Sashe 1
Budurwar Wawa Complete Hausa Novel · about 8 min read
[4/7, 10:11 AM] My number: https://chat.whatsapp.com/CodXIM9nLOXD1QDmW33svF
BUDURWAR WAWA
FCW
MAIƘOSAI
Wannan littafin ƙirƙirarre ne kuma ayyananne, idan yayi kamanceceniya da rayuwar wani ko wata to arashi ne.
Ban yarda a juya min littafi ta kowace iriyar siga ba, yin haka ya saɓa da doka, a kiyaye.
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA DA JINƘAI
01.
Tsananin zafi da azaba ya hana gaɓɓan jikinta motsawa. Sosai take yinƙuri a karo na babu adadi domin kufcewa salonsa na rashin imanin da yake aikata mata, sai dai wannan karon ta gaza aikata komai domin daidai da ɗan yatsanta ta gagara motsawa.
Wani gumi ne ya shiga tsattsafo mata saman goshinta, take ya zama ruwa ya biyo saman fuskarta, ji ta yi wani abu na biyo sawayen cinyoyinta,tsananin duhun dake mamaye da ɗakin ya sa ta kasa tantance mene ne shi,ruwa ko jini? Ta fashe da wani irin kuka sai ka ce zakanya, sai dai ko kaɗan babu ruwan hawaye a tattare da kukan ,abin da ya sake faɗar mata da gaba ke nan.
"Shi ke nan, ruwan cikin kogin idanuwan sun ƙafe" ta furta hakan a hankali, wanda da ƙyar furucin ya fita.
Ta sake yinƙurawa da nufin tashi, kaaccc! Ta jiyo sautin ƙarar ankwar da ke saƙale jikin ƙafafuwanta. Ta koma ta zauna da sauri jikinta na wata iriyar rawa, harta da naman jikinta na shi rawar sukudayen yake yi. Ji ta yi kowace gaɓa ta jikinta ta yi sanyi kamar ruwa a cikin firinji.
"Ka cuci rayuwata, ka wulaƙanta soyayyarmu da kai, me ya sa za ka yi min haka? Me na aikata maka haka?"
Ta shiga watsowa kanta tambayoyin da bata da amsarsu, ganin babu sarki sai Allah ya sa ta silalewa ƙasa ta kwanta ta yi lamo sai ka ce kada a cikin ruwa.
Mintunan da ba su haura biyar ba aka turo ƙofar ɗakin, haske ya bayyana kaɗan wanda ya daki idanuwanta,ta buɗesu a hankali tana mai jin wani nauyi kamar an ɗora mata dutse a saman idanun.
Daf! Da ita aka ƙaraso a ka tsaya ƙyam! Gabanta, kafin a saka hannu a kwance ankwar dake hannunta, tare da turo mata kwanon abinci.
"Dan Allah ka taimakeni, ka fitar da ni daga wannan azabar na roƙe ka"
Ta ƙarasa faɗa tana haɗe hannayenta biyu waje guda alamar roƙo.
"Shiii! Kada ma ki fara, kada ki kuskura domin ni ban san Allah ba, ban san mene ne wani abu taimako ba."
Ba ta sake furta komai ba ta sake sulalewa ƙasa ta yi kwanciyarta sai ka ce maciji.
Ganin hakan da ta yi ya saka shi murmusawa irin murmushin mugunta, yana mai mayar mata da ankwar tare da tura kwanon abincin daidai saitin kanta kana ya ce,
"Idan kin ga dama ki ci, idan kuwa akasin haka kika zaɓa ke ce a wahale domin kuwa kin san ba wanda zai iya kuɓutar dake daga wannan gidan."
"Sai Allah" Ta furta hakan a wahalce, domin gabaɗaya ƙarfinta da kuzarinta sun ƙare.
Bai bata amsa ba, ya sa kai ya fice daga ɗakin bayan ya ja ƙatuwar ƙofar da ta yi wa waje da ɗakin shamaki.
Ta sake fashewa da kuka mai tsanin cin rai a karo na biyu, ta saka hannunta da ke ɗaure da sarƙa ta janyo kwanon abincin ta soma ci hannu baka hannu ƙwarya.
