Sashe 2
Bintu Diyar Bayi Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Su na hawa su na sauka har sai da su ka yi sahu uku. Bintu na Murna da sun sake komawa za su kwashe sauran kayan. Budan bakin Gimbiya Binta sai cewa ta yi,
'’akwati nawa ne su ka rage?’’.
’Daya daga cikin bayin ta amsa mata da,
"huɗu ne su ka yi saura ranki shi daɗe'’.
Gimbiya ta ce,
"to! Za ku iya tafiya kubarwa ɗiyar bayi sauran ta k’arasa hawa da kayan’’.
Tuni idanun Bintu ya raina fata, ba wai wuyar hawa da kayan ba ne damuwan ta ba, a'a ita ta dan akwaitin k’arfe ta ta ke. Cikin girmamawa su ka durkusa su na mai faɗin,
"an gama ran ki shi daɗe'’,
hannu kawai ta ɗan ɗaga musu alamar sa iya tafiya. Cikin hanzari su ka daɗa rusunawa kafin su tashi su ka fice. Ai fa Bintu ba ta san san da ta arta a na kare ba, ta na ji sauran bayin suna dariya suna cewa:-
‘’Ba ke mai yiwa Gimbiya hidima a boko ba, Allah shi k’ara’’,
ɗaya ta k’ara da "ai tin da aka zab’e ta wani girman kai ya game jikin ta, ɗiyar bayi a makarantar girma’’.
Yi ta yi kamar ba ta ji su ba, ta k’arasa ta ɗauro akwati ɗaya a ka d’aya kuma ta jawo shi a hannu. Ba ta kai ga hawa bene ba ta yi kaciɓus da su, haka su ka wuce ta suna mata dariyar kyeta. Cikin himma ta haye abun ta sama, sai da ta kai ga kofar ɗakin ta tsaya dan ta ɗan sami nutsuwa dan kuwa idan Gimbiya ta gano ta lalle kashin ta ya bushe. A hankali ta tura kofar tare da sallama. Gimbiya ko ta nuna ta san ta shigo bare ma ta amsa sallamar. Cike da nutsuwa ta aje akwatinan sannan ta fito, nan ta sake zurawa a guje, ta kwaso sauran akwatinan kamar dai yanda ta yiwa biyun farko. Aje akwatinan ke da wuya ta juya da niyyar sake fita, Gimbiya ta daka mata tsawa,
"ina zaki? Nufin ki ni zan jera mi ki kayan yau kuma ɗiyar bayi?’’.
Jiki na rawa Bintu ta zube k’asa ta na mai faɗin,
"tuba na ke ranki ya daɗe ni ce zan jera dama sauri na ke dan kwaso nawa kayan kar Ado ya manta ya juya da su’’.
Shiru idan Gimbiya Binta ta tanka ko shakka babu dutse ma ya tanka. Da shirun yayi yawa Bintu ta ɗaga kai ta kai kallon ta gare ta, sai gani ma ta yi ta runtse ido kamar mai bacci. Dole jiki ba laka Bintu ta tashi ta shiga jera akwatunan, sai da ta gama tsaf sannan ta durk’usa ta ce,
‘’ran Gimbiya ya daɗe na idda’’.
Sai da wasu dak’ikai su ka shuɗe, har Bintu ta na tunanin ko dai bacci ta ke sannan ta ji ta ce,
‘’kya iya kwaso tsummokaran na ki’’.
A wulakance ta yi furucin cike da 'kas'kanci. Russunawa ta yi cike da girmamawa ta ce,
‘’godiya na ke ran ki shi daɗe", ta tashi ta fice. Nan fa duk nutsuwar ta ya gushe, ta ranta a na kare, ba ta ji ba ta ba ta gani. Dalibai ma su shiga da fice cikin farfajiyar wajan faɗi su ke,
"ta fara, in dai wannan ce dama duk dawowa hutu haka ta ke".
A guje ta fito daga harabar ɗakin kwana ta shigo sashen ajijjuwa. Ba ta ga tahowar shi ba sai ji ta yi karo da shi. Ta yi saurin yin baya saura k’iris ta faɗi ya yi saurin sa hannu biyu ya rik’o ta. Sakin baki ta yi ta na kallan sa,ta ma manta da gudun da ta ke.
Sanye ya ke cikin bakar _suite_, wankan tarwaɗa be mai dan faffaɗar kafaɗa. Ya na da dogon hanci, yayin da gashin bakin sa da ya zagaye bakin na sa ya k’ara masa kyau da k’warjini. Idanun sa rufe cikin bakin gilashi hakan ya sa ba ta sami damar ganin kwayen idanun na sa ba. Kamar daga sama muryar sa ya dakin dodon kunnan ta,jin ya ce
‘’hankali mana gudun me ki ke haka ke kuwa?’’.
Ta yi saurin ja da baya,hakan ya sa shi sakin ta.
’’Yi hakuri dan Allah Ado direba zai tafi da kaya na’’.
Bintu ta furta idanun ta na shirin kawo ruwa. Sai a sannan ya dubi kayan jikin ta ya na mai faɗin,
‘’Tabbas wannan shigar ta ki ta bayin Masarautar Sa'ayrasa ne, ina shigowa na ga motocin na su na fita, sun manta da ke ne...?’’,
ba ta bari ya karasa maganar ba bare ta bashi amsa ta sa gudu ta na mai faɗin,
"shikenan ni Bintu sun tafi da akwati na,shikenan na banu na shiga uku na lalace’’
Cikin rashin fahimta ya bita da kallo har sai da ta kure masa sannan ya d’aga kafad’a ya sauke sannan ya yi ciki abun sa.Isar ta wajan yawan motoci masu kai kawo ya k’aru,sai dai babu motocin Sa'ayrasa babu alamar su. Kwallar da ke idanun ta tuni su ka fara gangarowa bisa kuncin ta.
