← Book details Bintu Diyar Bayi Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 28

Sashe 10

Bintu Diyar Bayi Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kuwa Iya Dije amsawa ta yi "kwankwatsi ma kuwa, ba mai bi na bashin rantsuwa, ai ga d’iyar nanniya(ai ga yarinyar nan), gani ya kori ji’’ kan Bintu ta ankara iya dije ta ja dan hijabin jikin ta, sai ga daga hijabin har kallabin na ta hannun Iya Dije, dan kunya kamar k’asa ta tsage ta rufe, musammam yanda rabin gashin na ta ya sauka har gadan baya, rabi ya tsaya iya wuya. Ta so yanke sauran dan ta daidai ta su amma sammakon da Iya Dije ta doka mata ya sa ba ta sami dama ba.

Cike da tausayi Aisar ya ke duban ta, ji yake kamar ya ruke ta ya kwashe mata gaba d’aya damuwar ya mayar zuwa kan shi. Gashi saboda shi an wulak’an ta ta, har aka mata cin zarafi ta hanyar yanke mata suma. Malam Hashim kuwa duban sa ga Aisar ya ke, in da zuciyar sa ke jaddada masa lalle watan rufe wannan makaran ta tasu ce ta tsaya...

"Bintu....’’ ya kira sunan ta cikin wani yanayi ya na mai sassauta kullin nakatayal (Neck-tie) din wuyar sa, dan ji yake kamar numfashi ba ya isar sa tsabagen 6acin rai. Hatta Iya Dije da Malam Hashim sai da su ka kai kallan su ga Aisar, ita kuwa Bintu kasa d’aga ido ta kalle shi ta yi. Malam Hashim ya gyara murya ganin yanayin 6acin ran da Aisar ya shiga ya ce "Ina Iya Dije, zai fi kyau ku d’an ba mu hili (fili) mu zanta da Malam Aisar’’ ta na mai mik’awa Bintu kallabi da hijabin ta, ta ce ‘’ye to ai sai mu fita rariya (sai mu fita waje), Bintu mu tahi ko?’’

Da saurin ta, ta karb’a ta d’aura kallabin kafin ta sanya hijabin na ta, Iya Dije a gaba ta na biye da ita, idanun Aisar kan Bintu har su ka fita. Shiru ne ya biyo baya na wani d’an mintina, kafin Malam Hashim ya d’aure ya ce ‘’na san abun da ke ran ka, amma ina mai tabbatar ma ka makamancin haka be ta6a faruwa a wanga École ba, wanga da ya faru ma tsautsayi ne Monsieur Aisar (Malam Aisar)’’

‘’ka na nufin baka san d’aliban ka su na aje makami a tare da su ba Monsieur (Malam)? Ai na zaci k’aida ne hukumar makaranta ta na bibiyan d’akin d’alibai lokaci lokaci dan binciken kayan su domin gudun irin haka? Me ke faruwa a wanga École ? (me ke faruwa a makarantar nan?) Shin me ku ke yi da har irin haka ka iya faru? Ya ilahi da ta kashe d’iyar mutane fa!!!’’ fad’in Aisar wanda tun da ya fara maganar kansa ke kallan silin. Malam Hashim kuwa zufa ne ya lullub’e shi kana ya ce ‘’lillahi warasulihi Monsieur (Malam) abin ga da ya faru tsautsayi nai, na kuma yi maka alkawarin duk matakin da za ka d’auka daidai ta (daidai ne), amma kar ya shafi wanga École(Makaranta) ’’

Sai a sannan Aisar ya mayar da kallan sa ga Malam Hashim, kana ya ce ‘’wannan laifi ne da ba zan iya d’auke ido akai ba, kasan k’asar mu ta Nijar k’asa ce da ke san jama’ar cikin ta, mai daraja dukkan abu mai numfashin da ke cikin ta, a matsayi na na d’an k’asa mai kishin k’asan ga, na ga irin haka na d’auke kai tabbas na ci amanar k’asa ta’’. Jin haka hankalin Malam Hashim ne ya tashi. Sai gashi ya taso ya zo gaban Aisar ya na mai ruk’o hannun sa ya ce "wanga École (makaranta) ta kunshi d’alibai daga kowani sassa da yankunan jamhuriyar Nijar, ruhe (rufe) ta ba k’aramin asara ba ce ga k’asar ga, kai ka sani k’asar mu na buk’atar makarantu ma su inganci irin Sovereign.......’’

