← Book details Bintu Diyar Bayi Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 28

Sashe 16

Bintu Diyar Bayi Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Lafiya lumi, shin Baba kuwa an dawo?’’ Bintu ta sake tambayarta, inda Inna ta amsa mata da sun dawo lafiya lumi kan ta shige d’akin ta bayan ta gama alwala, ita ma Bintun buta ta d’auka ta shige band’aki.

Babban gida kuwa a yau rashin armashin sa ya fi na kullum, babban abin da ya bawa Bintu tsoro da ta shiga gidan da rana shi ne ganin Gimbiya K’amariyya cikin tashin hankali. An hana kowa shiga d’akin ta, Bintu ma dan ita ta takawa Gimbiya Binta baya zuwa wajan Gimbiya K’amariyya ya sa ta d’au haske, duk da dai ita ma iyakacin ta bakin kofa ne. Duk yanda Bintu za ta yi domin binciko abinda ke faruwa ta yi, amma abun ya ci tara, babu wanda ya iya bud’ar baki ya ce komai, dan kuwa kowa tsoran ace shi ya fad’a ya ke.

Haka dai Bintu ta koma gida jiki a sanyaye. Ta tadda Inna zaune tsakar gida, kusa da ita ta zauna a gajiye ta na mai fad’in ‘’Inna barka da yammaci, ashe kin taho’’

Bud’ar bakin Inna sai cewa ta yi "Barka dai d’iyarnan, ba dole na taho gida ba, Babban gida yau ba dad’i, fada babu kwanciyar hankali.......’’

‘’Yo to ina fada ina kwanciyar hankali!’’ Baba ne ya katseta, wanda ya fito daga b’and’aki hannun sa ruk'e da buta, sanye cikin shigar bayin Sa’ayrasa. Kujerar tsakar gida ya ja ya zauna kafin ya k’ara da "ai da ni mai fad’a aji ne a wanga masarauta, da aradu ba a je Fabarusa ba, yo to ina bawa d’an bayi, ina ni ina bada shawara?’’

Cikin k’aguwa ta ji abinda ke faruwa Inna ta ce ‘’Shin ya ta kasance ne Malam? K’ak’a an ka yi ne?’’

Murmushin takaici Baba ya saki kan ya fara ba su labarin yanda ta kasance a masarautar Fabarusa. Wato ba k’aramin fad'uwar gaba Bintu  ta ji ba jin Baba ya ce ‘’Da bud'ar bakin Sarki Abdulrahman sai cewa yayi za mu kawar da gaba, za kuma mu ba ku bashin damun hatsai da dabino yanda aka buk’ata daga gare mu dan ceto rayuwar alumma, amma fa da sharad’i.."

"Sharad’in me?’’ Inna da Bintu su ka tambaya a tare.
Baba na mai girgiza kai ya ce ‘’Ku dai tsaya ku ji furucin tsohon banza, sharad’in shi ne, Uban Gabasawa(sarki) ya amra(d’aura) masa d’aya daga cikin d’iyoyinsa mata....’’

Gaban Bintu ne ya yanke ya fad’i. ‘’A amra masa d’aya daga cikin d’iyoyin Uban Gabasa?’’ Inna ta maimaita.

Kai baba ya gyad’a mata, ya k’ara da ‘’Acewarsa, ba zai ba da zallar dukiya har haka ga tsohon abokin gaba ba, ba tare da ya sami madogara ba, kenan amren d’aya daga cikin Gimbiyoyin Sa’ayrasa shi zai sa dole Uban Gabasawa ba zai yi wasa da dukiyar ta su ba, a fad’ar sarkin Fabarusa fa’’

Hannu bisa ha6a Inna ta ce ‘’Hallo ta nan ya hito?  Ba ya taimako sabida da Allah sai an bashi d’iya? Na ji ance sarkin ga ya bawa shekara tamanin baya, tsufa dai ta yi gardama’’

Gaba d’aya hankalin Bintu a tashe ya ke, musamman da tasan alakar Gimbiya K’amriyya da d’an sarkin Fabarusa, wato Yerima Barde, kuma ta san babu shakka Gimbiya K'amariyya za a za6a ba dai Gimbiya Binta ba.