®
✏📖
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
©Khadija Sidi.....✍🏼
Wannan labari sadaukarwa ne kuma tukwici ne ga FIRDAUSI SODANGI,wacce ta amince da wannan batu na "garin masoya ba ya nisa" har ta kawo ziyarar ta gare ni. Allah ya bar zumunci ya bar kauna Amen.
0⃣2⃣
Bintu na shirin juyawa ta hangi akwatin ta jefe tsakiyar filin, da gudun ta ta k’arasa ta rungumo abin ta ta na maida numfashi. Wani mai mota ne ya ba a mata k’ura sa’annan ya lek’o ya na fa in
"shashasha sai kin jawo wani ya taka ki’’
ko aga kai bata yi ba bare ma ta san ya na yi. Ita dai burin ta ya cika ta sami akwatin ta.
Offishin shugaban makarantar katan ofishine wande aka kawata shi kai ka ce ofishin shugaban wani yankin ne. Ganin wanda ke zaune gaban sa da kuma abun da ke tafe da shi ya sa shi zufa na ba gaira ba dalili rufe shugaban makarantar. Kana ya nisa tare da fa in
"(your excenllency) Ya mai girma....’’
"Aisar,ko ka kira ni Aisar Gaddafi Nur,(his excenllely) ya na gida yallabai’’
ya katse shi hankali kwance. Zufa shugaban makarantar wanda dalibai ke kira Malam Hamisu ya goge,ya na mai gyara murya ya ce
"toh Yallbai,yanzu dai nufin za ka yi bad da kama kamar malami cikin wannan makaranta ta mu har tsawan zango aya.....’’
Yana mai murmushi ya ce
‘’ba bad da kama ba Yallabai,gyaran lafazin shi ne ina neman alfarmar koyarwa a makaranta na tsawan zango aya’’
cikin nazari Mallam Hamisu ya ke duban sa "me zai sa dan Shugaban kasa so ya koyar a makarantar nan?na zango aya? Ko shakka babu ya na daga cikin motanen oye wanda ke yiwa kasa bincike da aiki cikin surru, dama ba tun yau ya ke jin maganar ba,kaddai wani sharrin aka kullawa makarantar sa.....’’
Zancen zucin da ya ke yi cikin ran sa kenan dan kuwa ruwa ba ya tsami banza. Can dai ya gyara murya sannan ya ce
‘’Yallabai....’’
‘’Aisar’’
Saurayin ne ya k’ara katse shi ya k’ara da
"tunda zan zauna k’ark’ashin ka ya kamata ka saba da kira na da sunana.’’
Cikin jinjina kai Malam Hamisu ya amsa da
"Haka ne Aisar,muna maraba da kai,kuma ina mai tabbatar ma ka mu yan kasa ne masu kishin kasan mu,na gari ma su san ci gaban kasar mu.’’
Ya na mai murmushin nuna gamsuwa Aisar ya tashi tsaye gami da mik’a ma Malam Hamisu hannu ya ce
"madallah da kai,kuma na gode kwarai,gobe InshaAllahu zan fara koyarwa sai a bani aji a kuma zaga da ni makarantar sauran Malamai su sanni ko koyar da ni sharad’an makaranta idan akwai, duk abun da ka ke buk’ata in koyar shi zan koyar’’
Mallam Hamisu shi ma in tashi yayi,ya na murmushin yake ya amshi hannun Aisar,fa i ya ke
"Madallah Allah ya nuna mana’’
amma a zahirin gaskiya a tsorace ya ke da Aisar.
Sai da ya raka shi har kofa ya tabbatar ya tafi sannan ya dawo ofishin sa da sauri dan ha a taron zaman Malamai na gaggawa dan kuwa shi gani ya ke akwai matsala shi ya sa aka mu su shunan Aisar. Shi kuwa Aisar ya na fita shugaban su ya kira ya na mai sheda ma sa yanda su ka yi da Malam Hamisu,Shugaban na su yayi murna kwarai dan kuwa kamfanin da su ke bincike akai kusa da makarantar ne. Ko da ya aje wayar sai ya tsinci kan sa ya na mai waige waige ko zai sake ganin wannan baiwar,amma yawan daliban da ke kai kawo,da wanda su ka sa masa ido ya sa shi kasa gane wacece wace
"ba mamaki ma ta sami motar garin na su"
abun da ya fa a kenan kafin ya shige motar shi da ya saba basaja da ita ya bar harabar makarantar.
Wacece Bintu
Bintu Bala Mahuta sunan ta,amma Bintu iyar bayi ake kiranta a masarautar su kasancewa suna aya ta ci da da Gimbiya Binta, wato sunan maihaifiyar ta wacce Allah yayiwa rasuwa wajan haihuwar Gimbiya Binta. Mahaifiyar Bintu wacce ta ke babbar baiwar matar sarki wacce ake kira da uwar bayi,ta haifi Bintu yau,washegari aka haifi Gimbiya Binta kuma mahaifiyar Binta ta ce ga garin ku. Kun ga kenan sunan su aya,banbancin ranar haihuwar su kwana aya,dan haka shekarun su ma aya.