← Book details Bintu Diyar Bayi Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 28

Sashe 26

Bintu Diyar Bayi Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ba ta umarni. Har ga Allah ba ta son cire zoben, idanunta na fidda kwalla yayinda ta ciro zoben daga yatsanta, maimakon ta bashi sai ta dunk’ule shi cikin tafin hannunta. Ganin bata da niyar mik’a masa, ya mik’o hannunsa gare ta, a hankali ta d’aga ido ta kalle shi, ya na mai gyad'a mata kai ya mata nuni da hannunshi. Hannunta na rawa, ta aje zoben bisa tafin hannunsa, ba ta ankara ba sai gani ta yi yayi wulgi da shi gefe. Da sauri ta bi inda ya jefa da kallo yayinda ta ji zuciyarta na mata rad’ad’i, sai a sannan tasan ashe zafin da zuciyarta ke mata ba na rabata da iyayen ta kad’ai ba ne, har da na rashin Aisar har abada, gashi idan aka d’auke turarukan da ya bata, zobenshi ne kad’ai ya rage mallakin sa a gunta, ta na ji ta na gani Yarima Nuhu ya raba ta da shi kamar yarda ‘yar uwarsa ta rabata da shi, idan ita dan ta na son Aisar ne, shi kuwa Yarima Nuhu menene na shi azancin? Tambayar da ta yiwa kanta kenan, wanda nan ta ke kuwa ta ji amsarta, Yarima Nuhu na mai duban ta ya kira sunan ta da kakkausar murya
‘’Bintu’’
Hakan yasa Bintu dawowa da kallonta gareshi. Bai gushe ba ya cigaba

‘’Soyayya gaskiya ce, soyayya halal ce muddin ba a tsallake iyakokin Ubangiji ba, ba laifi ba ne don kinyi soyayya, amma ki sani duk duniyar nan da ni ya dace ki yi, Bintu ni mai kaunarki ne, ni Nuhu ni masoyinki ne da ni ya dace ki yi soyayya ba da wani tsoho da ake shirin amra mi ki ba, ko kuwa wancan sokon Monsieur da ya bawa d’alibarsa ajiyar zobe!’’

A tsorace Bintu ta fara ja da baya, ta na mai girgiza masa kai, tsabagen firgici ta kasa magana. Da sauri ya rik’o hannunta, ya na fad’in

‘’Karki guje ni Bintu, ni mai k’aunarki ne, kimin alkawarin za ki aje min kanki amana, ah ah kawai ki shirya mu gudu, duk k’asar da ki ke so aradu zan kai ki Bintu, kar ki yarda a amra mi ki wannan tsohon.’’

Cikin sauri Bintu ta fizge hannunta daga nashi, har lokacin ba ta fasa girgiza kanta ba, yayinda ta ke hawaye d’aya na bin d’aya, tunda ta ke a rayuwarta babu wanda ya ta6a furta kalmar so a gareta, kuma ba ta ta6a zaton zata ji shi daga bakin ko da ‘yantaccan d’an adam ba ne, bare kuma Yarima, Yariman ma na Sa'ayrasa. Hankalin Bintu bai dad’a tashi ba, sai da ta ga kwalla cikin idanun Yarima Nuhu na gangara a hankali bisa kuncinsa, nan ta mik’e tsaye da sauri yayinda kuka ya ci k'arfinta tana mai tattare kasan doguwar rigarta, ta juya da niyyar tafiya, hakan yasa Yarima Nuhu tashi da sauri, ya na mai rik’o kallabinta ya ke fad’in.

‘’Karki tafi ki barni Bintu, aradu zan iya rasa raina, ki tausayamin.’’
Sakar masa kallabin ta yi, gashin kan ta lub lub ya sauko har bisa wuyanta maimakon gadon bayanta da ya saba saukar sakamakon askin da ta sha gun Marry, tana mai tafiya cikin gudu gudu, sauri sauri, ta d’au hanyar fita daga lambun.