‘’Shin yanzu ina aka kwan?’’ Muryar Inna ta dawo da Bintu daga kogin tunanin da ta fad’a. Baba ya amsa mata da ‘’Tununna dai, an dai ce za a yi shawara, amma gaskiyar lamarin da kyar za mu kiya , jama’a ana cikin wani hali’’

Ya karkata buta ya fara alwala. Jin haka Bintu ta d’aura kai bisa gwiwa cike da tausayin Gimbiya K’amariyya, duk da dai ba kukan ta ba, mutuwar uwar kishiya.

🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪

©Khadija Sidi.....✍🏼

1⃣4⃣

Bangaren Gimbiya Kamariyya kuwa, tunda jakadiya ta sheda mata halin da ake ciki ta kasa samin nutsuwa, gaba d’aya ta fita daga hayyacinta. Washegari da safe ta na kwance bisa cinyar Gimbiya Binta ta na ta kuka kamar k’aramar yarinya, Gimbiya Binta ce mai rarrashinta. Wayarta ta shiga k’ara, da sauri ta duba, ganin wanda ke kiranta ya sa tayi sauran danna wayar ta kara bisa kunnenta.
‘’Yerima mun shiga uku, Yerima ya zan yi?’’

Muryar Barde kad’ai ta isa rikita mai sauraro, murya ce mai tattare da kwarjini, k’asaita da kuma nutsuwa. Duk da tashin hankalin da take ciki be hana ta runtse idanunta ba yayin da ta ji ya ambaci sunanta "K'amariyya.....’’ Sannan ya fara magana cike da k’asaita ‘’Ki kwantar da hankalinki, babu wanda ya isa ya auri matata, fad’amin shi wannan da ki ke magana akai wanene shi? Waye ubansa? Dan wani masarauta ne?’’

‘’Fabarusa, amma ba za mu iya jayayya da shi ba Yerima, sawun giwa ya taka na rak’umi....’’ Ta na magana ne cikin shasshek'ar kuka. Hankali kwance Yerima Barde ya ce "Fad’amin sunansa, dan wani gida ne acikin masarautarmu? Shin da me ya ke tak’ama haka ya tsoratar min da Gimbiya?’’

Ta na mai magana a hankali, dakyar ta iya furta ‘’Yerima Mai Mar-ta-ba ne.....’’
‘’Wanene Mai Martaba?’’ Ya tambaya a takaice. Jin haka ta san be gane in da ta dosa taba, ta ce ‘’Mai Martaba sarkin Fabarusa....’’

'Dif ta ji Yareima Barde, shiru kamar wanda ruwa ya shanye har sai da ta duba wayar dan azatan ta wayar ce ta yanke. Ganin be yanke ba, a hankali ta furta ‘’Yarima...’’

Dogon numfashi ya ja kafin ya ce "Akwai kuskure, babu wannan maganar, ki saurari wayata zuwa anjima.’’ Ya na gama fad’in haka ya katse wayar. Wani sabon kuka Gimbiya K’amariyya ta saka. Cike da tausayi Gimbiya Binta ta ke dubanta, cikin ranta kuwa ta k’udiri niyyar ceto rayuwar ‘yar uwarta. Ta na mai murmushi ta ce da Gimbya K'amariyya ‘’Didi kar ki damu, aradu sai na share mi ki hawaye, in har na kasa aratta kashe ni.’’ Sannan ta d'auki hanyar fita bayin ta na biye da ita.

******** *********

FABARUSA
Yarima Abubakar Abdulrahman wanda aka fi sani da Yarima Barde na Fabarusa, shi ake nufi da wannan kalmar kyau, dan buzu jikan buzu, shi ba sarki ba ya fi sarki iko da mulki. Fari ne sol, dogo mai k’irar nan ada ake danganta su da k’irar zaki. Ya na da faffad’ar kafad’a maji k’arfi da kumari. Sam babu alamar muni a tattare da shi, ya na da dogon hanci da ya zo daf da bakinshi, da manyan idanu mai rikita duk mai kallo. Bak’in gashin da ya sauko tun daga sajenshi ya zagaye fuskarsa, har zuwa saman bakinsa. Abun ku da buzu ya na da suma kamar balarabe, baki wanda yayi lub-lub kwance bisa kansa. Yawan sumar ya sa ba ya damuwa da aski, sai dai ya rage, hakan yasa idan aka gan shi akan yi zaton balarabe ne.

