← Book details Banbancin Kabila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 37

Sashe 11

Banbancin Kabila Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sun dade a gidan su Nabila, dan sai bayan isha, Hajiya tace ma Yaya Faeeq ya mai da su. Nan ma sanda Nafisa ta ita raba fada. Shi Faeeq, baya gajiya da tsokanan ta, ita kuma bata gajiya da bashi amsa, so shi yasa suke prolonging din issue.
"Wallahi Olamide, in kika bani haushi, anan zan sauke ki. Kuma kin san baki son a bun da zai sa dare ya same ki a waje, zanga yanda zaki koma gida". Faeeq ya fada a fusace.
"Ka sauke ni mana, sai me?
Ai ba mutuwa zan yi ba. Inada kudi na da zai kaini har gida". Itama ta fada tana huci.
"Sai ya tsayar da mota, ya fita, ya je side din da take. Daman tana back sit ne, Nafisa kuma na passenger's sit. Kuma anyi hakan ne, saboda kar suyi fada, amma ina abun nasu a cikin jini yake.
Daya tsaya abakin kofar, ya bude, sai ya ce "ki fita".
Kaman jira take, ta yi hanging din jakarta , dan daman tasa jakar saman cinyar ta ne. Tana hanging din jakar, ta fito. Nafisa na ganin haka, ita ma ta fita. Sai ya ce "baki da case Nafy, ki koma ciki. Daman wannan yar rainin hankalin ne".
"Gaskiya bazan iya kallon habibty na haka ba, so duk hukunci daka dauka akan ta, kaman akai na ka dauka. Ka wuce kawai, mun gode, dan na san da kyar in habibty zata kara shiga motan nan". Nafisa ta fada.
"A'a ke ba ruwan ki, ki shiga, kuma ita din ma, nasan zata shigo ai, ba yau muka fara ba". Yaya Faeeq ya fada.
Faeeq da Nafisa annan suna settling matter, ita ko tana can tana neman adaidaita.
Tana samu, tayi ciniki da shi, sai ta ce "habibty kizo na saman mana adaidai ta, kizo mu wuce time na tafiya". Ai ko tana jin haka, ta taho, suka shiga keken, ya wuce dasu.

Shi kuma yaya Faeeq, takaici ya kama shi, bai yi zaton zata samu abun hawa ba, gashi shi yaso ko in zata wuce, ta bar mai Nafisa. Kowa na ganin kaman Olamide ya ke so, but in real sense Nafisa yake so. Me shi zaiyi da yar yarbawa, su da akace suna da masifa, ga fada. Ai gashi ma ajikin Olamide, yarinya sai shegen tsiwa. Allah ya tsare shi, yaje ya aure ta, duk randa yan'borin ta suka tashi, tasa shorts, suyi fada. Gwanda ma Nafisa.

Suna sauka a bakin gate, Olamide ta ciro kudi ta ba shi, sannan suka shiga ciki. Suna shiga, Allah yayi akwai wuta, sai suka kunna fanka, kowanan su ta cire hijabin ta, ta ninke, ta cire bag, suka yi hanging din shi, suka sa takalman su a mazaunin su. Sannan Olamide tayi plugging din ruwa acikin kettle.
Tunda suka shigo, ba wanda ta ce ma wata kala, kowannan su nata harkan gaban sa. Ita dai Nafisa, bata son ta fadi abun da zai bata ma Olamide rai ne, ita kuma madam, sai huci take, tana regretting din zuwan su gidan su Nabila. Ita bawai ta sake masa ne ba, amma ita gaskiya ba zata bari yana zagin ta tayi shuru ba, lokacin da suke 100l, ta na dan jin kunyar sa, bata maida mai magana. Amma yanzu kam she can't take it. Mutumin da ba akan ta zagin ya tsaya ba, ya zage ta, ya zagi yaran ta, kuma abun da bai sani ba is that she is very proud of her tribe, duk da dai bata san garin su ba, amma she is still proud. Kuma ai Allah ya halice mu, yanda Ya halici baki, haka ma fari, ya halice mu in different nations, state, colours, tribes e.t.c, why not mu dauki juna as one, we are all Allah's creation. Amma wasu kam baza su iya ba. Inba racism be, toh tribalism, kuma yana everywhere. In yana ma wasu, suna barin shi, toh ita baza ta bar shi ba. Tana cikin tunani, wayar ta ya fara ringing. Data duba, taga sunan daya fito kan screen, tayi murmushi, ta daga. "Assalamu alaikum Ummi".
"Waalaikumus salaam ya'a. Kun isa gida lafiya"? Hajiya Hajara ta tambaya.
"Lafiya kalau Ummi". Ta amsa.
"Toh Masha Allah. Ina Nafisa"? Hajiya Hajara ta tambaya.
"Gata". Olamide ta fada, ta mika ma Nafisa wayar. Suka gaisa da Nafisa, kafun ta sa masu albarka, suma suka mata godiya, sannan suka kashe wayar.
"Habibty danAllah kiyi hakuri ki daina fushi please".
"Ba fushi nake ba. Kawai dai Ina regretting ne. Da ban san Nabila ba, da bazan hadu da tribalist dinnan ba. I hate his character wallahi. He should even thank his stars, ya girme ni, inba haka ba, daya fi haka shan maganganu a waje na, dana masa tas wallahi" Olamide ta fada.
"Kiyi hakuri kawai, ki dubi relationship din mu da Nabila, ki yafe mai".
"Daman ai saboda Nabila nake ragan masa, inba haka ba, dana dinga bashi amsoshin da zai kasa sa kan sa a pillow". Olamide ta fada.
"Ko ni, bana jin dadin yanda yake maki". Nafisa ta fada.
Suna cikin magana, kettle din ruwan da Mide tayi plugging, ya masu signal. Da sauri Mide ta kashe, ta zuba cikin bokiti, ta kara cika shi da ruwa, ta yi plugging.
Ta dauki bokitin ruwan zafi, ta wuce toilet, tayi wanka, sannan ta fito. Tana fita, Nafisa ta shiga, itama.

```BAYAN SATI DAYA```

Su Olamide kawayan amarya, sai shiri suke, sun dau anko har sun kai dinki, sun raba invitation, sunata shiri, don next week Saturday kam In Sha Allahu Nabila zata zama amarya.
Kuma duk zuwan da suke gidan su Nabila, Olamide bata haduwa da Faeeq, hankalin ta ya kwanta sosai, ta sake sosai a gidan, duk Familyn su Nabila da suka zo, su Olamide sun shiga masu rai, especially Olamide. Wasu macewa suke wai karya take ba bayarbiya bace, wai bata da halin su, kuma bata kama da su. Amma ai kun san ta da baki, ta ce masu wato kowani yare nada kaman sa kenan, kuma ko wani yare na da halin sa, ai ita bata taba sani ba, abun data sani shi ne, Allah ya halince mu duka.
Hajiya Hajara ko sai nuna ta ma kowa take, wai yar ta ce, although ba ita ta haife ta ba, amma yar'ta ce, ita ce yayar Safina.

