← Book details Bintu Diyar Bayi Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 28

Sashe 25

Bintu Diyar Bayi Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

‘’ni ma dai Gimbiya K’amariyya kawai na sani da ita aka fi fita damawa a masarautar ta su, in dai akwai Fatima sai dai ta kasance kanwa a gare ta, yo to ai Binta Fatima ta ke, ko shakka babu d’alibar ta ka ce ma" Junaidu ne ya amsa masa.

Aisar na mai d’aga kafad’a cike da nuna an yi ba daidai ba ya ce
'’kai amma yarinya ce sosai, gaskiya auren nan be dace ba bata fi shekara goma shabiyar ba, ina zancen makarantar ta kuma fa? Wannan ai tauye hakki ne, me zai hana a aurar da yayarta ta tunda ita ta kai munzali?'’

Duk abun nan ya na yi ne ba dan kowa ba sai dan Bintu, ta na yawan fad’o masa a rai tun sanda ya ji batun farin da ya addabi k’asar su, rashin lafiya Shugaba Gaddafi shi ya hana shi sakat, yo to ana ta kai wake ta kaya, amma idan ya tuna rayuwar fada ta ke, sai hankalin sa ya kwanta dan ya tabbatar ba za ta6a kwana da yunwa ba. Amma jin za a aurar da Gimbiya Binta ya sa hankalin shi tashi, dan babu mamaki k’arshen karatun Bintu kenan, kila ma ta na cikin bayin da za tura Fabarusa domin kula da Gimbiya Binta. Ya kai duban sa ga Shugaban Gaddafi wanda tun da su ka fara magana be tanka ba, ya ce
‘’Baba na ka duba wannan lamarin saboda Allah, wannan nauyin na Gwamnati ne, ceto rayukan al’umma, ba na Masarautu ba, mun san kana yi, kuma kai me yi ne’’

Maimakon Shugaba Gaddafi ya bashi amsa sai murmushi ya sakarwa d’an na sa. Junaidu ne ya bashi amsa da toh

‘’toh d’an k’asa mai kishin k’asa, kana ina san da Baba ya sa aka hannu za a fitar da damin kud'i dan aika abinci ga Masarautar’’

‘’to me ake jira ba a aika ba? Me ya kawo jinkirin? In dai rashin lafiyar Baba ne, Baba ya ji sauki, a yi maza a aika dan a taimaki bayain Allah’’
Cewar Aisar cike da damuwa. Shugaba Gaddafi na masa nuni ga takardar hannun sa ya ce

‘’ga amsar nan bisa hannun ka, jin Masautar Fabarusa za ta taimakawa S’ayrasa, da kuma niyar su na auratayya ya sa mu ka dakata, muddin hakan zai kawo k’arshen gaban da ke tsakanin su toh fa babu ruwan Gwamnati da shiga lamarin, sai dai mu bada gudunmawa ta hanyar amsa gayyata da kuma k’ara mu su k’arfin gwiwa, kud’in da mu ka ware dan ciyar da masarautar kuma ya tafi ga wani aiki wanda zai amfane su ta wani fannin’’

Aisar na mai girgiza kai ya ce
‘’na fahimta, Baba na san saboda yanayin jikin ka ba za ka sami halartar d’aurin auren ba, in zan sami dama ina so na zama d’aya daga cikin wanda za su wakilce ka’’

Jin haka Junaidu ya san hakan nan yanda Aisar ba ya san duk wani abu da zai had’a shi da siyasa, ya san banza ba ta kai zomo kasuwa, ya ce
‘’ah ah ka manta ranar za ku koma Ingila domin duba jikin Baba? Ka bari an hutasshe ka ni na je’’

Duk da yayi maganar ne cike da zolaya, sai da Aisar ya tsuke fuska, dan kuwa gani ya ke yanda ya ci burin ganin Bintu, duk wanda zai hana shi ganin Bintu shi an mak’iyin shi, jin za a je Masarautar su ya san tun da d’iyar bayi ce ko shakka babu zai gan ta, ko dan ya sami daman ganin iyayen ta, ya ji ya za su yi da karatun Bintu tun da dai ita Gimbiya Binta aure za a mata, kuma ya rok’e su da kada su cire ta daga makaranta, idan ya kama ne ya d’au nauyin ta, zai yi.

Ya na mai tsuke fuska ya ce
‘’zai fi kyau dai kai ka koma Ingila, tun da Baba ya ji sauki, duba shi kawai za a yi ina ga babu amfanin zuwa da ni’’

Shugaba Gaddafi ya ce
‘’to tsakanin ku, idan dukan ku biyun ne ma za su d’aurin auren daidai ne, ina jin sauki sosai, ba na buk’atar rakiyar ku’’
Murmushin jin dad’i Aisar ya saka, cikin ran sa ya na mai fad’in
‘’Bintu na ina nan tafe, ki kwantar da hankalin ki babu mai cire ki daga karatun ki’’

🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
[5/15, 7:22 PM] ‪+234 703 962 5239‬: ®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪

GARGA'DI

KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.

