bata amsa da,

  "Na sha faɗa miki kizo mu bi shawarata kawai domin kin san na shaida miki cewar mahaifina yaƙi amincewa da ke, kema kuma kin san mahaifi ki yaƙi yarda da ni kawai kizo mu gudu muje muyi aurenmu daga baya sai mu dawo ina da tabbaci idan har munyi auren muka dawo musu ba za su raba auren ba za su yarda su karɓi kowane sashenmu."
Chapter 17 · 0% Book details