Sashe 23
Bintu Diyar Bayi Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kan ya k’arasa ga 6angaran na ta su ka yi kaci6us a hanya, ta fito za ta turakar sarki. Ganin ta yayi saurin jan linzamin dokin domin tsayawa, har sai da dokin ya fara dara da nagarta (tsalle da rawa) cikin yanayin tada kura, Yarima Nuhu na mai damk’e linzamin gudun kar ya ji shi k’asa ya shiga k’ok’arin tsayar da dokin. Jakadiya na mai d’aga hannun ta na dama da ta d’unkule sama ta ce
‘’kiwo sannu Yarima, ba sake ba manko, kamazuru abokin dabara, amincin ka ya fi ga linzaminka’’
(ta na fahimtar da Yarima Nuhu ya nutsu, hankalin sa ya tafi kan linzamin dokin kada ya kada Shie’’
Ko da ta ga dokin ya tsaya, sai ta sa kai za ta yi gaba, Yarima ya yi saurin dakatar da ita ta hanyar fad’in
‘’ba ki ji ba Jakadiya, wannan zuwan na ki ne’’
Jin haka Jakadiya ta ja ta tsaya, ta na bashi amsa da
‘’anya kuwa ba na ce ah ah ga Yarima ba yayinda na ke kan hanyar da zata sada ni da Babban Bijimi ba?’’
Da sauri Yarima Nuhu ya sauko daga bisa dokin, ya na mai jan linzamin dokin ya dawo daga gefan Jakadiya, wani irin iska mai zafi da k’asa ke busawa duk da dadai la’asar ce sakaliya.
‘’wa ya isa tsayar da Jakadiya a hanyar da zata sada ta da Takawa?’’
Jakadiya na gyad’a kai ta ce
‘’barka da siddi masu duniya’’
‘’barka dai Jakadiya, gani na zo gare ki da buk’atar ganin Bintun arziki ko da kuwa na ‘yan dak’ikai ne’’
cewar Yarima Nuhu ya na duban Jakadiya. Ko da ta d’aga ido ta kalle shi sai ta ga ya mata kwarjini. Sanye ya ke cikin dokakkiyar shadda koriya d’in ‘yan fakistan. Ya d’aura falmaran ruwan zuma bisa, ga farar hular sa irin ta larabawa wacce ba ta da nauyi bisa kan sa, kafar sa kuwa takalmin fata ne sau ciki, shima kore an yi masa ado da d’igon ruwan zuma.
Ganin idan sa ya sa ta kasa yi masa musu kamar yanda ta saba yi masa akan duk abin da ya jib’anci Bintu. Kana ta tsinci kan ta ta na mai fad’in
‘’yo to Yarima ka san abun ga ba haka ake ba, Babban Bijimi ya ce a killace d’iyar bayin nan, amma tin da ka zo da kan ka yi tsimayi cikin lambu, zan sa a rako ta, amma kada ka ruk’e ta, kasan amare ba a san ana ganin su hakan nan sakaka saboda.....’’
‘’ina godiya Jakadiya, ba zan manta da wannan alfarma da ki ka yi a gare ni ba’’
Yarima Nuhu yayi saurin katse ta dan ba ya san jin maganar da Jakadiya ke masa game da auren Bintu, ya na mai jan linzamin dokin sa yayi hanya da za ta sada shi da lambun ba tare da ya jira amsar Jakadiya ba.
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
®
✏📖
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
GARGA'DI
KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.
©Khadija Sidi.....✍🏼
2⃣3⃣
Kasancewar ruwa be sauka ba, yawanci shuke shuken da ke cikin lambun duk a bushe su ke, sai kukan tsuntsaye da kwari ne ke tashi sama sama. Dokin sa ya saka ya na shawagi cikin lambun, yayin da ya sami wata shifid’a da ke k’ark’ashi bishiyar mangwaro, ya cire takalmin shi, ya zauna sannan ya kuma kishingid’a kan tintin da ke jere bisa shimfid’ar.
Be dad’e da zama ba ya hangi wata da ya kasa gane ko wacece ta shigo lambun ta na mai waige waige da alama akwai wanda ta ke dubawa. Daga in da ya ke zaune ya k’ura ma ta ido cikin kokanton abun da kwakwalwar sa ke fad’a masa.
Sanye ta ke cikin doguwar riga ruwan zuma, an mata aikin hannu irin na sarauta tun daga sama har izuwa k'asan rigar da jan zare. Kan ta nad’e da jan kallabi, haka ma talkamin da ke sanye k’afar ta ja ne. Ganin ta nufu in da ya ke sai da ya tashi zaune daga kishingid'ar da yayi, ya na mai gyara zama, tafiyar ta ya dad’a gasgata masa abin da ya ke gani, babu shakka ita ce d’in ce.
Tin da ta hango shi gaban ta ya shiga fad’uwa, ba a san ran ta ta fito ba, dan ko da Jakadiya ta zo ta tadda tela ta sa ta gaba ta na gwada kayan da aka sa tela ta d’in ka mata, ta na kan na k'arshe Jakadiya ta ce Yarima Nuhu na da buk’atar ganin ta.Ta so cire kayan da ke jikin ta dan ta fi gane shigar su na bayi, amma Jakadiya ta ce ah ah, kada ta 6ata lokaci ta yi maza ta je ta same shi yanzu yanzu cikin Sirri.
