← Book details Bahiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 23

Sashe 17

Bahiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da wuri na je gida na shiryo mana abin karyawa na ɗauko wa Nuhaira tufafi kamar yadda ta buƙata.
Ƙarfe tara a Office ɗin doctor Sam tayi min, cikin farin ciki na shiga shaida ma cewar na samo kuɗin aikin Mama, shima congratulations ya shiga furta min tare da faɗin in bari ya kira asibitin yaji yaya za'a yi.

Muna nam sai ga malama ta zo abinda take shaidamin shine tayi ta neman layin maman Khadijat baya shiga ga shi har 10:00am tayi amma Hajiya Hanifah shiru.

Bayan mun gama tattaunawa da likitan ɗakin da mama take kwance muka koma muka ci gaba da tattaunawar a can.

Firar mu ke amma gaba ɗaya yanzu hankali na ya dugunzuma ya koma kan Hajiya Hanifah, ƙirjina sai dukan uku-uku yake ganin ta kai har zuwa wannan lokacin bata zo ba, kar dai ace fasawa tayi? Wayyo Allah na....
Ban tantance cewa kuka nake ba sai da naji Malama na faɗin.

"Subhanallah! Bahiyya lafiya kuwa?”

“Matar nan fa har yanzu bata zo ba Malama, kada ta canja niyyarta gashi har sha biyu tayi.”

“Kwantar da hankalinki haba, in sha Allah tana tafe”

Daga haka ban sake cewa komai ba na yi shiru cikin raina ina faɗin Allah yasa haka.

Ba mufi minti ashirin da gama maganar ba sai gashi an aiko ɗan aike cewa ana nema na a Office ɗin doctor Sam.

Ko da naje zaune take a office ɗin suna magana da ita da turanci da alama maganar aikin Maman ce suke yi.
Na jima a tsaye kafin nan suka gama ta juyo ta kalle ni kai tsaye tace.

"Aikin ki ya kambala, na cika nawa alƙawarin saura naki”

Murmushin nasara na saki ina faɗin.

“Nagode na gode Allah ya saka da alkairi....” daga haka na fita da gudu  naje na kira Malama da Nuhaira suka zo.

Kallon halittar ta Nuhaira ta tsaya yi tana mai ƙara tsinkewa da lamarin ta domin ba ƙaramar mace ta gani ba, tasha wasu riga da wando, rigar bakin guiwa ne sai wando plazo tayi ɗan ƙaramin rolling ɗin nan na manyan matan nan, ko mai hassadar ka idan ka kalli Hanifah sai ka sara mata, fatar luwai-luwai ga faranta mai ɗaukar hankali ga wanka komai na ta manyan mata.  sai zubo mata addu'o'i take tamkar wata zararrariya bayan ta gama ne Malama ta kalle ta Itama tace.

“Mungode sosai Hajiya, Allah ya saka miki da mafificin alkairi...”

Sai yanzu tayi murmushi tace.

“Ba komai ai dani da Rasi duk ɗaya ne. Allah yasa a dace.”

Daga haka ta miƙe ta fice ni kuma na bi bayanta har bakin motar ta. Ba tare da ta kalle ni ba tace.

"Na gama nawa, idan kin shirya ki zo wurin wannan doctor ɗin naku zai sadaki da ni, bana so ki bar ni na tsaya jira da yawa”

“Ɗan risinawa nayi duk da cewa bata kallo na nace”

" In sha Allahu ba zan jima ba daga zaran an kambala zaki ji ni”

****************

NATIONAL HOSPITAL ABUJA,
CENTRAL BUSINESS
DISTRICT, ABUJA.

Wannan ita ce asibitin da aka shirya za'a yiwa Mama aiki nan da kwana huɗu mai zuwa.
Bayan an yi booking likitan yace sai nan da sati shida za'a aikin, but ganin condition ɗinta ya zama emergency doctor Sam ya shige mana gaba aka yi postponding ɗinsa zuwa kwana huɗu.

Kukan farin ciki na fashe da shi a lokacinda malama ta ke sanar min an gama biyan kuɗin aiki har da kuɗin magani, sannan akwai 500k daga maman Khadijat  inji ita Hanifah ɗin. Sannan kuma tace bayan shi ko da ace an gama aikin idan akwai wata matsala za'a neman ta kai tsaye ta hanyar doctor sam, sannan kuma tace idan anyi nasarar aiki an bata sallama akwai million biyu da za'a bawa Mama daban ta ci gaba da kula da kanta da Nuhaira kafin na dawo, tunda likitan ya gaya mata cewa ni ce babbar 'ƴarta duk wani rabin nauyin ya rataya ne a wuyana yasa ta ƙara mana da wannan kuɗin na daban. Nan Malama ta ji ta saki jiki da ita tayi amanna da kirkin ta tare da yi mata addu'a.

Bayan an gama shirya komai kwana biyu tsakani muka tattaro kayanmu da Mama muka dawo nan asibitin. Ɗaki ne aka bamu mai zaman kansa wai shi amenity, komai akwai cikin ɗakin tamkar kana gida zaune.

Bayan Malama ta koma gida na zo na zauna kusa da Mama na kalle ta da murmushi a fuskata na saƙala hannuna cikin nata nace.

“Mama na! Ina sonki, Ina matuƙar sonki ina alfahari da ke Mama. Haƙiƙa duk mai haƙuri yana tare da Allah, ubangiji ya dubi maraicin mu ne yaga bamu da wata mafita shi ne ya turomana agaji ta hannun wannan baiwar tasa mai cike da albarka. Alhamdulillah! Allah shi ne abin godiya, Allah ya ji ƙan Baba da Rahma. Haƙiƙa kin kula dani kin bani tarbiyya da ke da Baba iya gwargwadon iyawarku na yi miki alƙawarin zan kare mutunci na a duk in da na shiga a faɗin duniya komai wuya komai tsanani.”

