← Book details Banbancin Kabila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 37

Sashe 30

Banbancin Kabila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da suka wuce, shima ya koma daki, ya hau kan gado, ya jingina da pillow, sai tunanin Olamide ya fado mai. Me zai ce mata yanzu in suna waya?
Inma ya fada mata, hanya bai zai yi loosing din ta ba?

Haka ya ita tunani, har lokacin sallah yayi, yayi sallah acikin dakin shi.

Daya idar, yana cikin addu'a, wayar sa ya fara ringing. Ya duba wanda ke kira, sai ya ga sunan Olamide (my qalbi) boldly akan screen, nan ya fara jin heart din sa na beating, yama rasa mai zai yi, ya daga ne ko ya bari.

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Sanda Nafisa ta bari bayan 30mins, sai taje kusa da Olamide akan katifan ta, Olamide na ganin ta, ta juya fuska. Yanzu kam tama daina tunanin yanda iyayen Abdallah zasu yi reacting, haushin Nafisa take kawai, saboda ita baza ta iya fada mata haka ba, ko suggesting din shi baza ta yi ba.
Da Nafisa taga ta juya kai, sai ta juyar mata da kai tana kallon ta, tace "Allah sarki habibty, wallahi I care for you, I care about everything about you, bana son ganin hawayen ki. Kuma na fadi hakan ne saboda I really care about you. Kuma indai kin saurare ni da kyau, toh bance kuyi breakup ba, cewa nayi da baki son shi yanda kike son shi haka, dana ce maki kuyi breakup."
"Toh naji ki, sai da safe." Olamide ta fada, ta juyar da fuskan ta zuwa dayan gefen.
"Haba habibtyn Fisa, I really care about you, shi yasa kika ga na fada haka. Wallahi na tsani inga kina cikin damuwa, balle azo ga kuka, amma ina mai baki hakuri, kiyi hakuri da wannan stupid friend din naki, bazan kara ba." Nafisa fada.
"Toh naji." Olamide ta fada.
"Baki ce kin hakura ba." Nafisa ta fada.
"Ban hakura ba." Olamide ta fada.
"Haba habibty na, wallahi I care about you, kin ga idan kika ci gaba da haka, education din ki ma zai yi slacking. Bana son situation din da zaki dinga slacking a komai." Nafisa ta fada.
"Toh naji na hakura, shikenan?" Olamide ta fada ta juya kai tana kallon ta.
"A'a, ina son ki hakuran gaske, ba irin wannan ba." Nafisa ta fada a shgwabe.
"Wani irin hakuri ne yafi wannan, har ina amsa maki, toh na hakura, amma I don't want to talk to you." Olamide ta fada, ta tashi ta zauna.
"Haba habibty, so kike inyi ciwo, ya zaki ce kin hakura, amma baki son yin magana da ni, ki tuna fa I love you more than you can imagine, your happiness is my, and your sadness worries me too." Nafisa ta fada kaman zata yi kuka.
"I know you love me, and I also love you too, you mean a lot to me, but you should have consoled me, bawai ki dinga bani irin advice din nan ba at that moment. Wallahi alokacin nan, comfort nake so, ina bukatan ki kwantar mun da hankali ne. Ko kin san idan iyayen sa basu yarda ba, hakan na iya zama sanadiyan rabuwan mu, so I need comfort, not that type of advice. You can advice me that any day, banzan yi fushi ba, but I was hurt when you deed it at that time." Alokacin Olamide tana magana tana kuka.
"Ban san abun daya sa nake da saurin kuka ba, amma this is me." Olamide ta kara fada.
Nafisa bata san lokacin da ta yi hugging din ta ba, ta ce "am very sorry habibty, bazan kara ba, I just said it, ban yi tunani ba, danAllah kiyi hakuri." Nafisa ta fada.
"Nayi, amma Fisa na dauke ki as sister ta, ko kin mun laifi, bana iya fushi dake." Olamide ta fada.
"Am very sorry, banzan kara ba." Nafisa ta fada.

Da suka gama koke koken su, su dan yi hira, Nafisa ta ita kwantar mata hankali, su kayi barci.

Da suka tashi da safe, suka yi dutyn su, suna ta hira, ranan ya kasance Saturday, gashi basu da lectures, so suna ta huta duka gajiyan da suka yi tun monday. Ana cikin haka, Abdallah ya kira ta, ya sanar mata da cewa bayan asr zasu fada masu Abba, tun lokacin mood din ta ya canza, amma tana ta kokarin danne shi, not to make anyone around her worried.

Around 3 data ji shuru, sai Nafisa ta bata advice wai ta kira shi, da tana ta contemplating. Sai bayan sallan asr ta yi concluding kawai ta kira shi, kawai ta kira shi.