Yarima Nuhu rik’e da kallabinta ya shiga doka mata kira
‘’Bintu! Bintu!! Bintu!!!’’
Ina ko waige ba ta yi ba bare ta tsaya har ta fice daga cikin lambu, in da ta bar Yarima Nuhu rungume da kallabin na ta bisa k’irjin sa, ya zube gwiwowi biyu k’asa zuciyarsa na bugawa kamar za ta tsage ta fito.

🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
[5/15, 7:26 PM] ‪+234 703 962 5239‬: ®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪

GARGA'DI

KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.

DA BAZARKU NI NA KE TAKA RAWA ​FIKRA WRITERS ✌🏽

Ummuabdoul
Ummu Hannan
Rashida Kardam
Sanah Matazu
Aysha Kura
Batul Maman
Bingel
Farida Abdullahi
Da uwa uba Rufaida Umar, ba zan mance da ke ba. Allah ya bar zumunci.

©Khadija Sidi.....✍🏼

2⃣5⃣

Kai tsaye 6angaran Jakadiya da ya zame mata sabon wajan kwana ta shige, ta tsallake bayi biyu wanda ke ta faman had’e sababbin kayan da aka d’inko mata, ta shige d’akin Jakadiya ta na mai doka k’ofar gudun kar Yarima Nuhu ya biyota. K’uryar d’akin ta shige ta k'udundune ta na mai mayar da numfashi. Ba ta yi minti biyar da shiga ba bayin su ka biyo ta su na mai tambayar lafiya? Ko ta yi gamo ne?

Baki na rawa Bintu ta ba su amsa da ‘’Don mai sama ku rabu da ni, ko shakka babu na kusa rasa raina, na shiga uku ni Bintu na lalace, wayyo Allah Inna ta!’’

Kallon junansu su ka yi, su na mai gyad’a kai cikin jaddada zatonsu na Bintu ta yi gamo, har an fara jifanta daga Masarautar Fabarusa tun kan ta shiga Masarautar, su ka juya jiki a sanyaye su ka fito suna mai rufo mata k’ofa.
Daga waje baiwa ta dubi ‘yar uwarta ta ce
‘’Gide k'ak'a kenan, kinga har an fara yiwa wagga d’iya ture ko? Babu mamaki wani bakin aljanin aka fara mata ture da shi don ta fita hayyacinta ta ce ta fasa amran ga, wagga sharri sai kishiyoyi, maza je ki shedawa Jakadiya tun kafin abu yayi tsamari.’’
Cike da jimamin abun baiwar ta amsa mata da
‘’Wagga batu gaskiya ta, aradu wagga d’iya gamo ta yi, inda kin lura har launin idanunta ya sauya, bara dai na je ga Jakadiya, mutum hege ne, mutum ba imani.’’

Tana mai ta6a kafad’arta, ta ce
‘’Maza Ladiyo, ni bara na tsaya daga rariya ko da wani abun zai faru.'’
Jikin baiwar na rawa ta fara tafiya, tana fad’in
‘’Eh tsaya Kyallu, bara na ruga na dawo, Allah shi fisshemu daga sharrin mahassada.’’
Ta fice, inda ta bar Ladiyo da tsaron k’ofar Bintu. Ita kuwa Bintu ita kad’ai tasan abinda ke damunta, yau ta ji ta kuma ga abinda ba ta ta6a tsammani ba, ko shakka babu tasan rayuwarta ce ta zo k’arshe, ko kuwa dai Yarima Nuhu ya soma shaye-shaye kamar yanda wasu samari daga cikin bayi su ke yi. Abinda ke d'agawa Bintu hankali shi ne sake rike hannunta da Yarima Nuhu ya yi, ita tasan rayuwarta ce ta zo k'arshe.

Jin Bintu ta fara yin gamo tun ba aje ko'ina ba, nan da nan Jakadiya ita ma ta had’o kayan tsubbuce tsubbucenta, haka ma Hajja Kilishi, wacce dama ita aka damk’awa Bintu a hannu. Suna mai jan kunnan bayinnan biyu, Ladiyo da Kyallu, akan kar su sake aji maganar a waje.

