← Book details Banbancin Kabila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 37

Sashe 25

Banbancin Kabila Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Suna breakfast, suna hira, magana daya biyu, sai Nabila ta fada masu yanda zata yi missing din su, su kuma su ita fada mata maganganun da zasu yi calming din ta. Haka suka ita yi, har suka gama hada breakfast din su, suka ci, Nabila ma ta ci da su, sannan suka yi mata wanke wanke, duk da ta nuna masu bata so, amma haka suka yi. Da suka gama clearing din komai, suka koma daki, itama ta koma dakin ta.
Da suka shiga, Olamide ta samu wayar ta na ringing, ta yi suri ta dauki wayar, sunan mummy ya fito a screen din, ta daga cikin murna.
Sun yi 20 mins suna magana, tayi tambayar Farida, Mummy tace tana nan tana shirin school. Daman Hakeem ya koma school shi ma, so mummy da Farida suka rage a gida, Mummy ta masu addu'an Allah ya sauke su lafiya, tace ta ba Nafisa wayan, daga nan suka yi sallama, suka kashe wayan.
Ai ko bai fi 5mins ba, kiran Abdallah ma ya shigo. Cikin kunya, ta daga.
"Assalamu alaikum ifemi."
"Waalaikumus salaam qalbin Abdallah. Kin tashi lafiya, ya gajiyan jiya?" Abdallah ya tambaya.
"Lafiya kalau. Kai fa?" Olamide ma ta tambaya.
"Same alhamdulilah, but I kept dreaming about Mrs Abdallah Umar Muhammad Yero. I can't wait for you to be mine yide am (my love)."
"Me too ifemi, I can't wait. But meye ma'anan yide am kuma." Ta tambaye shi confusedly.
"Aww, ashe sai na dinga koya ma yide am fulatanci." Abdallah ya fada, su biyu suka yi dariya. Olamide ta ce "ae mana, kar azo ana zagi na."
"Haba qalbin Abdallah, bazan taba zagin ki ba, ko wani naji yana zagin ki, mai raba ni da shi sai Allah, sai ni na zage ki?
Toh maybe am mad then. So yide am means my love. Or ain't you my love?" Abdallah ya tambaye ta.
"Aww, ashe ma'anan shi kenan. Of course am your love yide am." Ta fada a kunyance kaman yana ganin ta.
Suna cikin waya, ita kuma Nafisa sai kallon ta take, Nabila ta shigo, tace ma su su fito, yanzu zaa kai su gareji. Nafisa ta tashi, ta dauki handbag din da suka sa kayan su, da side bag din ta, ta ma Olamide signal da hannu ta dauki nata bag din, da wani amebo leda. Olamide tayi nodding kan ta. Sai ta ce "uhmm ifemi, yanzu yaya Farouq zai kai mu gareji, zamu yi waya anjima."
"Okay, kinn ki in kai ku park din. But anyways, in kuka isa park, ki kira ni. Bye, mi yidi ma yide am. Meaning ina son ki masoyiya ta." Abdallah ya fada.
"Bye, mo ni ife re emi na ifemi. Meaning I love you too my love."
"MashaAllah, zan koya maki fulatanci, keh kuma ki koya mun yarbanci. I really love the way this words came out of your mouth, although am not seeing you. Anyways bye qalbin Abdallah." Abdallah ya fada, sai ya kashe wayar.
Ba abun da Olamide ke yi inba murmushi ba, gaskiya Abdallah na faranta mata rai sosai, Allah yasa iyeyen sa su yarda, saboda ta san from her side, bata da matsala, mummy zata yarda, dan a familyn su, akwai wayanda suka auri wasu kabilan.
Ita ma ta sa hijab din ta, ta dauki side bag din ta ta rataya a kafada, sannan ta dauki amebo ledan, suka bar dakin tare da Nafisa.

Da suka shiga parlor, suka samu, Farouq da Nabila na jiran su, su Olamide suka gaishe shi, sannan dukan su suka fita, Farouq ya sa ma kofar key, suka shiga mota, Nabila a gaba su Olamide kuma a baya. Farouq yayi horn, mai gadi ya bude mai gate, ya fita, sai gareji.

Luckily, suna zuwa, akace mutum biyu ya rage motan ya cika, sharp sharp aka yi loading kayan su, nan suka ita hugging din juna, Nabila harda kwalla. Da suka shiga motan, ta yi waving din su, Farouq ya riko hannun ta, suka matsa ma motan ya samu hanya ya wuce, suka ita waving din juna, har motan su ya bace masu, sannan still hannun Nabila cikin nasa, ya bude mata gaban motan ta shiga, sannan ya je driver side, shima ya shiga. Sanda ya ita rarrashin ta, kafun tayi shuru, shima ya ja motan, suka koma gida.