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Sanda wayan ya kusan tsinkewa, ya daga.
Daya daga bai yi magana ba, sanda ta ita sallama, kafun ya yi clearing din muryar sa kafun ya amsa.
"Baka amsa mun ba tun dazu ina ta salama." Olamide ta fada.
"Kiyi hakuri, yanzu na tashi daga barci shi yasa." Abdallah ya fada.
Allah ya ga baya son yin karya, amma ya ya iya, ba zai iya fada mata abun daya faru ba.
"Toh yayi, shi ne ka bar ni da damuwa ko?" Ta tambaye shi.
"Kiyi hakuri, su adda could not make it, shi yasa muka chanza timing din, sai duk ran da they are free again." Abdallah ya fada.
"And you didn't bother telling me. Kasan yanda na damu kuwa?
Gashi instead ace muna progressing, sai baya mu ke zuwa. Gaskiya ni bazan iya irin relationship din nan ba, our parents need to know about us. But if you don't want that, we can call it a quit." Olamide ta fada, sannan ta kashe wayar.
She was soo frustrated, ta rasa abun da yasa Abdallah yake mata haka. Shi ya sata agaba, sanda ta sanar ma mummy, amma ya sanar ma iyayen sa ya zama matsala.

Shi kuma Abdallah, data kashe wayar, ya rasa yanda zai yi da rayuwar sa, the pressure is too much, ya rasa abun yi, ji yake kaman ma ace he is not Abdallah any more.

```Thanks for reading```

Comment
Like &
Share.

~Zeexee ce~ 🖊️🖊️🖊️
[8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹
*BANBANCIN KABILA*
_(Short story)_
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹

*TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION*

*_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_*

*T.W.A*

*WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_

MARUBUCIYAR

*-RAYUWAR HUSNA*

*-MAHAKURCI MAWADACI* _(2020)_

3️⃣7️⃣&3️⃣8️⃣

_Bismillah_

Da su umma suka shiga ciki, Umma tace "wai ni alhaji me ke damun yaran nan ne in aka zo zancen aure?"
"Ai kuma ba ni zaki tambaya ba Hajiya, su zaki tambaya. Ina ganin sakewan dana masu ne yayi yawa." Abba ya fada rai abace.
"Gaskiya kam, sai ko wannan su zai yi aure ake meeting akan mu kullum." Umma ta fada.
"Hmmm bama wannan ba. Kin san me Abdallah ya fada?" Abba ya tambayi umma.
"A'a alhaji." Umma ta amsa.
"Kin tuna ran da na dawo nace baffa Dajjo ya mun maganan auren shi, kuma muka ce mai koma waya ya auro, in dai ta mai?" Ya tambaye ta.
"Haqqun na tuna. Kar dai shiyasa ya nemo mana bayarbiya. Yarbawan da basu da tarbiyan?"
"Shi nake gani nima ai, saboda da na kusan fita a parlor, yake cewa ai mun ce ya auri koma waye, indai ta zauna mai." Abba ya fada yayi tsaki.
"Toh shine yaje ya samo bayarbiya, yarbawan da kowa ya san halin su?
Be ma nemi yar arewa ba, yar kudu ya nemo." Umma ta fada takaici na kama ta.
"Ai shi ne. Ni fa when we said that, I only thought about someone from arewa, me zamu yi da yar kudu?" Abba ya fada ya dafa kai.
"Ai shi ne na gani. Me ma ya kai tunanin sa zuwa nan?" Umma ta fada.
"Oho masa." Abba ya fada.
"Ni kam gaskiya bazan yarda ba, saboda gaskiya yanda mutum ke jin labarin yarbawa, they are not people we can live with." Umma ta fada.
"Gaskiya they are not people to live with." Abba ya fada yana kada kai.
"At all. Kuma kar mu yarda gaskiya alhaji, saboda ban zan yarda ace mu zama abun zagi a gari ba." Umma ta fada.
"Ai baza mu yarda ba, ya ma san inda dare ya ma sa." Abba ya Fada.
"Ai kuwa." Umma ta fada.

Haka su Abba da Umma suka ita maganganu.

Abdallah ya kara kiran Olamide, bata daga ba, ya kira ta yafi sau bakwai amma ta ki dauka, sai ya kira Nafisa. Olamide ta tambaye ta ko shi ne, ta ce ae, Olamide tace mata kar ta daga. Har sau uku ya kira ta, itama bata daga ba.
Although ta so dagawa, amma Olamide ta ki, tace kar ta daga, inba haka ba zasu yi fada. Ita kuma gudun kar kawar ta tayi fushi, ta ki dagawa, amma ta kuddura a ran ta, anjima zata kira shi.

Rashin dagawan da suka yi, ya tada ma sa da hankali sosai, yaji ba abun da ke mai dadi. He felt so heart broken, ya rasa inda zai sa kan sa. Olamiden da ta kamata ta kwantar masa da hankali, ita ma tana fushi da shi.

Aranan kam Abdallah ya rasa yanda zai yi da kan sa, dan su abba ma sun ki kula shi. Inma ya masu magana ba kula shi suke ba. Abun duniya duk yabi ya ishe shi, ji yake kaman ya je tsakiyan compound din gidan su, ya dinga ihu, ko zai dan ji relief.
Chapter 30 · 0% Book details