Gaba d’aya ta kasa sakewa, dan ta kwana biyu ba ta saka k'afar ta waje ba,gashi kayan da ke sanye jikin ta da ma takalmin da ke k’afar ta duk sun saka ta na jin kan ta daban, abun da ba a saba ba, gashi a dole ta na ji ta na gani an sa ta gaba da gyara, lalle sai ta yi kama d’iyar saraki, ita dai wannan masifa ba ta ta6a ganin irin shi ba.
Da wanan tunani ta k’arasa gaban sa, amma ko da ta masa sallama ta na mai zubewa a k’asa kamar yanda ta saba duk sanda ya bayyana gaban ta, sai ta ji shiru be amsa ba. Ba ta gusheba kan ta sunkuye ta sake masa sallamar a karo na biyu, shi ma shiru, na ukun da ta sake ne ta d’aga ido da niyar kallan in da ya ke zaune, sai tsintar idanun ta tayi cikin na sa, ya taso izuwa gaban ta ya durk'usa ya na kallan ta kamar zai had'ye ta. Cikin fad’uwar gaba ta yi saurin yin k’asa da nata idanun ta tana mai fad’in tuba
‘’tuba na ke Yarima’’
Niamey
‘Bangaran Aisar kuwa, yau take kwana uku da dawowar su Nijar daga k’asar Ingila, in da aka duba mai girma shugaban k’asa Gaddafi Nur. Zaune Shugaba Gaddafi ya ke a k'awataccin falon sa, tare da babban d’an sa wanda ake kira Junaid da kuma Aisar. Jikin na sa Alhamdulillahi yayi kyau kwaran gaske, wanda hakan ya bashi dama zantawa da 'ya'yan na sa akan abubuwan yau da kullum.
Aisar kuwa kamar kullum, yanzun haka ma gangan jikan sa kad’ai ke wajan, amma zuciyar sa na ga Bintu, tunanin Bintu ya hana shi sakat, ya jagula tunanin sa har ya na da yak'inin cewa muddun ba zuwa yayi gare ta ba zai iya shiga wani hali.
Cikin wannan hali ne kamar daga sama ya ji Shugaba Gaddafi ya ambato sunan Masarautar ta su Bintu, wato Sa’ayrasa. Wanda haka ya sa yayi saurin dawowa cikin hankalin sa, ya na mai san jin ainihin maganar da shugaba ya ke.
Nan ya sami amsar da ya ke buk’ata, takardu guda biyu Shugaba ya mik'awa Junaidu ya na mai fad’in
‘’gashi nan Junaidu wasik’ar gayyata ce daga Masarautar Fabarusa da Sa'ayrasa, wanda za su gudanar da auratayya tsakanin junan su nan da mako guda’’
Cike da farin ciki, kafin ma Junaidu ya kar6a Aisar yayi saurin sa hannu ya kar6e ya na mai fad’in
‘’mashaAllahu, wato Bintu ta yi gaskiya auratayya ce zai kawo silar k'arshen gaba tsakanin wannan Masarautun, wannnan yarinya ba dai kwakwalwa ba’’
Ya na magana ne ya na k’ok’arin bud'e ma'jin waasikar, be san daga Shugabn k’asa har Junaidu kallan sa su ke cike da mamaki ba, musammam Junaidu da be ta6a jin zance wata mace daga bakin Aisar ba, ya ce
‘’Bintu? Wacece Bintu?’’
Sai a sannan Aisar ya tuna ashe fa a zahiri ya yi maganar, ya na mai duban Junaidu hannun sa rike da wasikar da ya bud’e ya ce
‘’wata d’aliba ta ce a makaranta da na koyar mai kwazo da hazak’a, bakin ta na fara jin auratayya na iya kawo k’arshen gaba, yar Masarautar Sa’ayrasa ce’’
‘’yar wani hakimi ce a Masarautar?’’ Shugaba Gaddafi ya tambaya cike da farin cikin ko dai ya kusa samin sirika ne. Ga mamakin sa sai ji yayi Aisar ya amsa masa da
‘’d’iyar bayi ce.....’’
Shiru ne ya biyo baya, yayinda Aisar ya duk’ufa kan karanta wasik’ar gayyata na musammam da aka aiko daga Masarautar Sa’ayrasa, cike da mamaki ya ce
‘’gide Sarkin Fabarusa da kan sa zai auri d’iyar Sarkin Sa’ayrasa? Na yi zatan tsakanin ‘ya ‘yan su ne? ko da shi ke harkar manya ba a cewa komai’’
‘’ai auren dama za a yi ne ba hakan nan bak’atatan ba, za su yi ne saboda taimako da Sarki Sule na Sa'ayrasa ya nema daga Sarki Abdulraman na Fabarusa akan fari da ya addabi Masarautar ta su, ka na Ingila shi ya ba ka da labari"
Aisar na mai duban sunan Fatima da ya bayyana bisa wasik’ar ya ce
‘’dama ya na da d’iya Fatima ne? Na san dai akwai wata d’iyar sa Binta wacce na koyar a makarantar Sovereign’’
‘’ni ma dai Gimbiya K’amariyya kawai na sani da ita aka fi fita damawa a masarautar ta su, in dai akwai Fatima sai dai ta kasance kanwa a gare ta, yo to ai Binta Fatima ta ke, ko shakka babu d’alibar ta ka ce ma" Junaidu ne ya amsa masa.
Aisar na mai d’aga kafad’a cike da nuna an yi ba daidai ba ya ce
'’kai amma yarinya ce sosai, gaskiya auren nan be dace ba bata fi shekara goma shabiyar ba, ina zancen makarantar ta kuma fa? Wannan ai tauye hakki ne, me zai hana a aurar da yayarta ta tunda ita ta kai munzali?'’