← Book details Banbancin Kabila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 37

Sashe 17

Banbancin Kabila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shima Abdallah, suna gama duk abun da zasu yi, ya wuce gida, tunda dare yayi. Yaso yaje gidan Adda Fadi, dan suyi magana, amma lokaci ya wuce, ga shi ma agajiye yake.
Daya isa gida, suka gaisa da su Umna da Abba, Umma tace ga abinci nan a dinner, ya ce shi ya koshi. Wata zuciyar ta ba shi wai ya fada masu shi ya samu wace yake so, wani kuma yace a'a kar ya fada, wannan maganan na neman natsuwa ne, dole sai kowannan su na cikin farin ciki, kafun ya iya tunkaran su da wannan maganan, kuma ya fara fada ma Adda Fadi, tunda she is more closer to him, and she understands him better.
"Tunanin me kake ne auta na"? Abba ya tamyaye shi
"Bakomai abba na, na gaji ne kawai, ka san wannan harkan akwai gajiya". Ya fada yana mika.
"Kai kam akwai randa ba zaka dawo kayi complain ba kuwa, gaskiya banga rannan ba, maybe nan gaba". Umma ta fada tana jijjiga kai.
"Subhanallah! Abdallah ya fada yana dafa kai. "Wai ni ni kam Umma me yasa baki so na ne?
Kullum sai kin yi complain, kar ki damu, na kusan barin maku gida, ko kya huta da da complain". Ya fada.
"Ai kuwa dana ji dadi sosai.
Amma in tambaye ka, har ka samu mata ne"? Umma ta tambaya, idon ta a kan sa.
"Kai Umma what do you mean, amma dai something like that, but it's not settled yet, when it is, In Sha Allahu zaku ji". Yana fadan haka, ya dau jakar sa, ya bar parlorn da sauri, gudun kar Umma ta kira shi da marasa kunya.
Yana barin wajan, Umma ta ce "ni kam me yaron nan ke nufi ne"? Ta fada tana kallon Abba.
"Oho, nima ban sani masa ba. Amma baya ce zamu ji ba in komai yayi settling, so have sabr my dear wife".
"Okay I will, amma idan suspicion dina ya tabbata, I will be soo happy, saboda at least wannan tsohon ba zai kara maka maganan banza ba". Ta fada tana huci.
"Bari kawai, ni zan ma fiki jin dadi. Kin san jiya ma dana je gaishe shi, sanda ya tada maganan, kinga irin kallon rainin daya ke mun ne, worst part din shi ne, dana je, na samu Wasila da mijin ta da yayan ta, wai sun je mai gaisuwan jumma'a. Wasilan da rabon ta da gida, almost one month, amma dana ce me tazo yi, Baffa yace wai sun zo gaisuwan jumma'a kaman yanda suka saba zuwa. Toh shiyasa kika ga jiyan nan sun biyo ni, saboda kunya". Abba na fadan hakan, ya sake numfashi.
"Nima gaskiya na rasa wace iri ce Wasila. Tunda tayi aure, ta guje mu, kiran ma da Sudais, da Bilkisu da Fadila ke mun kullum safe, ita kam sai taga dama take kira na. Ta bi ta dauki mutumin nan tamkar mahaifin ta, mu kuma ta dauke mu tamkar iyayen goyon ta. Kuma bata son taga laifin sa sam, shiyasa bana ma wani shiga shirjin ta, saboda duk abun da akayi a gaban ta, sai tsohon nan yaji. Shi yasa ma mijin ta yafi ganin mahinmancin tsohon nan, akan mu". Umma ta fada rai a bace.
"Ya muka iya, tagan mu talakawa, amma ta sani, acikin wannan gidan ta girma, ci da shan ta, da sutura, duk mu muke mata, bata taba ganin tsohon nan ya bamu kobo ba. Kuma ke kika dau cikin ta tsahon wata tara, kuma kika raine ta. Amma tun da rayuwar da tayi choosing kenan, Allah ya bada sa'a. Ai ni ban ma san suna baya na ba, dan dana ga yanda aka ita share ni, nima na tashi, na fita. Ban kai su kudi bane, amma ina da mutunci, bazan bari su raina ni ba. Ina fita na shiga mota, Idi yana ganin expression dina, ya san ba lafiya, shima ya ja mota, muka bar gidan. Ashe dana fita, sun biyo ni abaya, shiyasa kika ga mun shigo tare ai". Abba ya fada.
"Hmmm, wallahi da bani na haife ta ba, dana cire hannu a cikin alamarin ta, amma yana iya, sai dai in ci gaba da mata addu'a. Ada ko Wasila ta fi su hankali duka, amma yanzu kam sai hamdallah". Umma ta fada.
"Kaman yanda kika fada, mu ci gaba da mata addu'a kawai".
"Ya muka iya, ai dole".

Da Abdallah ya bar parlorn, dakin sa ya tafi, nan ya watsa ruwa, ya fito ya sa PJ din sa, sannan ya kwanta kan gado, ya jawo wayar dake saman bedside drawer, yayi dailing din numbern Olamide, amma ya ita ringing, ba'a daga ba, ya kara kira, still ba'a daga ba. Sanda ya kira almost 7times still the same, sai ya mata sms, ya saurari reply almost 20mins, still ba reply, sai yayi concluding maybe tayi barci ne, gobe zata gani, Allah Yasa ta kira shi. Ya ajiye wayar, ya shige blanket, ya kwanta kan hannun daman shi, yayi azkar, ya shafa, aiko nanda nan barci ya dauke shi.

