← Book details Bintu Diyar Bayi Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 28

Sashe 22

Bintu Diyar Bayi Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

‘’Ko ba Bintu ba? Tak’ama da isa ba ta gada ba, amma Allah ya mata shi a halittar ta, kin ga baiwar Ubangiji ko? Ba ki ga tsayinta da dirinta ba ne? Su kad’ai sun isa nuna tak’ama, shi yasa na ke mai bakin cikin rasa ta da zan yi ta sanadiyar san rai irin na k’auna ta.’’

Kamar mai shirin yin kuka Gimbiya Binta ta furta ‘’Yarima......Bintu d’iyar bayi ce!’’

Ya na mai had’e rai ya ce ‘’Hakanan k'auna ce ta na ke kuma rainon san ta cikin raina tun kafin na mallaki hankalina, ina jin ta har jinin jiki na duk da kuwa ita d’iyar bayi ce, ni kuma d’an saraki, ki sani na san da duk wani tukgun da ki ka kulla ke da K’amariyya tare da d’aurin gindin Jakadiya! Har ki na da bakin kuka dan ance za ki bar k’asa? Da da ki ke gina ramin muguntar ba ki san za ki iya wad’awa ba?’’

Kuka Gimbiya Binta ta sa, hawaye d'aya na bin d’aya ta ce
‘’Ina soyayya da k’auna ta jini da amintaka? Ni fa ‘yar uwar ka ce jini d'aya, za ka za6i d’iyar bayi akan yar uwarka? Ka ce da ni wasa ka ke, ba ka san wanga d'iyar bayi.’’

Tashi tsaye ya yi, ya na mai danna idanunsa cikin nata ya ce
‘’Ni abinda ya ke ban takaici kenan, jini na ta san ta iya had’a tuggu haka? Kin san abun da ki ke shirin saka babban mutum kamar Takawa ya aikata kuwa? Kin san girman laifin kuwa? Ina mai gargad’inki, muddin ki na so mu shirya ki gaggauta kunce wannan sak’ar da ki ka kulla tun kan ya k’ure miki’’
Ya juya zai fita, har ya kai k’ofa Gimbiya Binta ta k’ara kiran sunan sa ‘’Yarima....’’

A hankali ya juyo ya na dubanta, idanunsa sun kad’a sun yi jajur. Gimbiya Binta na mai hawaye ta sake furta ‘’Bintu d’iyar bayi ce......’’

‘’Ita na ke kauna kanwata, idan har ki na so na da farin ciki kar ki ja min asarar Bintu ta ta arziki’’ Ya na gama magana ya fice, ya bar Gimbiya Binta ta na mai bin bayansa da kallo.

🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪

GARGA'DI

KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE

2⃣1⃣

Khadija Sidi......✍🏼

Duniya ta yiwa Gimbiya Binta zafi, ba ta san sanda ta durkushe kasa ta na mai sakin kuka mai tsanani. Gimbiya K’amariyya ce ta fito hannun ta ruk’e da sakon Bintu, gani Gimbiya Binta cikin tashin hankali ya sa ta sakin sak’on na Bintu bisa kujera, ta k'arasa gare ta da sauri ta na mai waige waige cikin fargaban sharrin masu tsirku. d’ago ta yi ta na fad’in
‘’haba ‘yar uwa, ba yanzu mu ka gama rarrashin ki ba, me yayi zafi Binta shi ba wuta ba? Maza tashi mu yi ciki kar bayi su gani su sami abin yad’awa’’

Kanta ta d’aura bisa kafad’ar Gimbiya K’amariyya ta na mai fad’in
‘’na shiga uku Didi, duniya na neman juya min baya, hatta d’an uwa na ya fi kaunar d’iyar bayi akai na ni da na ke cikin umman sa’’

Gimbiya K’amariyya na mai buga bayan Gimbiya Binta a hankali cikin rarrashi, ta ja ta su ka yi ciki. Sai da su ka shiga d’akin Gimbiya K'amariyya, ta sallami baiwar da ke cikin d’akin sannan ta zaunar da Gimbiya Binta bisa gado ta nemi ba'asi akan tsakanin Yarima Nuhu da Bintu. Nan Gimbiya ta fad’a mata yanda ta kasance tsakanin ta da Yarima Nuhu, jin haka ba ta yi mamaki ba, sai ma tsaki da ta ja ta ce
‘’shiga shigila gand’e ma shiga rawar takai! Har kya ma damu da Yarima Nuhu, in dai wajan shiga shirgin da ba na shi ba ne in aka gan shi kowa ya shafa fatiha, ya manta ba kauna ba, ciki d’aya su ka hito da Bintu! kar ki wani damu, zancen komawar ki k'asar Nigeria kuwa InshaAllahu zance ne, kuma in dai Aisar ne ya ma zama na ki an gama’’

Gimbiya Binta na mai kwantar da kan ta bisa gwiwar Gimbiya K’amariyya ta ce
‘’ina godiya Didi, dan Allah kar ki bari Takawa ya raba ni da farin cikin rai na’’
Ta na shafa kan ta ta ce
‘’in dai wannan ne kar ki damu, bayan auren d’iyar bayi na miki alk'awarin shedawa Hajja Kilishi lamarin ki da Aisar, sai a san yanda za a bullowa lamarin, ko?’’

Ta k’arasa maganar ne ta na mai d'ago fuskar yar uwar ta ta, cike da farinciki Gimbiya Binta ta tsinci kan ta ta na mai washe hakora, ashe dai da rabo. Haka dai su ka cigaba da hirar su cikin kwanciyar hankali har Gimbiya Binta ta mance da maganar Yarima Nuhu bare ma ya dame ta.

