← Book details Banbancin Kabila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 37

Sashe 7

Banbancin Kabila Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Da kyar Abdallah yake cin abinci, saboda tunani ya mai yawa. Of course shi ya san yana son aure, amma da wanda za'ayi shi ne matsalar sa. Ina zai fara. Kuma ko su Umma basu fada ba, shi bazai iya auren cousins din sa ba. Hamma Sudais din daya yi, yaga zai iya ne, kuma ma ai yayi hitting din jackpot, saboda matar shi akwai hankali. Ko adda Wasilan da take cewa ya zaba daga cikin su, ta manta da abubuwan da duka fada akan ta ne, ita da suke cewa zata auri mijin ta ne saboda kudin sa. Amma data yi aure, ta fara fita, tana daukan wanka, suka soya hali, ko wannan su ta zama yar dakin ta, iyayen su ma suka zama abokiyar ta. Ita kuma Adda Bilkisu, tana da kudin kan ta, kar ma ayi maganan na mijin ta, yasa suke ribibi akanta, ita da ma ba'a nan take zama ba, tunda Allah ya buda ma mijin ta, ya samu aiki a dubai, suka fara son ta, harda yayan ta. Basu ki yayan suce masu suzo su taka kan su ba, saboda tsabaragen son abun duniya. Ita kuma Adda Fadila, mijin ta akwai rufin asiri, ba laifi. Dan itama ba zaka ganta ka raina ta ba. Amma abun mamaki, sun raina iyayen su, amma suna son yayan su saboda abun duniya. In shima ya auri daya daga cikin su, shi ma zai zama dan so. But to hell, bazai bi abun da kawu Dajjo ke so ba. In sauran nayi, shi bazai yi ba. Shi zai bi umarnin iyayen sa ne.
"Abdallah! Abdallah!! Abdallah!!! Sanda Abba ya kira sunan sa sau uku, kafun ya amsa.
"Na'am Abba na".
"Naga baka cin abincin ka ne"? Abba ya tambaye shi.
"Bakomai Abba, ai ina ci".
"A'a, Abdallah bamu saba ganin ka haka ba, kai da you are always there to make us laugh". Umma ta fada.
"Toh ai shi ne". Abba ya fada.
"Bakomai. Bana ma jin yunwa, sai da safen ku". Ya tashi zai tafi dakin sa, Abba yace ya dawo.
"Gani Abba na".
"Zauna".
Ya zauna.
"Nasan abun dake damun ka, kar ka damu da abun da tsohon nan ya fada, na shi kawai yake fada. Ni yanzu zan bari ne ya maka auran dole ne?
Kuma in aure ne, lokacin ka ne baiyi ba auta, in lokaci yayi, ba mai iya stooping din shi. Saboda haka, ka saki jiki ka ci abinci".
"Ai kuwa. Ka daina damuwa da bad energy. In yaga sauran na dancing to his tones, toh ai ya kamata ya san mu kam bamu cikin su. Kuma ka auri koma waye, but make sure she will be a good wife and mother to your kids". Umma ta fada.
"Am in support of what your Umma said. Ba dole bane ka auri bafulatana ba, ko bahushiya ka samu kuma ta zauna maka, ko shi bazai daura auren ba, ni zan daura agidan nan. Nine uban ka ba shi ba". Daga yanda yake magana kasan ran Abba ya baci sosai.
"In Sha Allahu, nagode sosai Abba na da Umma ta, Allah yasa ku dade mana, Allah ya saka maku da aljannah, thanks for the support".
"Bakomai, ai responsibility din mu ne as iyayen ka ko Hajaju"? Abba ya tambayi Umma.
"Kwarai kuwa".
"Barci nake ji, gobe ina da morning duty". Abdallah ya fada yana hamma.
"Toh, kuma kar adawo gobe ayi mana complain, dan naga yau da wuri za'a yi barci". Umma ya fada.
"Toh ai ina huta gajiyan yau ne, gobe ma ai zan yi nashi gajiyan ko Abba na". Abdallah ya tambaye shi".
"Haka ne auta na., ko wani rana nada gajiyar sa".
"Wannan kuma ku kukasani" .
"Manta da ita Abba na, kishi take" Abdallah ya fada. Yana magana, Umma ta dau pillow, ta jefa masa, amma yayi sauri ya bar wajan.