"ka na nufin ita kad’ai ta École mai inganci a wanga k’asa ta mu? (ita kad’ai ce makaranta mai inganci a wanga k’asa ta mu?) Kada fa ka nemi ka zagi k’asa ta Monsieur Hashim!’’ Aisar ya katse shi cike da nuna 6acin rai. Cikin sauri Malam Hashim ya girgiza kai ya ce ‘’ba haka na ke nufi ba Monsieur Aisar, yo to na fad’i haka ban yi ma k’asa ta adalci ba, aradu ma kuwa, École (Makaranta) kuwa masu inganci mu ke da su a k’asar mu, amma ruheta kan iya jawo asarar d’aya daga cikin su, sabida Allahu da manzan sa wanga batu ka duba, duk hukunci da za yiwa wannan d’alibar ka mata ita ta jawa kan ta, yo mi zan ce zanin aro ya toye? amma kada laifin wani ya shafi wani’’

Bayan nazari na wani d’an lokaci Aisar ya ce "ko wani hukumci ka ce Monsieur Hashim?’’ Malam Hashim ya jinjina kai kafin ya ce ‘’ko wani hukunci muddin ba zai shafi wanga École ba, ba zai kuma shafi jarabawar gama sakandiri da d’iyar ta ke rubutawa ba....’’ wani irin kallo Aisar ya watsa masa jin maganar ta sa. Da sauri Malam Hashim ya ce ‘’ba dan d’yar ba Monsieur Aisar, dan cigban k’asar mu, ka ga idan ya shafi jarabawar hallau ya shafi cigaban k’asa ta fannin karatu, k’ak’a ka gani?’’

Tashi yayi ya na bai gyara nakatayal(neck-tie) d’in sa, sannan ya ce ‘’na fahimce ka, zan mata hukunci daidai da yanda ta aikatawa yar uwar ta’’ ya na gama magana ya fice in da ya bar Malam Hashim ya na mai zubewa bisa kujera yayinda ya ke goga zufan da shi kan sa be san ya tsefo masa haka da yawan gaske ba. A waje Aisar ya tadda Bintu da Iya Dije tsaye suna jiran tsammani, be iya kallan in da Bintu ta ke ba tsabagen haushin kan sa da ya ke ji akan abun da ya jawo mata. Kana ya dubi Iya Dije ya ce ‘’ko zan iya samin Ciseaux da sabuwar reza gun ki Iya Dije?’’ Cikin fad’uwar gaba Bintu ta d’ago kai ta na mai duban Malam Aisar, sai a sannan ta lura da yanayin shi da ya canza gaba d’aya, ya zama kamar ba shi ba tsabar 6acin rai. Murya a sanyaye ta ce ‘’dan mai sama Monsieur (Malam) ayi hakuri a bar maganar ga, yo to menene dan an aske gashin niya?(menene dan an aske gashi na), in dai dan niya ne arudu na gafarce ta’’

Kallan ta Aisar yayi ba tare da ya tanka mata ba ya sake maimaitawa Iya Dije tambayar, ganin haka Bintu ta sawa bakin ta sakata, in da Iya Dije ta amsa da ta na da su duka, ya ce to ta kawo masa filin taron d’alibai(assembly ground) yanzu ba tare da 6ata lokaci ba. Ya wuce ya bar Bintu da bin bayan sa da ido. Ita kuwa Iya Dije jiki na b’ari ta nufi 6angaran su dan d’auko sak’on Aisar.

