Sashe 19
Budurwar Wawa Complete Hausa Novel · about 5 min read
Gaba ɗaya kan Salisu a ɗaure yake tamau. Sam ya kasa tuna komai, ya kasa tuna lambar da Abubakar ɗin ya ba shi da nufin ya neme shi ta nan, lambobin da suke rubuce jikin takardar da ya ba shi wacca ya zirata cikin aljihun wandonsa bayan ya fito daga gidan yari.
Ya ja wani yauƙaƙƙƙen dogon tsaki yana mai dafe kansa da ke tsananin sara masa. Ya sake lura da tun kafin fitowarsa daga gidan kaso idan ya yawaita tunani to sai kansa ya sara masa sarawa mafi tsananin muni. Jin kan nasa na san rabewa gida biyu ya ja jiki ya zauna dabas! A ƙasa yana kuma ci gaba da jan carbin tunanin da yake yi. Sai da ya ji ciwon na sake ta'azzara ya yi fatali da tunanin. Hawaye sai saraftu suke yi kan kuncinsa.
Bayan Shuɗewar Wasu Awanni
Dare ya tsala sosai, yayin da liman da Lauwali ke kwance suna sharar barcinsu. Salisu na zaune yana ta dama maganganu cikin ransa tamkar wani mai dama fura, zuciyarsa na sake ɗanɗanar masa roman ƙunci.
"Me ya sa kake son yawan saka kanka cikin damuwa da takure kai wajen tunani?" Ya tsinkayo muryar liman na kwaranya cikin magudanar jinsa.
A hankali yake bin fuskarsa da kallo kana ya kai ga furta,
"Bacci ya riga ya jima da ƙauracewa idanuna malam, bana jin ko kaɗan zan iya runtsawa."
"Ka yi haƙuri Salisu, shi fa mahaƙurci mawadaci ne. Ka zamo mai tausar zuciyarka mana kada ayi haihuwar guzuma ɗa kwance uwa kwance, kana dai ganin halin da mahaifinka ke ciki yaya zamu yi idan kaima ka kasance cikin halin?"
Ba da ban kar liman ya ce yana son bijire masa ba da san nuna masa bai isa da shi ba, da sai ya juyawa maganganun nasa baya, da kuwa sai dai ayi haihuwar guzumar.
"Ka kwanta," liman ya ce ganin bai ba shi amsa ba, don sai ya lura kamar ma wani sabon tunanin ya tafi.
Ba tare da ya musa masa ba ya yada haƙarƙarinsa ya kwanta kan shimfiɗar da yake zaune, ya kalli gefensa da Lauwali ke kwance yana sharar baccinsa har da su minshari tamkar rago hankali kwance sai ya sake jin ya sake tausayawa kansa. Ya saka yatsansa manuniya ya lakuce ruwan hawayen da suka soma yi masa saraftu kan kuncinsa.
'Allah ɗaya gari bamban' ya yi furucin sa'ilin da ya sake kai ganinsa kan fuskar Lauwali da ya gyara kwanciyarsa alamar baccin ya yi masa daɗi. 'Shi babu abin da ke damunsa, tunda malam lafiya lau yake,' ya ce can ƙasan maƙoshinsa. (Lauwali ɗan malam liman ne na uku) Sai ya ji ina ma a ce shi ne Lauwali da ba shi da wata damuwa tattare da shi.
'Kada kadamu, daman shi haka Allah yake al'marinsa. A duk lokacin da ya so aukuwar wani abun zai ce masa 'kasance' kuma sai ya kasance kamar yadda ya ce. Kada kadamu komai mai wuce ne Salisu. Da sannun za ka sami salamar ruhinka' Wani bigire na cikin ma'aikatar ƙwaƙwalwarsa ya sanar da shi haka. Bai yi baccin kirki ba shi ma baccin don dai ɓarawo ne shi ya sa ya sace shi. Ya tashi da wani irin matsanancin nauyayyen ciwon kai da yake ƙwarzanarsa sosai, domin jin kan nasa yake yi tamkar zai ragargaje.Yadda ake dukan turmi da taɓarya haka yake ji ana yi a cikin kansa.
