← Book details Banbancin Kabila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 37

Sashe 12

Banbancin Kabila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Which of the favors of your lord would you deny". Abdallah ya fada.
"Non ya akhi". Farouq ya fada.
"I can wait to see my Bila wallahi". Farouq ya kara magana.
"Ni kam I have seen my qalbi, amma ya rage yanda zata zama nawa, don kasan heart dita ce, dole na samu yanda zan daidaita ta". Abdallah ya fada yana rubbing din palms din sa.
"Gaskiya ne, daga ganin yarinya har ka fara maganganu"? Farouq ya tambaya.
"Dole na fara, saboda Allah's creation is sooo beautiful, full of beautiful features. Just take a look at her, batayi wani makeup ba kaman sauran, amma tafi su. Kaga daa bahaushiya nake nama, amma Allah ya kawo mun bafulata a sawwake". Abdallah ya fada.
"Toh Mallam ka dauke ido, only first look is halal. Gaskiya kam, kana da over assurance. Amma idan bai yuwu ba, sai mu fada ma Bila, sai ta taimaka ma rayuwar ka. Kuma to be sincerely speaking, ban taba ganin kana ma mace haka ba, but just looking at her made you this way, what if ta yarda, maybe you will loose a knot". Farouq ya fada.
"Ai naga haka kaima kayi loosing din knot, kaga dole in bi sahu". Abdallah ya fada da wasa.

Olamide ko, data fito daga cikin motan, ta gyara tsuwar ta, Nabila ta fito. Kai sunyi kyau sosai. Daman ankon Olamide da Nafisa, daban ne dana sauran kawayen, kuma style din su daya.
Da Nabila ta fito, Olamide ta ce dan gombe bai iso bane"?
"Ke baki gani ne, ga dan gombe can da wani handsome kusa da shi". Nafisa ta Fada.

Su Abdallah na ganin fitowan Nabila, suka kara sa inda suke. Duk yanmatan da suka wuce, kallon su kawai suke, amma ina ango da abokin ango, anyi nisa.

Nafisa na ganin suna zuwa direction din su, tace "subhanallah, Bilatu, wannan shi ne wanda kika fada mana ko"?
"Ae shi ne, harkin fada a tarkon sa ne"? Nabila ta tambaya.
"A'a, ya mun haske da yawa. Nikam na bayan nan, daya ke bayan angon ki directly, ya shiga mun rai, ala dashi za'ayi wuf". Nafisa ta fada tana dariya.
"Ohhh Asim! Ai shima Doc ne. Yawancin abokan yaya na, Doc ne". Nabila ta fada.
"Habibty, yana ga kin yi shuru ne, ba zaki tofa naki ba"? Nafisa ta tambayi Olamide.
"Toh me zance, duk basu mun ba. Bana imagination akan abun da nasan da kyar ya zama gaskiya. Ai suna jin koni wata yare ce, zasu fara nuna mun tribalism, kuma kunsan bana taking shit. So in other to avoid that, gwanda na auri bayarbe ko dan Suleja, hankali na kwance". Olamide ta fada.
Nafisa na son ta yi magana kenan, su Abdallah suka iso.

Da suka jeru, Olamide da Abdallah suka kasance side by side, Nafisa taso ace ita da Asim suna side by side, unfortunately, yana bayan wanda ke side din ta, kaman tace masa suyi exchange da Asim.

Da kowa ya samu wuri ya zauna, kawayan amarya suka zauna kusa da ita, akan stage. Ai ko Abdallah ya ita satan kallon mide, tun bata sani ba, har suka zo suna ido 4 har sau uku. Na hudu kuma, Mide ta harare shi, ta murguda mai baki, amma ko ajikin shi, instead ya ragu, sai kallon ya karu. She was feeling soo uncomfortable, sai tace ma Nafisa "Habibty, inaga zan tashi anan in koma inda jama'a suke, am feeling uncomfortable". Olamide ta fada tana daure fuska.
"Kai habibty, haka bai dace ba, kinga mune manyan kawaye, ya kamata mu tsaya da ita, wallahi zata ji wani iri inta gan ki a can". Nafisa ta fada.
"Ni kadai nasan abun dake damuna, amma I will be patient. But if I keep feeling this way, gaskiya zan bar wajan nan" Olamide ta fada fuska a daure.
"Ae, ki bari, zan maki coverup a lokacin, but for now ki zauna please".
"Shikenan" Olamide ta amsa.

Bayan some mins, aka fito rawa, Olamide tayi gum kaman bata wajan. Amma Nafisa kuwa ana can Ana cashewa.

Abdallah ma yaki shiga wajan rawa, ya zauna kan kujeran sa kaman wani boss, yana ta dubawa ko zai ganta cikin masu rawa, amma yaga bata wajan, sai yaga Fisa ana cashewa. "Hmm, yarinyar nan akwai busy body. Although nasan na yaba mata, amma bata da natsuwa. Amma ga qalbi na, bata shigo cikin wannan hayaniyan ba, qalbi na natsasiya ce.

Da Olamide ta gaji da kallon masu rawa, ta tashi zata bar gurun, wayan ta yayi ringing, tana duba wanda ya kira, taga Hakeem. Ciki jin dadi da walwala, ta daga, sannan ta fita daga hall din, saboda kara yayi yawa.