A wajan taron d’alibai(assembly), d’alibai da malamai babu wanda be hallara wajan ba, filin ya cika mak’il. Bayan sun yi abin da su ka sabayi kullum, wato na daga al’adar makarantar ne aka bawa Aisar filin. Gannin shi gaban su d’alibai su ka yi tsit, ita kuwa Marry zawo ne kad’ai be zubo mata ba, musammam ganin Iya Dije tsaye kusa da Aisar hannun ta ruke da almakashi. Kamar saukar aradu haka ta ji sunan ta bakin Aisar, bayan ya kira Bintu. Nan da nan d’alibai su ka shiga bud’a mata hanya, da kyar ta ke iya d’aga k’afa ta na takawa saboda tsabagen nauyin da k’afar ta yi mata, har ta kai ga Aisar da tun fitowar ta ya ke mata kallan hadarin kaji.

Jin umarnin da Aisar ya bata na da ta juya ta tsugunna bisa gwiwowin ta gaban d’alibai ya sa ta matsawa kusa da Aisar ta na magana a hankali dan kar a ji abun da za ta ce tace ‘’dan Allah Monsieur (malam) ka taimaka kada su raina ni’’ wani irin tsawa ya daka mata ya na mai fad’in ‘’matsa min daga nan in ba haka ba ina kishe ki a nanniya!(in ba haka ba ina dukan ki a nan)’’ da saurin ta ta ja baya, ba ta san sanda ta zube k’asa ba jiki na 6ari. Ba tare da wani dogon bayani ba, haka ma d’alibai ba sa buk’ata dan kuwa gaban su aka yi komai dan haka Ciseaux din hannun Iya Dije ya kar6a ya na mai mik’awa Bintu ya ce ‘’kyarbi ki mata abin da ta mi ki jiya!’’

Hannun Bintu na rawa amma ta kasa d’aga su ta kar6a, cikin magiya ba tare da ta iya furta wani abu ba ta ke kallan Aisar ta na mai girgiza masa kai. Ga mamakin kowa sai jin Aisar cikin rarrashi ya ce da Bintu ‘’kar6ar wanga Ciseaux tare da yiwa wanga azzalumar aski shi ne hukunci mahi(mafi) sauki a gare ta, idan ba haka ba barin wanga École nan har abada ba tare da ta gama jarabawar ta ba ya kamata, za6in na ki ne’’ jin haka tuni waje ya kaure da hayaniya d’alibai, masu tausayin Mary da masu Allah shi k’ara wanda su suka fi yawa, in da yan aji shida kuwa idan ran su yayi dubu ya 6aci, dama duk ajin Mary aka fi tsoro, ita ce mai kankaro mu su girman yau ga ta tsugunne gaban kowa kuma a wulk’ance, tsabagen d’ibar albarka ace yar aji uku ce za ta mata aski! Gaskiya sun zube ba nauyi. Sai ga hawaye sha6e sha6e a fuskar Mary.
Tuni zufa ya fara kyetowa wa Bintu, musammam da ta kai kallan ta ga Malam Hashim ya gyad’a mata kai dan kuwa dai ba kukan sa ba uwar kishiya ta mutu. Wata malama ce wacce dama ta dad’e da tsanar Mary ta k’araso kusa da su ta na mai fad’in ‘’ Monsieur ba ka san halin wanga d’ya ba ne (wannan yarinyar ba ne), in aka biya ta za mu shekara nanniya ba tare da an samu abun da ake so ba, bari kawai ni na taimaka mata da zab’in’’ ta na magana ne in da ta ke aikawa Marry da sako murmushin yayinda ta sa hannu ta cizge kallabin Mary, Mary ta yi saurin d’aura hannayen ta bisa kan ta domin 6oye cinyayyen gashin ta, ai ganin gashin sai ga d’alibai na darawa.
Chapter 10 · 0% Book details