Murmushi ta sakar min itama tana mai gyaɗa kanta a hankali ta buɗe bakinta murya can ƙasan maƙoshi tace.

“Allah yayi muku albarka Bahiyya, yadda kuka ji ƙaina kuka tausayamin ina roƙon ubangiji ya baku rayuwa mai albarka ya baku mazaje na gari ko bayan bani a duniya”

Kallon ta na sake yi tare da jin nauyin kalmar ta ta ƙarshe a ƙirjina tamkar an ɗoramin falalen dutse nace.

“Mama kullum na tambaye ki sai kice zaki faɗamin Mama, dan Allah ki faɗamin mi yasa muka kasance mu huɗu kawai a duniyar mu? Ga shi mun rasa Baba duniyar mu ta sake canzawa zuwa mu uku kacal, shin mi yasa Mama ba zamu iya komawa ƙasar mu ba?”

Girgiza kanta tayi tare da haɗiye wani yawu mai ɗa ci a maƙogwaronta tace.

"Bahiyya ba ina ɓoye muku bane don wani abu, babu kalma ɗaya mai ɗaɗin saurare a cikin wannan mugun labari, domin idan har na sanar dake zaki yi ta damuwa ne a banza, zaki tsani dangin Mahaifin ki tsana ta har abada, sannan kuma zaki yarda cewa tsakanin 'ƴan uwa na jini babu amana. Ki bar wannan maganar Bahiyya”

Shiru tayi tare da juyamin baya alamar bata son ma zancen ganin haka yasa nima na kama baki na nayi shiru tare da tattara kaya na fita na kira Nuhaira nace ta dawo in da take.

***************

Tunda aka shiga da Mama na je na ɗoro alwala na fara jera nafila ina ta kai kuka na a wurin mai duka akan ya taimake mu yasa ayi lafiya a ƙare lafiya,yayinda Nuhaira da Malama suke girke a bakin ɗakin suna zaman jira.

Wannan likitan doctor Sam ba musulmi ba ne amma yayi mana abinda tsawon rayuwar mu ba zamu manta da shi ba, komai ake yana nan tare damu yana taimaka mana.

Ƙarfe biyu na rana aka fito da Mama daga ɗakin tiyata zuwa ɗakin hutu. Muna nam jugum jugum muna ta kallo aka yi mata duk abinda ya kamata ayi mata na bayan fitowa tiyata.

Mu kuma muna nan muna ta aikin kula da ita duk da cewa bata cikin hankalin ta yanzu.

Ku san Ƙarfe biyar na yamma ta farfaɗo wanda ni kai na da nake kusa da ita bana jin mi take cewa, muna cikin murnar kawai muka ga ta fara fisge numfashi ƙirjin ta na sama da ƙasa, jikin duk ya ɗau mazari, a gigice na nufi waje wurin nemo likita, yayin da Nuhaira ta shiga rera kuka mai ban tausayi........

*Oum Ameer*
💝 *BAHIYYA*💝

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

               *BY*
*AMINA IBRAHIM*
  *(OUM-AMIR)*

*BAHIYYA NOVEL ƊIN KUƊI NE KIBIYA 500 TA WANNAN ASUSUN 3132703269 FIRST BANK AMINA IBRAHIM SAI KI TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAYIN 08068974831*

*FREE PAGE*
          *BABI NA GOMA SHA BIYU*

......... A Irin yadda muka ga jikin Mama ya rikice bamuyi tunanin likita zai kai ga shigowa ba ruhinta bai bar gangar jikin ta ba. amma cikin ikon Allah sai gashi a hankali bayan likitan sun shigo sunyi iya yinsu ta dawo normal.

Kulawa mai kyau Mama ta samu tun daga doctors har zuwa nurses da mu kanmu, Alhamdulillah! Aiki ya yi nasara domin Mama ta samu lafiya sosai tamkar ba ita ce a mawuyacin hali a kwanakin baya ba. Saida muka kwashe sati biyar masu kyau sannan aka bamu sallama da kuma lokacin follow - up a kai a kai domin gujewa matsala bayan an ɗora ta akan tsarin maganin da ya dace. Kuma doctor Sam ya tabbatar mana cewa daga yanzu har abada ya dawo likitan ta duk lokacin da taji wani sauyin yanayi a jikin ta zata iya zuwa gare shi.

Gida mai daɗi. Tunda muka koma nayi sallar zuhr bacci ya ɗauke ni sai bayan asr sosai na farka da wani irin tsoro, domin mafarkin dai kamar ko yaushe babu daɗi, wanda har ya zame min jinin jiki wanda a yanxu sai dai inyi addu'ar da manzon Allah (S. A. W) ya koyar da mu, in ci gaba da abubuwan gaba na.

Bayan kwana biyu.
      Zaune muke mu uku muna cin abinci a faranti ɗaya, ni, mama, Nuhaira. Mama ta kalle ni tace

“Bahiyya Malam Maharazu shiru, rashin samun sa a waya ya dame ni”

Cikin alhini nace.
“Wallahi kuwa mama. Abin da mamaki, ki duba duk tsawon lokacin da kika ɗauka a kwance har aka miki aikin nan ace har yau babu labarinsa abun akwai alamar tambaya, ni jiki na yana faɗamin ba lafiya ba”

Nuhaira ce tace.

“Wai Mama da ke da Baba kunce Baba Maharazu ɗan uwanmu, to mi yasa shi yake iya zuwa Nijar ɗin mu ace bamu iyawa?”

Girgiza kai mama tayi tace.
Chapter 17 · 0% Book details