Yarima Barde bai da wata sutura da ya wuce farin tufafi, kullum tufafinsa fari ne k'al, haka zalika rawanin ko hularshi. Mutum ne mai tsafta, isa da k’asaita, wanda hakan kan janyo wasu da dama danganta halinsa da mai shegen girman kai. Shi ne na ishirin wajan mahaifinsa, inda ya ke da yayye goma sha tara, goma sha takwas mata duka suna gidajen mazajensu, da namiji d’aya Abdulkarim wanda ake kira Sadauki, tsirar watanni biyar ne tsakaninsu, shekararsu Talatin da biyu da haihuwa. K’annensa goma, mata biyar da maza biyar.

Kasancewar hali da ya bambanta tsakanin Barde da Sadauki, inda Barde ya ke da nutsuwa hankali da sanin yakamata, Saudauki shi ne shaye shaye, rashin tarbiya da bin mata. Hakan ya sa Barde ya zama mafi soyuwa wajen mahafinnasu Mai Martaba Sarkin Fabarusa, duk da kuwa da yawa ana lak’anta soyayyar d’an da mahaifin akan soyayyar da Sarki ya ke yiwa mahafiyar Barde ne ya shafi d’an na ta, duk da dai ba ta cikin fada, ko ince k’asar Nijar baki d’aya.

Cikin lambu ya ke zaune bisa katuwar darduma, tare da dogarawa uku wanda ke tsaye daga gefe guda. Yanayin da iska ke kad’awa da kuma yanda gayayyaki da furanni su ka yi koreshe shi zai tabbatar maka da daminar bana ta yi kyau a masarautar Fabarusa.

Sanye ya ke cikin farar shadda dinkin yar shara, ga farar hular shi da ta sha kari karkace bisa kan sa. Tunda ya aje wayar Gimbiya K’amariyya ya kasa motsawa daga in da ya ke. Dogon numfashi ya saka, ya na mai k'in gasgata abun da ya ji daga Gimbiya K’amariyya, kasancewar ba ya nan sa’in da Sarkin Sa’ayra da tawagarsa su ka ziyarci Fabarusa.

Ganin ya yunk’ura da niyar tashi, Dogarai su ka yo kansa da sauri, yayin da d’aya daga cikin su ya matso gaban Yarima ya aje farin takalmi gaban sa, su na mai fad’in "Hattara dai magajin Sarki, hattara salamun Yarima’’

Cikin k’asaita ya zura k’afafunsa cikin takalmin, Dogarai su ka rufa ma sa baya, ba su fasa fad’in
"Lafiya salamun Yarima, lafiyarka dama da hauni, dama da hauni lafiya, salamun salamun’’

Isar su bakin kofar lambu, da ke kufar ba ta da tsayi sosai, ga Barde da tsayi mashaAllah. Dogarawa su ka ce "Shafi bisa Yarima, sunkuye salamun’’(ma’ana Badde ya dan sunkuya kada ya bugi hular sa).

Da fad’ar haka Barde ya d’an sunkuya, sai gasu sun fito daga cikin lambun. Duk in da su ka gifta sai ka ji ana mik’a gaisuwa. Shi kuwa ko kallo ba su ishe shi ba, Allah Allah ya ke ya isa ga turakar Sarki, sai dogarawan ke amsa masa gaisuwar, haka kuma ba su basa fasu nusar da shi ba ta hanyar kiran lafiya, duk san da su ka yi arba d abin da zai iya tuntu6e da shi, ko wanda zai iya 6ata shi kamar danshi, ko gidan tururuwa ko rami, sai ka ji su na ambaton
‘’Hattara salamun Yerima’’

Haka har su ka kai ga turakar sarki, in da su ka tadda Jakadiya daga bakin kofa. Ganinta Yerima ya tambaya Sarki shi kad’ai ne zai iya ganinsa? Da ke Yerima Barde dan gaban goshin Jakadiya ne nan da nan ta masa iso. Kai tsaye ya shige yayinda sauran dogarawan su ka yi tsaye su na jiran sa daga waje.
Chapter 16 · 0% Book details