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Cikin dare, alarm din Olamide ya fara kara, a tsorace, ta tashi, dan tama manta ta sa alarm, soboda irin gajiyan da suka yi. Tana tashi, taga alarm ne, tayi snoozing din shi, after 5mins, ya kara ringing, ta gaji sosai, amma it's time for tahajjud, haka ta tashi, jiki ba kwari, ta dauki toothbrush din ta da toothpaste. Daman indai Olamide zata je hutu, ko a ina ne, sai taje da brush, toothpaste, da soson wanka, da kuma sabulu, shi yasa ma bata ma wani damu ta tambayi Nabila komai ba.
Tana daukan toothbrush din ta da toothpaste, ta shiga toilet din dake cikin guestroom, tayi business din ta, sannan tayi brush, kafun ta yi alwala, ta fito daga toilet. Data fita, taje ta side din da Nafisa ke kwance shame shame kanan wata gawa, ta fara tada ta, da kyar ta samu Nafisa ta tashi, kafun ta rike hannun ta, tayi leading din ta zuwa toilet, ta tura ta, sannan ta rufe kofar. Luckily akwai sallaya adakin, ta shinfida masu, ita ta fara sallah.
Acikin toilet kuwa, Nafisa nata faman zuba ruwa a fuskar ta, ko idanuwan ta zasu budu garau, amma ina, sai kara rufewa suke. Da kyar dai ta samu tayi alwala, ta fita a toilet, ta saka hijabi, itama ta fara sallah. Suna idarwa, ko wacen su ta dauki wayar ta ta bude Islam pro app, suka karanta alqur'ani, sannan su kayi addu'a safe da maraici. Suna gamawa, da kyar ma suka iya nannade sallayan da suka yi sallah akai. Sharp sharp suka hau kan gado, suka koma barci.

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Cikin dare Abdallah ya tashi, yayi sallah, lokacin fajr yayi, ya samu Abba a parlor, suka hada hanya, suka tafi masjid tare.
Da suka dawo, yayi tillawa, yayi addu'an safe da maraici, sai ya kwanta, dan haryanzu gajiyan bai gama barin jikin shi ba.
Yana cikin barci by 9:00am Umma ta zo ta kwankwasa kofar sa, yana ji ana kwankwasa, amma yayi zaton ko yana mafarki ne, sanda yaji tas abaya, ya tashi arazane.
"Kai Umma, wai me yasa kika tsane ni ne haka?
Haba Umma na, wani laifi na maki ne". Ya fada yana shafa bayan sa da ta dake shi.
"Toh ai kai din ne baka ji, kasan abun, amma kullum sai na tuna maka". Ta fada tana jan kunne sa.
"Oush Umma, laifin me nayi kuma yau"? Ya fada yana kokarin cire hannun ta.
"Laifin rashin zuwa cin breakfast da wuri". Tana fadan haka, ta sake mai kunne, ta kara cewa "ka tashi kazo ka ci abinci, ka san fa jiya baka ci dinner ba, and that is not good for your health at all". Umma na gama magana, ta bar dakin.
Tana fita, shi ma ya tashi, ya shiga toilet, ya kuskure baki, ya wanke fuskan sa da ruwa, sannan ya goge da towel, kafun ya fita, ya wuce dinning, ya samu shi suke jira, ya samu wuri ya zauna, nan suka ci abinci tare.
Yana clearing din kwanonin da suka ci abinci da su, wayar sa ya fara ringing, sai ya ajiye kwanonin hannun sa da sauri, dan a tunanin shi, maybe Olamide ke kiran shi. Ya na ganin sunan Asim, yaja tsakin takaici, sai ya yi picking.
"Assalamu Akaikum". Ya fada.
"Waalaikumus salaam. Nace kar dai ka manta yau zamu je gidan Farouq". Asim ya fada.
"A'a ban manta ba, ai baku fada time ba".
"Toh su Ahmad sun ce wai by 10, sai muyi kaman 30mins or less". Asim ya fada.
"Toh hakan ma yayi, sai ku biyo mun, kun san nike kusa da hanyar gidan".
"Shikenan, sai mun zo. DanAllah ka shirya da wuri, banda nawa". Asim na fadan haka, ya kashe wayar.
Abdallah ko yayi murmushi, ya jijjiga kai, sannan ya ci gaba da aiki, yana tunanin dalilin da ya sa Olamin sa bata kira ba, Allah yasa dai lafiya. Kuma yau In Sha Allah, in suka bar gidan ango, gidan Adda Fadi zai fara zuwa, suyi magana, kafun ya koma ya dauke ta, su koma gidan Adda Fadi. Amma still Allah yasa Qalbin Abdallah na lafiya.

Duk abun da yake, hankalin sa bai kwanta ba, yanzu suna hanya ne, da shi da sauran abokanan sa zasu gidan Ango. Tunanin qalbin Abdallah yake, Allah yasa dai lafiya.
Chapter 17 · 0% Book details