Abdallah na juya kan sa, ya gan ta zata fita, ya tashi cikin natsuwa, ya biye mata baya, nan yaji tana waya. Ya aza ko saurayin ta ne take waya da, har heartbreak ya fara kama shi, sanda yaji tana cewa zata dake shi inta dawo, shi yasan bayanda zata ce zata daki saurayin ta. Hakalin sa bai gama kwaciya ba, sai lokacin da yaji tana kiran Fa'iza da autan Mummy, sannan hankalin sa ya kwanta. Yana ta ears dropping, har ta gama waya. Yana jiran yaga ta juya ta shiga hall, sai yaga ta nemi kujera, ta zauna. "Wato qalbi bata son damuwa da hayaniya kaman ni, hmm maybe in mata magana yanzu, because banda time kuma, gobe daurin aure, kuma ana gamawa, zamu kama hanyan Gombe, gwanda kawai na fada mata yanzu".
Sanda yayi addu'a ya tofa ma kan sa, dan according to him, this is a life changing matter.

Da Olamide ta gama waya, ta ce bari ta zauna kafun masu rawa su gama rawan su, sai ta koma. Sai ta nemi wuri ta zauna, ta kunna data, tana WhatsApp. Tana cikin chatting din ta, taji ana mata sallama.

Daya gama addu'a, ya tofa, ya kara cewa "ya Allah, kaga niyya ta akan ta, I don't mind getting married to her in the next two to three months, but Allah you know best, if she is going to be good for me, ya Allah kasa ta yarda dani, in kuma she will not be good for me, ya rab kasa karma ta saurare ni".

Da bismillah, ya fara takawa har inda take, yaga duk hankalin ta na kan wayar hannun ta, sai yayi sallama. A hankali ta dago kai, ta amsa mai.

Olamide na ganin shi ne mai kallon ta a hall, ta fada a zuciyar ta, tace "ai kuwa sai ka fada mun dalilin daya sa ka kure ni da ido, sai kuma na maka lectures, saboda Islamically, only first look is halal, we are meant to lower our gaze, both male an female".

Tana cikin tunani, taji yace "ina iya zama akan wannan kujeran"?
"Ka zauna ma, tunda dai baa kai na zaka zauna ba". Ta fada tana wani bata rai". Tana fadan haka, ta maida hankalin ta kan wayar ta.

"Dan Allah ki dan bani attention din ki, magana mai mahinmanci zan miki". Abdallah ya fada.
"Toh ina sauraran ka". Olamide ta fada, sanan ta kashe kawar.
"MashaAllah. Gaskiya ban san daga inda zan fara ba, amma let me start from anywhere. Please try and understand me, cause have never done this before". Abdallah ya fada.
"Ba damuwa ina jin ka" Olamide ta fada.
"MashaAllah. Gaskiya kin burge ni, yanayin ki ya burge ni sosai. Yanda kike babbar kawan nan, da wata ce data caba fuskar ta da makeup, kuma tasa kaya anyhow, irin yanzu da ake rawa, ta zaman gaba awajan, kuma ta dunga rawan kai, amma ke kam ko ajikin ki. Wallahi tun da kika fito daga mota, nake ta observing din ki, and subhanallah, I found the feature in you, although yau na san ki, kuma yau din ma bai wuce 1hr ba, amma ji nake kaman na san ki da'a".
Haka Abdallah ya ita zuba, ikon Allah, mutumin da baya wani sonyin magana dayawa da mutani, Olamide ko sai kallon shi take.

"Baki ce komai ba sister. Sorry, ban mayi tambayan sunan ki ba, am very sorry for that. So please zan iya sanin sunan beautiful creation din Allah"? Abdallah ya yana murmushi.
"Uhmnn Olamide". Olamide ta amsa mai.
Cikin surprise, Abdallah yace "Olamide, ai wannan sunan yarbawa ne, ko akwai wannan sunan ne cikin Fulani, amma ban taba ji ba".
"Toh ni nace maka ni Fulani ce?
Shi yasa ma bana son yan north na mun irin wannan maganan, dan yanzu zaku fara tribalism din Ku, mtchwwww" ta ja tsaki, ta maida hankalin ta kan wayar hannun ta.
"A'a sister, ni dai am not one of them, amma wallahi nayi zaton ke bafulatana ce".
Cikin zafin rai, ta kashe wayar ta, tace "tunda kaji ba bafulatana bace, sai ka tashi ta koma inda ka fito, dan daman anan ka same ni".
"A'a kar muyi haka da ke. Saboda ke ba fulani bace, doesn't mean zan nuna maki banbanci, although akwai *BANBANCIN KABILA* tsakanin mu, saboda hakan yasa nakara son ki miss Olamide. So can I have digit please, kinga sai mu fara zumunci".

"Hmm ban san shi a kai ba". Bata gama magana ba, taji muryar Nafisa tace "ni nasani". Nan taba shi digit din Olamide, ita kuma tana ta fushi, dan still bata so bashi numbern ta ba.
" So Mr Handsome, inba damuwa, zan dan rage maka jindadi, saboda Mide has to be inside likewise you".
"Ba damuwa, nagode maki sosai kawar mu".
"Awwwnn my pleasure mijin habibty. Amma sunana Nafisa". Nafisa ta fada tana murmushi kar kunne.
Chapter 12 · 0% Book details