Lokacin da liman ya ankare da shi sai ya nemi jin ba'asin abin da ke damun shi, amma ya gaza sanar masa da komai. Sai dai kowace daƙiƙa yana ankare da shi da duk wani motsinsa, yana kuma lura da shi lokaci zuwa bayan lokaci yakan dafe kansa tare da rumtse idanu. Kafiya da na ci irin nasa suka gaza ba shi damar sanar masa da cewa 'ba shi da lafiya' duk da daman ya san Salisun ba tun yau ba akwai shi da zurfin ciki. Sai kawai ya ci gaba da zuba masa idanu ya ga ƙarshen tuƙewa.
***
20-02-2021
A guje ta faɗo falon fuskarta cike da maɗaukakin annuri. Tun lokacin da Abba ya yi mata magana akan Abbas sai ta gwammace su haɗu a waje gudun ɓacin ran mahaifin nata.
"Momi albishirinki" ta ce tana rungumar momin.
"Kin ga ni cika ni, karki ƙarasa min sauran ɗan kuzarin nawa."
"To ai ba ki ce goro ba"
"Goro shi ke nan"
"Yauwa momita, kin san me Abbas ya ce min iyayensa zasu zo gobe a yi maganar aurenmu."
Jim momi ta yi, annurin fuskarta ya ɗauke saboda tasan ba abu ne mai yuwuwa ba, domin a ɗazu komai ya warware wannan soyayyar tasu.
"Momi lafiya na ga ba ki yi murna ba."
"Falmata ina ma ace kafin ɗazu kika zo da wannan albishir ɗin zan ji daɗi sosai, sai dai a yanzu zuwansu ba shi da amfani domin mahaifinki ya riga ya bayar da ke ga mijin yayarki Asma'u."
****
2022
A hankali ta zira hannu cikin jakarta ta ciro kuɗaɗen da suke ciki ta zube gaban mama, dake zaune har yanzu kan kujerar tsugunno gabanta.
Cike da farin cike take bin ɗiyar tata da kallo da jin daɗin ganin kuɗin, amma wani sashi na zuciyarta na ɗan saka mata shakku game da kuɗin.
Miƙewa tayi zuruf kan ƙafafunta ta suri kuɗin tana kallon Zuhra da ke taugunne, kafin takai hannu ta ja hannun zuhran tana faɗin,
"Mu shiga daga daki, ki faɗa min waya baki wannan maƙudan kuɗaɗen zuhra? Wane aiki kika yi masa har haka da zai buɗe miki bakin aljihu haka?"
"Haba mama" faɗin zuhra tana zame hannunta daga riƙon da tayi mata, kafin ta tsugunna tana mayar da numfashi, tsawon wasu daƙiƙi kafin mama ta sake furta,
"Baki sanar da ni inda kika samo kuɗaɗen nan ba Zuhra ina ta tambayarki kin yi mini shiru" ta arasa maganar tana sake zaro ido sanda ta sake yin arba da tumulun kuɗin hannunta tana jujjuyasu.
Murmushi Zuhra ta yi, kafin ta ce,
"Wai mama me ya sa kike kokwanto akaina a wasu lokutan da dama, na sha shaida miki bana aikata komai kawai dai ina kisisina ta ne a wajen maza yadda nake laso kuɗaɗensu."
"A'a Zuhra ki sanar da ni gaskiya, ina jin cewa kamar kina ɓoye min wani abu."
"Gaskiyar ke nan, idan ba ki yarda ba sai na kwashe kuɗin na mayar masa, na kuma faɗa masa gaskiyar ala'amarin cewa mahaifiyata lafiya lau take, kawai mun haɗa baki da ita ne domin mu samu kuɗaɗe ta hannunka."
Wannan shi ne last free page, zaki iya tura kuɗinki 300 acc:8085307740 opay maryam abdulaziz domin samun cigabansa.
Maikosai
08130266650