Bintu kuwa ko da ta samu ta ganta d'akin Hajja Kilishi, nan ta yi zaune abun ta, da Hajja Kilishi ta tambayi sak’on na ta, sai cewa ta yi ba ta ga Gimbiya K’amariyya ba. Hajja na k'orafin dama ba ta ce Bintu ta je da kan ta ba, ta sake aika wata baiwar ta karb’o sak’on, sannan ta bawa Jakadiya da ta zo tafiya da Bintu.
Sak’onni ne na kayan gyra jiki wanda ya had’a da su dilka, halawa, kalta, kurkum dadai duk sauran kayan gyaran jiki wanda musammam Hajja Kilishi ta sa aka mata sautin su daga Agadez.

A daren ranar Bintu ta fara shiga hannu, mai gyaran jiki na yi, mai koya mata kissa da dabarun zaman fada na yi, mai mata jawabi yanda sabuwar rayuwar ta za ta kasance na yi. Telar babban gida ma ba a barta a baya ba, haka ta yi tattaki ta zo ta gwada Bintu tare da tafiya da damin siturun da Hajja Kilishi ta zab’arwa Bintu. Hatta gashin Bintu da Marry ta yanke sai da Jakadiya ta saita almakashi ta daidaitasu, ta na mai tambayar ya aka yi gashi rabi dogo rabi gajere. A lalle sai an wayar da Bintu ta fito fes kamar d’iyar saraki. Ita kuwa Bintu ba ta fasa kuka da kewar Innar ta ba.

🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪

GARGA'DI

KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.

©Khadija Sidi.....✍🏼

2⃣2⃣

Daga ranar zuwa washagari sai ga Bintu an fara wasai. Washagari da safe, Bintu da Jakadiya tare su ka zauna karin kumallo, cin abinci ma sai Jakadiya ta koya mata dan kar ta je ta bada su a masarautar abokan gaba. Abinci ne kala kala na alfarma irin na gidan saraki, kai ka ce ba fari ake a masarautar ba. Bintu na gani Innar ta ce ta fad’o mata a rai, ba makawa ta san yanzu ta na nan ta na fama da hatsi da dusa, amma ita nan ga abinci har da na b’arna a gaban ta.

Da kyar ta iya cin kad’an daga abinci, hakan ma sai da Jakadiya ta sab’ar ma ta, ta na mai tuhumar ta da tsabar mugunta ne ya sa Bintu k'in cin abinci, dan a ganta ramammiya ta sa ace tsabar yunwar da ke addabar Masarautar su ne, ko kuwa cutar yunwa ya kama ta.

Kan wannan jaraba na Jakadiya ne ya sa ta bi yanda Jakadiya ta ce, ta na mai gwada mata yanda za ta yi haka har dai ta ta6a wanda za ta iya, a dole Jakadiya ta hakura ta rabu da ita.

***** ******
Sai da ya rage saura sati guda auren Bintu sannan Innar ta ta yarda ta zo wajan Jakadiya ganin Bintu, hakan ma sai da Jakadiya ta matsa tukunna. Ganin yanda Bintu ta canza ta yi wasai fatar ta har shek’I ya ke, duk da dai ta yi wani irin rama sai da ta ji dad’i. Sun dad’e suna hira, nan ta ke sheda mata sarki ya ‘yan ta ta. Sam Inna ba ta yi wani murna ba, a fad’an ta da hatsarin da aka jefa d’iyar ta har gwara a bar ta d’iyar bayi har abada. Da Inna ta zo tafiya da kyar Bintu ta sake ta, nan fa taita sana'ar ta ta, wato kuka babu kuma mai rarrashin ta bare ace mata ya isa.

Bayin da aka amince da su, wanda su aka yarda su shiga wajan Jakadiya kuwa kishi su ke da Bintu, musammam da su ka ji ashe ita ce za a aurawa sarki ba Binta ba, ga gyara da hidima da ake mata sai kace wata d’iyar saraki. Baiwa ta zama ‘yan tacciya. Da yawan su kan ce kukan munafurci Bintu ta ke, wasu kuwa fad’i suke ina ma su an Bintu, da kakarsu ta yanke sak’a.

Babban gida kuwa Gimbiya Binta Hajja Kilishi ta sa a gaba ta na mata gyaran jikin bogi, a lalle ayi basaja gudun ‘yan tsirku na fada. Amma a zahirin gaskiya Sarki ya sa a duba makaranta mai kyau da tsada k’asar Nigeria domin mayar da ita can. Har ila yau daga Gimbiya Binta har K'amariyya ba su fasa k’ulle k’ulle da shige da fice ba dan neman yanda za a yi Takawa ya sauya shawara, amma dai abin ya ci tira. Har kar gaban ta ya sa ko ta kan Bintu ba ta bi, bare ta sa ta a idanun ta.

Haka ma Yarima Nuhu, wanda ya rame a ‘yan kwanaki kad’an tsabagen fargaba auren Bintu da ke gabatowa bilhakki. Gashi gaba d’aya an 6oye Bintu cikin fada, raban da ya sa ta a ido tun randa ya zo ya tadda ita da Gimbiya Binta ta na mata cin kashi, duk yanda zai yi ya gan ta yayi amma babu Bintu babu alamar Bintu. Daga bisani ya yanke hukuncin tarar aradu da daka, bayan sun dawo daga shawagi, ko sauka daga dokin sa be yi ba, yayi tattaki zuwa wajan Jakadiya da buk’atar sa na ganin Bintu
Chapter 22 · 0% Book details