Ba dan tana so ba, ba dan daɗi ko garɗi take ci ba, sai dai kawai dan gujewa yunwa dan ta lura ba za ta bar gidan ba , ta ji ma da sanin cewa lallai ajalinta a gidan nan yake cikin wannan ɗakin.
A haka ta kammala cin abincin ta ture kwanon gefe, ta sake silalewa ƙasa ta kwanta.
"Ya Allah! Na tuba ka gafarceni, na san na cuci kaina na aikata zunubin da nake ji tamkar ba zan samu afuwarsa ba. Ya Allah! Kaine kake cire bawa daga ƙangin rayuwa ya Allah ka fitar da ni daga wannan wajen ko na samu na nemi yafiyar mutane ukun da suka so inganta rayuwata."
Ta rushe da wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.
"Na gaza ba zan iya ba, ba zan iya ci gaba da zama a nan ba, ni mace ce kuma mai rauni wayyo Allahna!" Ta sake furtawa, tana dukan ƙasa da hannayenta biyu a hankali.
'Ya kamata na fita daga gidan nan' tayi maganar can ƙasan makoshinta.
'To amma ta ina zan soma, bacin duk wani yunƙuri da na yi a baya a tutar babun baɗinuhu ya tashi' ta sake raya zancen a zuci.
Tuni ta sake rushewa da kuka sanin cewa duka hanyoyin fitar sun toshe, tunani ya cika ƙwaƙwalwarta yadda ta gaza samar mata da mafita.
Ji ta yi an sake turo ƙofar ɗakin, ba ta yi ƙoƙarin ɗagowa ba domin ta san ba zai wuce wanda ya shigo ɗazun ba.
Naushin cikinta da ta ji an yi shi ya ba ta damar buɗe manyan idanuwanta da suka kumbura suka suntuma suka haye suka yi sumtum, wanda nauyinsu ya sake ƙaruwa fiye da na ɗazu.
Ta saki wata ƙara mai ƙarfi tana ƙoƙarin dafo cikin nata ta sake ji an finciko gashin kanta kamar za a cire shi.
Ta sake sakin wata ƙarar a karo na biyu, tsananin duhun ɗakin ya kasa sawa ta gane ko wane ne, sai dai ƙamshin turaren da ya daki hancinta ya ba ta damar tantance mata ko waye.
Mutumin da ya ɗakkota daga jaharsu ya kawota wannan jahar, mutumin da ya kasance masoyinta kuma mijinta wai yau shi ne yake gana mata azabobi iri-iri saboda kawai son zuciya irin tasa wacce ta gaza ba shi damar...
Kafin ta ida kaiwa ga zancenta ta ji an ɗora mata wani abu kamar bulo a gadon bayanta, tsananin nauyinsa ya sa ta saki wahalallen numfashi. A ka sake ɗora wani akai, ta yi ƙasa da kanta wanda ta tafi za ta kifa ta yi rub-da ciki, sai dai jin wani abu saman ƙirjinta ta yi wanda shi ne ya tokareta ya hanata ƙarasawa ƙasan. Ba za ta iya cewa ko mene ne ba, amma abun ya tokare mata ƙirji yadda har ta ji numfashinta na barazanar ɗaukewa.
Sai da aka ci wajen sakan ashirin sannan aka sauke mata abun, tare da cire mata wanda ya tokare mata ƙirjin na ta.
Jan ta aka shiga yi ,tare da dire ta gaban wani ƙaton baho da aka cika shi taf! Da ruwan sanyi, babu shiri a ka tsunduma kanta ciki, ta ja wani dogon numfashi tare da furzarwa wanda har sai da ya sa ta shaƙi ruwan sosai ta hancinta.
Shiɗewa ta yi amma hakan bai sa ya sassauta mata na daga azabar da yake gana ma ta ba, sake mayar da kan ya yi cikin ruwan wanda shi ne ya yi sanadin ɗaukewar numfashinta ɗif! Ta daina numfashi.
