← Book details Banbancin Kabila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 37

Sashe 32

Banbancin Kabila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daya gama komai, sai ya koma parlor, ya samu kowannan su a parlor, suna hira. Ya kira baban cikin su, Jamila (yarinyar mijin Adda Wasila), ya mika mata leda cike da su chocolate, sweets, chewing gum, da dai sauran su, ya ce ta raba masu.
Ya kalli umma a shagwabe ya ce "umman auta, ina jin yunwa fa".
Adda Fadila na jin haka, ta ce "ai ba sai ka fada ma umma ba, ko ni sai ka fada min, bari in kawo maka. Anan zaka ci ko a dinning?" Ta tambaye shi.
"Anan zan ci." Ya fada a shagwabe.
Yana fadan haka, ta tashi, ta wuce kitchen, ta je kawo mai abinci.
"Kai auta! A lan an kwaso gajiya ne ko?" Abba ya fada yaba shafa bayan sa.
"Sosai abba na, na gaji." Abdallah ya amsa.
"Sannu Uncle auta, ai kana kokari sosai." Aunty Aisha matar hamma Sudais ta fada.
"Ni kam ku bar shagwaba shi, wai ku baku san ya isa ace yana da yara ko yaro ba ne da zaku dinga wani shagwaba shi kaman baby." Adda Wasila ta fada.
"Ai shi ne, ji yanda kuke yi dashi." Umma ta fada, sai ta kalli Abdallah, ta ce "kai kuma ka tsaya a wajan a dinga maida ka yaro."
Tana gama fadan gakan, sai ga Adda Fadila niki niki da Abincin Abdallah a kan tray, sai ta tura stool, tasa a gaban shi, kafun ta ajiye abinci, ta ce "A ci lafiya auta."
Suna hada ido da Umma, taga irin hallon da take mata, sai ta kau da kai.
Umma tace "ku kuka sani, in yaso ku maida shi dan shekara biyar."
"A'a Hajiya ya ishe ki haka. Yaro ya kwaso gajiya, instead ki lallabe shi, kina kara mai gajiya akan gajiya. Ya samu masu mai kuma kina complain. Kar ki damu, inya yi aure, ya rage ni dake, zaki san value din auta. Ko auta." Abba ya fada yana kallon shi.
"Sosai ma, idan na auri Ola...." Sai yayi shuru, ya ma manta, bai san lokacin da sunan ya fito daga bakin sa ba.
"Ka auri wa?" Adda Wasila ta tambaya.
"Babu, ina auri all my wives nake son fada." Abdallah ya fada yana murmushin dole.
"All your wives kuma?
Ashe mata da yawa zaka aura a rana daya." Umma ta fada.
"Kai Umma, ai uncle auta ba haka yake ba, kawai dai wasa yake. Kuma ai yana da ikon auran matan hudu." Aunty Aisha ta fada.
"Toh ai shi ne, in yaso ya aure su a rana daya, but the fact still remains, zaki yi missing din auta." Adda Fadila ta fada tana murmushi.

Haka suka ita hira, Umma da adda Wasila na zolayan Abdallah, kafun shima hamma Sudais yazo, teams din suka cika 3-4, wannan team din na zolayan Abdallah, wayannan kuma na bada amsa.

Daman idan 6:pm yayi, ko wannan su ke komawa gida. So by 5, Abdallah ya ma hamma Sudais da adda Fadi text, yace su hadu a balcony, shi zai yi kaman yayi fushi, ya fito, su kuma su biyo shi.

Haka ko aka yi, adda Wasila na dukan shi a baya da wasa, ya hada rai, ya tashi ya bar wajan, suma suka biyo shi a baya. Da suka fita, suka yi dariya kasa kasa, hamma Sudais yace "toh me kake son fada mana ne, ka fada yanzu, kafun su ga mun dade, a fara suspecting din wani abu."
"First of all, ina son in maku godiya for like her, na gode maku sosai, Allah ya saka maku da jannah."
"Amin." Su biyu suka amsa.
"Secondly, akan yandan zan fada masu abba ne, nace ko zaku zo ne gobe ko jibi, ku taya ni mu fada masu please."
"Any day is okay with me, but zanyi preferring din Saturday more." Adda Fadi ta fada.
"Toh muzo Saturday. Allah yasa su yarda, Allah ya sa ka auri Olamiden ka, they will be pleased and happy to accept your relationship In Sha Allah." Hamma Sudais ya fada.
"Amin suka amsa tare."
Sai suka koma ciki, aka ci gaba da hiran, da su.

6:pm nayi, alokacin sun taya Umma girka dinner, kuma suma sun ci, kafun ko wannan su ya ja motar sa ya bar gidan, amma banda adda Fadi, saboda ita bata dashi, so sanda ta jira mijin ta, ya zo ya dauke su, ita da yaran ta, kafun suma suka bar gidan.

A rannan dai, Abdallah ya kwana ya na tunanin yanda gobe zai kasance in Allah ya kai mu da rai da lafiya, Allah yasa su yarda. Daya fada ma Mide ma lokacin da suke waya, ta nuna mai damuwa, yana ta kwantar ma da hankali, alhalin ko shi ma hankalin sa bai kwanta ba.