Su Olamide kuwa, motan su na barin gareji, ya kama hanyar barin Gombe, ta ce "kai Habibty, gaskiya garin Gombe nada kyau fa sosai."
"Bari kawai. Am going to miss this state, duk da cewa bamu san ko ina ba, still garin ya kwanta mun. Balle ma, muma fa nan zaa kawo mu, zamu ga garin, har ya ishe mu."
"Hahhhh habibty, wallahi kin ban dariya, wai nan za'a kawo mu." Olamide ta fada tana dariya, data ga mutani na kallon ta, ta rufe fuskan ta da tafin hannun ta.
"Toh daa karya nake, kema dai kin san nan zaa kawo mu, inda rai da rabo In Sha Allah." Nafisa na rufe baki, wayar ta ya fara ringing, sunan Asim ya fito, sai ta kalli Olamide, ta daga mata gira, tace " bye sweety, ki kira ifen ki."
Nan Olamide ta tuna yace ta kira shi in suka isa gareji. Sai ta dauki wayar ta, ta fara kiran Mummy, ta sanar da ita motan su ya tashi, suna hanya, mummy ta yi masu addu'a, sai ta kira Hakeem ma, tace mai ga shi gari kusa kusa suke da school din sa, amma ba halin su hadu. Suka dan yi hira, kafun yace mata yana da lectures, zai tafi school, ya masu addu'an safe trip, ya kashe wayar. Zata kira Abdallah kenan, kiran Ummin Nabila ya shigo. Ta daga, ta gaishe ta, ta ita masu godiya, tace ta ba Nafisa, tace Nafisa na waya, ta masu addu'a, suka yi sallama, ta kashe kiran, sannan ta kira Abdallah, har kiran ya katse, bai daga. Yana tsinkewa, bai fi 2mins ba, kiran sa ya shigo, ta daga, tayi sallama, ya amsa. Ya ce "sai yanzu kuka isa gareji, this is 8 something fa qalbin Abdallah, gashi na ita kira, ana ta ce mun line busy, da wa kike waya haka ne?"
"Da mutani nake waya."
"Toh su mutanin basu da suna ne?" Abdallah ya tambaya.
"Nace maka mutani, ka bar wannan zancen, and wish us a safe trip."
"A'a gaskiya bazan iya barin zancen nan ba, why is it so hard ki fada mun sunan su?" Ya tambaya.
"Nothing." Olamide ta amsa.
"Then tell me please, inba haka ba, my mind won't be at rest." Abdallah ya fada.
"Nifa bana son kishi wallahi ifemi. Kuma da mummy, da Hakeem, da Ummin Nabila muke waya."
"Toh what was hard there yanzu. Kuma gaskiya indai kishi ne, sai dai kiyi hakuri, dan ina matukan kishin ki, amma in the right way."
"It's better be in the right way gaskiya, dan ni kam bana son bakin kishi. So wish me safe trip."
"Toh yide am, Allah ya sauke ku lafiya, ya tsare maku hanya, ya kare ku daga sharin karfe, da duk wani sharrin dake kan hanya."
"Amin my young doctor." Olamide ta amsa, tana murmushi har kunne.
"Yauwa qalbi, nima yanzu zan shiga office, so ina Samu break, zan kira ki."
"Okay toh, Allah ya baka saa, banda kallon yan mata." Tana fada haka, ta kashe kiran, tana murmushi.
Shima yayi murmushi, dan yaji dadin maganan ta sosai, wato tana kishin shi, shine take cewa bata son kishi. Daman baya kallon su, gashi yide(love) tayi warning din sa, gashi islamically, it is said to lower your gaze, so abun yazo daidai.

Throughout lokacin da Abdallah yake aiki, yaki kallon female patients, sai dai yaji complains din su, ya karbi card, ya rubuta masu magani, ya mika masu, next patient ya shigo. Haka ya ita yi, har lokacin break yayi, suka hadu da Asim, suka fara zuwa masjid, suka yi sallah, kafun suka aiki wani cleaner, ya siya masu drink da biscuit. Saboda basu son cin abincin a waje, gashi ba wanda ya kawo lunch daga gida acikin su. Never the less, by 2 something zasu bar wajan aiki. Kuma gaskiya sunyi missing din Farouq Sosai, click din su bai yi complete ba without him.
Chapter 25 · 0% Book details