← Book details Banbancin Kabila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 37

Sashe 6

Banbancin Kabila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna isa school, suka fara zuwa bursary, suka bada receipt, dan daman sun riga sun biya school fees din su a bank. Daga nan suka fara biyan student unions, sukayi online reg ma. Arannan dai sun dade a school, dan basu bar school ba, sai misalin 5:30pm.
Agajiye suka koma gida. Suna shiga gate din gidan, wasu neighbours dinsu su biyu, suma student ne, suka rungume su. "Oyoyo Olami's" daya daga cikin su mai suna Hafsat ta fada.
"Oyoyo my yar'fara". Olamide ta amsa.
Nafisa kuwa, abun ya kai mata har wuya. Ta tsani taga ana shishige ma habibtyn ta haka.
"Ooh Olami's, ko dan kiban nan baki yi ba. Ni na rasa irin wanan jikin naki, ba ya karuwa, kuma baya raguwa". Halima dayan kenan, ta fada. Halima da Hafsat, dakin su daya suma.
Gidan da suke, one room apartment ne, bedroom, kitchen, and toilet. Kuma apartments hudu ke gidan.
"Nima na rasa roomie. Kuma gata da zubin fulani. Abun dake bata show, shi ne inkaji ance Olamide. Nan ma in baka san ita bace, toh zaka nima Olamide ka rasa". Hafsat ta fadi.
"A'a Hansey, kar muyi haka da ke. Kuma bari mu shiga daga ciki tukun, kunga yanzu agajiye mu ke". Olamide ta fadi.
"Awww, haka ne fa. Fisa baby, ya gajiya, na ma manta kina wajan". Hafsat ta fada.
Nafisa kuwa ta riga ta cika, tayi fam, amma bata son su gane, sai tayi faking din murmushi, ta bar wajan. Olamide ko ta riga ta san abun dake damun kawar ta, sai tayi murmushi, ta ce masu Hafsat "zaku biyo mu dakin mu ne yanzu, ko kuma sai bayan isha ku shigo kaman yanda kuka saba"?
"Hmmmm, zamu zo bayan isha, saboda alokacin hira ke yin pepper ko Hafsah"? Halima ta tambaye ta.
"Ae hakan ma yayi. Amma Olamis, baki kyauta ba, ko kiyi tambayan su Khausar da su iklima".
"Awww sorry, na ma manta da su wallahi". Olamide ta fada
"Sun ce sai next week zasu dawo. Kinsan Khausar da Hafiza cousin's ne, kuma rana daya suke zuwa. Su Iklima da Mufida ma, suma sunce sai next week".
"Gaskiya ne, zamuyi complete kenan next week. Allah ya dawo dasu lafiya".
"Amin". Halima da Hafsah suka amsa.
"Yauwa, kunga bari in shiga ciki, na gaji sosai". Tana fadan haka, ta bar wajan, bata ma tsaya jin amsan su ba.

Data shiga ciki, ta samu Nafisa ta jingina da pillow, tayi lamo kaman bata jin dadi. Ta cire hijabin ta, tayi hanging din jakar ta, ta sa takalmin ta amazunin shi, sannan taje kusa da Nafisa, ta taba ta, tace "ya akayi ne habibty, tun awaje naga mood din ki ya chanza".
Sanda tayi wani nishi, ta ce "babu, me kika gani"?
"Don't ask me that, na san akwai abun da ke damun ki, ki fada mun mana please, kar ki bari hankali na ya tashi".
"Babu komai fa, am just resting ne kawai".
"Please stop telling me that, kin san bana taba kaunan in gan ki ahaka, hankali na na tashi". Olamide ta fada helplessly.
"Ba komai my habibty, let just say ina missing din gida ne".
"Ban yarda ba Nafisa, ban yarda ba. I thought am like a sister to you, then what is my role as a sister"? Mide ta tambaya.
"To always be there for me in any situation, and vice versa".
"Then why are you not letting me play my role". Alokacin, har idanuwan ta sun kada.
"Bakomai, kawai dai, kawai dai". Bata iya completing din statement din ta ba, ta fashe da kuka.
Abun so ya samu, Olamide ma ta fara kuka. Sai suka rungumi juna suna kuka, Olamide na rarrashi Nafisa. Cikin kuka Nafisa ta ce "na sani inga ana miki shishigi, yana kona mun rai, na tsani inga mutum na nuna maki so agaba na, sai in dinga jin wani iri. Wallahi na dauke ki tamkar yar'uwa ta ta jini, shi yasa kika ga nake kishi akan ki. Kina nuna mun son da maybe in ma ina da yaya ko kanwa, da kyar sununa mun. Kuma soyayya bai tsaya akan ki ba, harda Mummy da kannan ki, kuna nuna mun so sosai. Shi yasa in naga wata na kokarin shige maki, sai inji kaman za'a kwace mun ke". Ta fada tana kara volume din kukan ta.
"Shiiiiii, ya isa haka habibty, bana son kukan nan, kar ciwon kai ya kama ki". Ita ma ta fada tana kuka.
"Zan daina, amma sai kinyi promising dina ba zaki bar ni ba, zaki tsaya da ni kaman yanda true sisters ke tsayawa da juna". Nafisa ta fada.
"Am not perfect, and I don't know what tomorrow holds, amma ina son ki sani I will always be there for you ore mi( kawa ta)".
"Shikenan, na daina kuka, kema ki daina. Kuma nima na maki alkawari, I will always stand by you".
"Yauwa, ki daina kishi, Fai'za ta Nafisa ne, itama Nafisa ta Fai'za ce".
"Ae". Nafisa ta amsa, tana goge hawaye.
"Kinga tashi muyi alwala, ana kiran sallah".
"Okay toh. Amma me zamu ci ne da daddaren nan, wallahi yunwa nake ji".
"Toh mu ci talliya mana". Olamide ta fada.
"Gaskiya kam, tunda muna da stewssssss".
"Hahhhh, gaskiya kam muna da su".