Ya sake fito da kan, tare da sake mayar da shi cikin ruwan da ƙarfin gaske yana mai cizgar gashin kanta da iya ƙarfin da Allah ya hore mi shi.
Take ta saki wani nauyayyen ajjiyayyen numfashin da ya farkar da ita, wahala ta saka ta sakin jikinta wanda ya sake yin la'asar.
Ganin haka ya ba shi damar ƙyaƙyacewa da mahaukaciyar dariya, wacca ba komai ne a cikinta ba fa ce zallan zalunci da rashin imani.
"Bakin rijiya ba wajen wasan yaro ba ne ba yarinya"
Ya faɗa yana yin wurgi da ita, sai ka ce ƙullun kayan wanki.
Kukan ma ya kasa zuwa, tsananin azaba ta hanata furta komai, sai dai cikin zuciyarta Allah ya isa kawai take jefa mi shi tafi a ƙirga.
Tana ji ya sake buɗe ƙofar ɗakin kamar yadda ya buɗe ya shigo haka ya buɗe ya yi ficewarsa abun shi, ba abin da ya dame ranshi da rayuwarshi.
"Allah ya isa mugu" Ta furta hakan a wahalce, wadda muryarta ma ta dashe ba ka iya jin sautin fitar algaitar sosai da sosai.
***
Dogowar riga ce ta atamfa sanye jikinta, ɗinkin ya amsheta hakazalika ita kanta atamfar ta karɓeta sosai. Hannunta ɗauke da jaka launin da ta dace da atamfar.
Ita ba fara ba, haka nan ita ba baƙa ba ce, za ka iya kiranta da kalar ruwan wankan tarwaɗa ko cakulet. Kyakkyawa ce sosai ma sha Allah, hancinta ya ɗan tasa ga tsine wanda shi ne ya sake fito mata da kyan fuskar, sai manyan idanuwanta ma su kalar shaf ɗin ƙwai, launin ƙwayar idanunta kuwa fara tas! Ta ke. Gashin kanta da ya zubo har kan kaɗarta, sajen dake shimfiɗe gefen fuskarta ya sake haifar mata da wata cikar zatin.
Hannunta na dama sanye da awarwaro guda biyu rak! sai zobe guda uku jere a 'yan yatsun hannun. Sai agogo dake ɗaure a tsintsiyar hannunta na hagu, kafaɗarta kuwa rataye take da ɗan ƙaramin gyale wanda ba ta yafa shi ba.
"Mama sai na dawo"
Ta yi furucin da ɗan ƙarfi.
Mama da ke cikin wani matsakaicin ɗaki ta fito bayan ta ɗage labulen da ya mata shamaki da 'ƴar tata, ta tuƙe a wajen tana mai ƙarewa 'ƴarta ta kallon tsaf.
Cikin murmushi ta soma furta,
"Ka ga ɗiyar arziƙi wacca ta ga ji arziƙi. Ko da yake daman hausawa na cewa kyan 'ya ta ga ji uwarta, tabbas ke kam kin gada domin kuwa ni ba jinin talauci ba ce jinin arziƙi ce wacca ke fankama da arziƙi, kuma har abada da arziƙi zan mutu. Ni na sa ni, na san abin da nake miki ba zai ta shi a tutar babu ba, shi ya sa nake ƙara jin danƙon sonki cikin zuciyata 'yar nan. Ki tabbatar dai wannan fitar kin yi babban kamu."
Zuhra da ke tsaye gaban mahaifiyarta tana wani kwalmaɗa jiki sai ka ce tana, ta yi 'yar ƙaramar dariya kana ta ce,
"Kwantar da hankalinki Mamana tamkar kin sanya tsumma a randa, wannan ai shi ne yafi komai sauƙi a wajena. Me kike ci na baka na zuba haka har da dilalar yawu?"
Ta tuntsire da dariya kafin ta ɗora da,
"Ka da ki manta wannan Zuhran ki ce fa son kowa ƙin wanda ba shi da rabo."
Mama ta yi dariya sosai har da guɗa, tana mai saka hannu tana juya Zuhran.
"Ai daman na sani, maza ki je ɗiyar arziƙi, Allah ya bada sa'a."