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Da Abdallah ya kashe wayar, ta tashi da sauri, ta shiga toilet, ta yo alwala, ta fara nafls, saboda hankalin ta yaki kwatawa kwata kwata, sai taji kaman this phone call was there last goodbye, amma daya ita kwantar mata da hankali lokacin da suke waya, she felt a little bit alright, but still ba wai hankalin ta ya kwanta bane.

Ta ita yin nafil, tana kuka, ya ilahi, she true loves Abdallah, but what will she do idan iyayen sa suka ki relationship din su, ina zata sa kan ta. Haka dai ta ita sallah tana kuka, tun kuka baya fita, har ya fara fita.
Da Nafisa taji kaman tana kuka, sai ta bari sanda ta yi tayya, tayi sallama, kafun taje gaban ta, tace "what is it again habibty, wai me yasa almost every time idan kuka gama waya sai kin yi kuka, kuma idan akan iyayen sa ne, kar ki damu everything will be alright.
Wallahi if not because you are already in love with him, dana yi advising din ki kuyi breakup haba what is it self, kullum ke kenan cikin tashin hankali, baki da natsuwa, kullum sai kuka. Ni kam idan relationship din nan ba zai sa ki dinga samun kwanciyan hankali ba, toh ki bari gaskiya."
Da jajjayen idon ta ta kalli Nafisa ta ce "abun da zaki ce kenan?" Ta tambayi Nafisa hawaye na zuba a idon ta.
"Ba haka bane, amma ni fa kwata kwata bana son inga hawayen ki." Nafisa ta fada tana share mata hawaye.
Cikin jin haushi ta ce "ki kyale ni. Say the truth, tunda muke tare, na taba irin halin?
"A'a, ni fa habibty, bance ki daina son shi ba, I said da baki son shi yanda kike son shi ba, dana baki advice kuyi breakup." Nafisa ta fada.
"Shi yasa nace ki kyale ni, if you can't give me advice, just let me be. Ni kadai na san abun da nake ji, ni nasan irin son da nake masa, so if you can't be with me in this time of worry, then ki kyale ni." Olamide ta fada, sai ta tashi ta je ta kwanta akan katifan ta. Takaici duk ya bi ya dame ta. Nafisan data kamata ta kwantar mata da hankali, tana mata irin wannan maganganun.

Ita kuma Nafisa, tama rasa abun fada, saboda Olamide bata fahimce ta ba.

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Da Abdallah ya tashi, yayi routine din sa, yau din sai yaji duka jikin sa a mace, yana jin wani iri, Allah yasa yayi nasara, Allah yasa su Umma su yarda.

Banyan zuhur suka ce zasu zo (hamma Sudais da adda Fadila), so ana idar da sallah, da suka dawo daga masjid da abba ya ji hankalin sa ya kara tashi, kawai ya yanke hunkuncin instead ya dinga tada hankalin sa, why not ya ita addu'a saboda du'a is the sword of every muslim, and with Allah everything will be alright.

Da su hamma suka zo, sun samu umma da abba da Abdallah zaune a parlor.
Da suka zauna, adda Fadila ta je ta kawo masu drinks ita da hamma, suka sha. Sanda suka bari sun yi nisa sosai da hira, kafun hamma Sudais yace " Abba, Umma, kuma kun san wannan zuwan mu kam da dalili, saboda jiya muka zo, kuma ace gamu kuma yau."
"Tabbas, ina son ma in tambaye ku ne." Abba ya fada.
" Abdallah ne yake da magana da ku, amma our presence is needed." Hamma ya kara fada.
"Toh kai Abdallah, me kake son ka fada mana ne da har sai yayyin ka sun zo?" Umma ta fada
"Daman, daman akwai. Abdallah ya kasa ci gaba da magana.
"Kayi magana mana?" Umma ta fada.
"Na samu wace .........."

```Thanks for reading, please kuyi maneji.```

Comment
Like &
Share.

~Zeexee ce~ 🖊️🖊️🖊️
[8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹
*BANBANCIN KABILA*
_(Short story)_
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹

*TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION*

*_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_*

*T.W.A*

*WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_

MARUBUCIYAR

*-RAYUWAR HUSNA*

*-MAHAKURCI MAWADACI* _(2020)_

3️⃣9️⃣&4️⃣0️⃣

_Bismillah_

*BAYAN WATA DAYA*

"Baza mu yarda ba and that is final."
"Abba dan Allah, am begging you guys please."
"Wai kai wani baza mu yardan ne baka gane ba?"
"Dan Allah umma kar ku mun haka, one month kenan fa ina rokon ku, dan Allah, kuyi ma Allah da manzon sa ku yarda, wallahi Olamide is not like that, kuma yanda kuke cewa yarbawa basu da dabi'a haka ma wasu fulanin." Abdallah ya fada da hawaye a idon sa.
"Toh masani fada mana, ka san ni da Abban ku bamu san komai ba." Umma ta fada.
"Wallahi umma ba haka bane, am just trying to make you guys understand that's why. Dan Allah ku yafe mun indai magana na ya bata maku rai, amma dan Allah ku yarda da ni, wallahi bazan yi disappointing din ku ba." Abdallah ya fada.
"Ka tashi ka fita kafun rai na ya kara baci inyi abun da dukan mu zamu yi regretting." Abba ya fada rai abace.

Jiki a sanye Abdallah ya mike daga inda ya tsuguna, ya fita a dakin, hawaye na zuba shar shar a idon sa.
Chapter 32 · 0% Book details