🕊Special shoutout to all the Atikus🙋🏽🙋🏽 onelove💞😘😘

©Khadija Sidi.....✍🏼

2⃣4⃣

Kallon Bintu Yarima Nuhu ya ke cike da so da k’auna, murya can k’asa ya kira sunan ta
‘’Bintun arzki, dama haka ki ke da kyau? Anya kuwa Bintu zan juri rashin ki?’’
Kanta a k’asa ta d’an ja da baya, dan kuwa ganin Yarima Nuhu durkushe gabanta ba k’aramin takura ta yi ba, dad’in dad’awa yau kuma ya zo mata da saban salo na magana. Ai kuwa sai ta yi kamar ba ta ji ba. Kana ta ce

‘’Allah shi taimaki Yarima, Barka da yammaci, Jakadiya ce ta ce Yarima na da buk’atar gani na’’

Hannunta da ke rawa ya bi da kallo, in da idanunsa suka sauka bisa zoben hannunta, sai kyalli da shek’i ya ke, ba tare da wani tunani ba ya d'aura hannunsa bisa hannun lta mai d’auke da zoben. Jin sabon salo hannun Yarima Nuhu bisa na ta ya sa Bintu janye hannunta a firgice cikin sauri kamar wacce aka d'aurawa garwashi, nan ta shiga yarce hannun tana ka6ewa kamar wanda wani abu ya mak’ale. Gaba d’aya ta firgice idanunta na shirin kawo ruwa.

Cike da mamaki Yarima Nuhu ya ke dubanta, kana ya ce
‘’Haka ki ke k’yank’yamina Bintu? Duk wannan d’aga hankalin da yarfe hannun dan na ta6a ki ne?’’

Sai a sannan ta farga da abun da ta ke, tuni ta zube hannayen nata a k'asa, idanunta na fidda kwallar da dama su ke mak’ale cikin kwayar idanunta, fad’i ta ke.

‘’Na tuba, kamin rai, na tuba, ba na so na mutu Yarima, aradu ba na san na rasa raina.’’
Ya na mai jinjina maganar cikin ransa, cike da mamaki ya ce da Bintu
‘’Wa ya ce za ki mutu?’’

Zuciyarta d’aya, har ila yau ba ta fasa hawaye ba ta ce
‘’Iya Dije ce’’
‘’Iya Dije?’’
Yarima Nuhu ya maimaita. Bintu na mai gyad’a kai ta ce
‘’Eh Iya Dije, ta ce idan har na sake na bari namiji ya ta6a ni mutuwa zan yi, kwankwatsi ma kuwa.’’

Ga mamakinta sai gani ta yi Yarima Nuhu ya jefa kansa baya ya na mai saka dariya mai sauti. Cikin rashin fahimta Bintu ta duk’ar da kai jiki na rawa.

Tashi ya yi, ya koma wajan zamansa na fari, yayinda ya zauna ya na mai kishingid’a bisa tintin cike da mulki da sarauta. Har a lokacin idanunsa kanta ya ke, fuskarsa kunshe da murmushi bayan wasu d’an dakik’ai ya ce
‘’Bintu d’ago ki kalle ni.'’
A hankali ta d’ago kanta, cikin bin umarni ta kai kallonta gareshi, fuskarta cike da hawaye. Gefansa ya mata nuni da shi sannan ya ce
‘’Dawo nan ki zauna.’’
Ta na fidda kwayen idanu ta ce
‘’Iye?’’
Kai ya gyad’a mata cikin jaddadawa, bai kuma fasa mata murmushi wanda ke k'ara masa kyau ba. Cike da shakku Bintu ta tashi a hankali, inda ya mata nuni nan ta je ta zauna, amma can nesa da shi.

Ya na mai jin dad’in maganar Bintu, duk da yayi mamaki ace baiwa kamar Bintu batasan komai ba har haka, sakamakon shaidar rashin kamun kai da ake yiwa matasan bayi irinta. Kana ya nisa tare da fad’in
‘’Iya Dije ki ka ce kowa? Ko shakka babu ta yi gaskiya’’

A tsorace Bintu ta d’ago ta kalleshi ta na mai fad’in
‘’Shikenan ni Bintu mutuwa zan yi, na shiga uku na lalace.’’

Dakyar Yarima ya iya kunshe dariyar da ta kusa cin k’arfinsa, ya na mai k'ok’arin d’aure fuska ya ce
‘’Banda yanzu, ba za ki mutu ba tunda ni ba ta6a ki, hallo na yi ba gangan ba, zoben hannunki na ta6a, amma kar ki yarda wani ya ta6a ki muddin ki na so ki yi tsayin rai, musamman idan aka kai ki wannan Masarauta na Fabarusa, ko da kuwa Sarki Abdulrahman ne da kansa.’’

Ta na mai tunani yo dama me zai sa Sarki Abdulrahman ya ta6a ta, ta yi saurin amsawa da
‘’Aeadun Allah ba zan bari ba, hallo ni ma ba na zuwa kusa da maza, Inna ta ta hana’’

Yarima na mai duban zoben hannun ta wanda hakan nan ya ji ya tsole masa ido, ya ce
‘’Wagga zobe na hannunki, wa ya baki?”

Zuciyar Bintu d’aya ta amsa masa da
‘’Monsieur Aisar ne ya bani ajiya.’’

Wani bakin kishi ne ya ta so masa jin sunan namiji bakin Bintu, nan da nan ya sha mur ya na mai kausasa murya ya ce
‘’Akan wani dalili zai baki zobe ajiya? Shi waye d’in ki? Ashe dama ki na soyayya?’’

Cikin k’ok’arin kare kai ta ce
‘’Wallahi ba na soyayya, ban ta6a yi ba, idan k’arya na ke aratta kashe ni, Monsieur ne a École ya ce na ajiye masa.’’
‘’Ciro zoben ki bani’’
Chapter 25 · 0% Book details