Da suka idar da sallan magrib, suka sa talliya awuta, kafun isha, har ya dahu sun ci, kafun suyi isha. Suna idarwa, kaman su Halima na ganin su, suka shigo.
"Ooooh yes Olamis, mun zo shan hira. Kinsan jiya da kika dawo, bamu nan, munje gidan aunt dina, nan muka kwana". Hafsah ta fada.
"Hmmm haka ne. Ko dai anje hmmm....". Olamide ta fada tana murmushi.
"Kefa mun chanza, mun daina".
"Allah yasa". Nafisa ta fada.
"Ke zan mazge ki fa". Halima ta fada.
"Ki mazge ta, adalilin me"? Olamide ta fada.
"A'a aunty, kar kiyi fushi. Mun san baki son ana tsokanan habibtyn ki"
"Gaskiya kam bana so, ko kadan". Halima ta amsa.
"Ku manta da wannan, mu sha hiran mu kawai". Hafsah ta fada.
"Ae ku sha hiran ku. Ba shekaran jiya na dawo ba, me ya hana ku zuwa shan hira"? Nafisa ta fada.
"Babu, kema fa kin san mun fita, kuma ai da muka dawo mun dan shigo ai". Halima ta amsa.
"Ya isa. Kun san me"? Hafsat ta tambaya.
"Ya zamu sani"? Olamide ta fada.
"Kai habibty, you always have answers to every question". Nafisa ta fada, tana dariya.
"Kuyi shuru mana". Hafsat ta fada.
"Mun yi". Suka fada a tare.
"Aha, Nabila fa ta kusan aure".
"Wace Nabilan"? Olamide ta tambaya.
"Nabila kawar ku mana, bata fada maku ba ko?
Actually nima dai ba ita ta fada mun ba, naji ne, kin san gidan su ba nisa da gidan aunty na". Hafsat ta fada.
"Ai ko in bata fada mana ba, baza mu je ba ko habibty"? Olamide ta tambayi Nafisa.
"Ae, mu bamu gayyan sodi". Nafisa ta amsa.
"Kai! Why is your blood rushing, ai bata fada ma kowa bako, kuma dai kun san zata fada maku". Hafsat ta fada.
Olamide tayi wani dariya, sai ta ce "abun ya yuwu da dan gombe kenan". Tana fada, suka tafa da Nafisah.
"Toh ku ma yaushe za'ayi naku"? Halima ta tambaya.
"Randa Allah yaso. Kuma kema kin yi ne"? Nafisa ta tambaya.
"Toh ai na kusa, next year In Sha Allahu, maybe june'.
"Allah ya kai mu, amma still you have no right to ask us, tunda ba'a gwanjo ake samo mazan ba". Olamide ta fada.
Duk suka fashe da dariya.
"Gwanjo kuma habibty?
Kin san gwanjo ma akwai grade ko"? Nafisa ta tambaya.
"Ae da anan ake samun su, da zamu dinga zuwa da wuri, dan mu samu grade, ba zamu ba in 9:am yayi , sai dai ya same mu acan". Olamide ta fada.
Duk suka kara fashewa da dariya.
"Kai Olamis, baki da dama. Shiyasa nake son hira da ke. Although kin iya shunning din mutum, amma still kina da ba mutum dariya, but banda angry part din ki, lokacin da kike mantawa kinba mutum nickname, sai ki kira sa da sunan sa". Hafsat ta fada.
"Bari kawai yar'faran habibty, ai in habibty tayi fushi, ta na mantawa da soyayyan da take nuna ma mutum. Kinga in tayi fushi, alokacin zaki ji tana NAFISA SULAIMAN".
Duk suka fashe da dariya.
"Bari kawai ba zaku gane ba. Ai alokacin, nickname baya mun dadin fada, sai dai sunan mutum".
"Toh Allah ya shirye ki. Ya zaki yi da mijin ki, ko shima da sunan sa za'a na kiran sa, in ya kai ki neck"? Hafsat ta tambaya.
"Ke abu kadan miji, baki gajiya ne. Toh ko shima, zan kira sa da sunan sa, so he will know am serious".
"Toh ai it's not my fault, at this stage of life, abun da ya kamata mu damu da shi kenan. In mu kayi aure kuma, mu fara maganan yara". Hafsat ta fa.
"Toh sannu marriage consultant. Kai yar'fara, wanan aikin zai miki kyau fa". Olamide ta fadi.
"Sosai ma". Halima da Nafisa suka amsa.

Su Halima basu bar dakin su Olamide ba, sai 9:39pm. Nan ma, saboda Olamide ta masu complain cewan suna jin barci ne. Inba haka ba, basu ki aita hira ba har cikin dare. Wani hiran ma sai sauran hudun sun dawo.

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️
Chapter 6 · 0% Book details