Da yaje office, yayi attending to patients, lokacin komawa gida yayi, ya dauki briefcase din sa, ya cire coat din sa, ya rike a hannu. Yana kan tafiya, wani ya kira sunan sa "Dr Abdallah!".
Yana jin sunan sa, ya juya, yana juyawa, yaga abokin shi ne Dr Farouk.
"Bana ce maka akwai magana ba"? Farouk ya tambaye shi.
"Am sorry, na manta ne. Kasan stress din patients dinnan".
"Gaskiya attending to patients ba karamin aiki ba ne". Farouk ya fada.
"Wallahi. So what up"? Abdallah ya tambaye shi.
"Muje mu zauna akan bench dinan dake karkashin bishi yan nan".
Suka je suka zauna, Farouk ya fara magana " Guy kasan ansa aure na da Nabila bayan sungama wanan semestern, amma yanzu sun chanza, wai inba damuwa, ayi shi nan da two weeks, twoo weeks fa". Ya fada yana nuna yatsun sa biyu.
"Congrats man, Allah ya sanya alheri". Abdallah ya fada.
"Am serious fa, kuma kasan worst part din, su Abba sun yarda, wai hakan ya fi". Farouq ya fada.
"Toh me ke ciki, ayi abun da za'ayi kawai ka huta. Yours is even good, mufa yanzu muka fara hunting".
"Toh kai aganin ka hakan ya fi kenan"? Farouk ya tambaya.
"Ae, wallahi, na maka murna fa sosai. Ka ce dai mu fara shirin zuwa kano, ko muma zamu samo wata acan". Abdallah ya fada.
"Toh mashaAllah, tunda abun ya zauna cif, nima nayi relaxing. Amma da'a I was so worried".
"Kar ka damu, your brother in islam is here". Abdallah ya fada.
"Yeah thanks for za support. Sai yanzu ma maganan ka ke flashing. So ba ma raka ni zakayi ba, kaima zaka je neman mata ne"?
"Ae mana, ai yanzu na fara wife hunting, kuma I want it soon, bana son ana raina mu iyaye". Abdallah ya fada.
"Ban gane ba, wake son raina Su Abba"? Farouq ya tambaya.
Nan ya fada mai komai, sai Farouq ya ce "aiko, ko ni am in support. Allah yasa ka samu. Dama ka samu bahaushiya, muga expression din wanan kawun na ku".
"Amin aboki na, muga iya gudun ruwan sa, muga ko zai kashe ni ne, ko kuma me. Shi din daya ke magana, ai second wife din sa bajara ce. Amma ya bi ya takura mana, wai sai bafulatana dole". Abdallah ya fada.
"Kyale shi, dan yaga shi ne babba ai, shi yasa yake mulki akan ku yanda yake so. Aboki na, Allah ya baka bahaushiya, muga karke Kawu". Farouk ya fada.
"Amin ya rab aboki na. Shi yasa neke ji da kai".

```Thanks for reading, sharhi is bea, kaman yanda kuka sani.
```

~Zeexee ce~ 🖊️🖊️🖊️
[8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹
*BANBANCIN KABILA*
_(Short story)_
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹

*TAMBARI WRTER'S ASSOCIATION*

*_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_*

*T.W.A*

*WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_

MARUBUCIYAR

*-RAYUWAR HUSNA*

*-MAHAKURCI MAWADACI (2020)*

```Dedicating this page to my Kawallie (Hansey)🤭🤭🤭🤭 and my kanwas(boddi'am). I love you guys soooo much, long live the three musketeers💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼 .```

9️⃣&🔟

_Bismillah_
Chapter 7 · 0% Book details