A gaba Jakadiya da Hajja Kilishi su ka sa Bintu, tambayar duniyarnan sun mata akan gamon da aka ce ta yi, amma shiru Bintu ta kasa ce musu komai don kuwa muddin ta fad’i gaskiya to kashinta ya bushe. Ganin haka su ka yanke hukuncin fara kare ta tun daga yanzu don babu mamakin sammu da aka fara mata har da na d’aure baki. Bintu na ji ta na gani aka fara mata lalas da siracen magunguna, har da na sha da wanka, kan ka ce me tuni ta fita hayyacinta in banda attishawa babu abinda ta ke yi, ko iya haka aka barta ta san ba k’aramin masifa ganin Yarima Nuhu ya jaza mata ba.
Bayan siracen da ta sha, sai da Jakadiya ta bi duka ga6o6in jikin Bintu ta na d’aura mata laya, wai gudun kar a zo mata cikin dare, nan ko ba su san in ma akwai aljanin ba zai wuce Yarima Nuhu ba, kai Allah shi fisshe mu aikin jahilci.

Saida su ka tabbatar sun gama kafe Bintu kaf, Hajja Kilishi na mai duban Bintu da gaba d’aya ta jigata saboda siracen da ta sha, gashi cikinta har juyawa ya ke tsabagen had’aka na magunguna da Jakadiya ta afka mata duk da sunan makarin sammu da kafiya, Hajja Kilishi ta ce

‘’Ni ko Jakadiya d’iyarnan na shan maganin da’a kuwa(maganin mata)?’’

Jakadiya na mai susa k’eya ta amsa da
‘’Yo to wani maganin da’a za a bawa wagga d’iya za a amran da ita ga tsoho ank’i rami? Ai ni a tunanina tunda dai Sarkin Fabarusa an tsufe ban ji zai damu da abubuwa irin wagga, ko k’ak’a kin ka gani?’’
Hajja Kilishi na mai murmushi ta ce
‘’Tsoho ba mutum ba Jakadiya, yo to maza ma ai ba sa tsufa, kar ki so ki ga yanda Takawa ke ji dani duk farin gemun nan nasa, yauwa tun da magana ta kawo magana, Jakadiya ina mai buk’atar zuwan Takawa gare ni a yau ma, hallo zannuwa da kallabi har guda goma na nan tafe izuwa ga d’akin Jakadiya nan ba da dad’ewa ba’’
Dama dai maganar kenan, ta 6ige da Bintu gudun kar Jakadiya ta ga kamar ta cika naci, don kwana hud’u kenan ita Jakadiya ta ke kai wa Sarki, kasancewar hatta kwanan matan Sarki sai wacce Jakadiya ta za6a tsabagen matsayi irin na Jakadai a fada.
Jakadiya kuwa mai idon cin naira, jin zannuwa na tafe tuni ta kada baki ta ce
‘’Yo to menene, in ma sau goma ki ke san zuwan Babban Bijimi aradu gun ki ya ka kwana, an gama ranki shi dad’e, sai kin ga zuwan mu.''

Hajja Kilishi na mai jindad’in yanda Jakadiya ke damawa da ita, duk da dai ta san na d’an k’ank’anin lokaci ne, in dai Jakadiya ce bakin ganga ta ke, arzikinka shagalinka. Ta mata sallama in da ta barta da Bintu ta mai mata jawabin yanda za ta yi ta kare kanta a Masarautar Fabarusa. Ita dai Bintu jinta kawai ta ke, amma ko yaya ta rufe idanunta fuskar Yarima Nuhu ta ke gani yayinda ya ke furta kalmar so a gareta, haka zalik’a maganganunsa ke mata yawo cikin kwakwalwarta. Ko shakka babu Bintu ta yi gamo, amma fa da Yarima Nuhu, mutuwarta kad'ai ta ke jira kamar yanda Iya Dije ta ce muddin namiji ya ta6a ta.
Chapter 26 · 0% Book details