```WEEK DIN BIKI```

Kawayan amarya ansha lalle, itama amarya, ta sha gyare gyare, Hajiya Hajara da yan'uwan ta, sun gyara ta spiritually, physically, ta mentally, sai kyali ta ke, black skin din ta yayi kyau sosai, Nabila ta dawo kaman ba ita ba, tabi tayi kyau sosai.

Yau Friday, za'ayi kamu, yan matan amarya, sun sha makeup kala kala, da wanda nata yayi fitting din ta, da wanda nata baiyi fitting din ta ba. Nafisa ma ba'a barta a back ba, makeup artist da aka dauka, ta rangada mata makeup itama, tayi kyau sosai, inba kasan ta ba, baza ka gane ta ba. Olamide kuwa anyi anyi da ita a mata makeup, taki, wai su foundations, din da za'a sa mata, zai sa zafi ya kama ta, kuma ita baza ta iya juriyan safi ba. So powder, da wani nude colour lipstick ta sa. Itama tayi kyau daidai gwargwado. Sai shiri ake za'a kamu by 4:00pm.

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

A matsayin sa na aminin ango, tare suke zurga zurgan biki, suje nan suje can. Gidan da za'a sa amarya ma, sanda suka ga gidan was looking it best.
Abdallah ya kai makulli, lokacin da aka zo jere.
In suna tare da Farouk, ya ita tsokanan sa, sai kuma ya shiga land of dreams din sa, ace shi ne ma zai yi auran, daya ji dadi, sosai.

Ranan Friday da safe, suka tafi kano, da shi da ango, da sauran abokanan su. Suka sauka awani hotel, kafun lokaci yayi, su tafi venue din da za'ayi kamun.
Bayan asr, suma suka fara shiri, dakin ya dauka da kamshin turaren maza kala kala. Sunyi kyau sosai, abunka da fararen maza, amma still cikin su, ba'a rasa bakaken ba, suma sun sha kyau sosai.
Basu bar hotel din ba, sai 4 dot, suka kama hanya, suka je venue din event, nan suka samu, wasu kawayan sun zo, amarya da main girls din ta basu zo bako, amma within 5mins, suma suka iso. Suna isa, Nafisa ta fara fita daga cikin motan, tana wani kyali. Abdallah, ya kallie Farouk, ya ce "Guy baka fada mun amarya nada extraordinary beautiful friends haka ba. Just take a look at this one, although dai tayi makeup, kuma kasan I don't go for madeup girls". Yana cikin magan Olamide ta zura kafafun ta ahankali, ta fito. Ai anan bakin shi yayi full stop, yama kasa cewa komai, sanda Farouk yayi taping din shi sau uku, kafun ya ce " subhanallah, which of the favors of your lord would you deny".

```Thanks for reading, please kuyi maneji.
```

~Zeexee ce~ 🖊️🖊️🖊️
[8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹
*BANBANCIN KABILA*
_(Short story)_
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹

*TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION*

*_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_*

*T.W.A*

*WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_

MARUBUCIYAR

*-RAYUWAR HUSNA*

*-MAHAKURCI MAWADACI (2020)*

```Dedicating this page, to my Moza(Xulley sparks)🤭🤭🤭 and my abokiyar fada🤭🤭💃🏽💃🏽💃🏽. I love you guys overdose🤭🤭🤭🤭.```

1️⃣3️⃣&1️⃣4️⃣
Chapter 11 · 0% Book details