Sashe 8
Asp Zarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
... Jidda ce ta gyara zama tare da fara magana.
"Wani sanannen ɗan siyasa a ciki da wajen Bauchi, anyi mishi shaidar rashin arziki da wulaƙanci gami da cin zarafin na ƙasa dashi, baya ragama kowa kasancewar yana da muƙami ga dukiya kuma daya tara, shiyasa yake taka kowa ya zauna lafiya daga shi har ɗan nashi. Ana faɗin cewa zai iyayin komai akan yaronshi ko da kuwa kisa ne. Shiyasa nake tsoron kar wani abu ya haɗa su da Zarah saboda baza'a haifar da ɗa mai ido ba."
Kai Saleem ya girgiza kana yace.
"Gaki a haka kamar Jaruma amma zuciyarki fal take da tsoro, ni a gani na wannan ba wani abu bane da za'a tsorata har ayi shakkun yin shari'a dashi. Insha Allah zamu zauna anan har sai munga an kwatar ma yarinyar nan hakkinta. Kuma ni zan zame mata lauya."
"A zahiri bakai bane zaka zame mata lauyan amma a baÉ—ini kai ne." Zarah ta faÉ—a idonta a lumshe kamar ba ita tayi maganar ba.
ÆŠan juyuwa Saleen yayi yana son fahimtar abinda take nufi.
"Wani lauyan zamu nema yanzu a matsayin wanda zai kareta, saboda zai iya siye duk wani lauya da zamu É—auka da kuÉ—i. Bayan mun gama yarda muna da lauya sai ranar da za'a shiga kotu mu rasa mafita. Shiyasa a yanzu dole mu É—au wani lauyan na ganin ido, amma a baÉ—ini zamu cigaba da gudanar da bincike tare da haÉ—a shaidun da zamu gabatar a kotu." Cewar Zarah
Sosai suka ƙara mamakin fasahar ta wajen yin tunani abinda masu laifi zasu aikata.
"Sam banyi tunanin haka ba da farko, kuma tabbas nasan Alhaji Mai Riga zai aikata haka." FaÉ—in Jidda tana mai haÉ—e hannayenta alamun jinjina ga Jidda.
Haka suka cigaba da tafiya suna hira jefi-jefi har suka ƙaraso gidan.
Ɗakinta ta wuce kai tsaye tare da shigewa banɗaki, wanka tayi sannan ta fito ɗaure da towel a jikinta. Zama tayi da nufin yin shafa amma ta kasa illa kwakwalwarta dake tariyo mata irin matsalolin da take dasu a gabanta, riƙe kanta tayi da hannu biyu bayan ta kifashi a jikin mirro ɗin.
Saitin zuciyarta ta kuma dafewa da hannu ɗaya tanajin yadda take bugawa da sauri, tabbas tasan watarana matsalolin ƙasar nan zata haddasa mata bugawar zuciya saboda yadda ta ɗau matsalolin tamkar yadda take ɗaukan duk wani abu da ya shafeta ko danginta.
Miƙewa take shirin yi ta nufin saka kaya batare data shafa man ba, turo ƙofar da akayi ne yasata dakatawa tare da maida kallonta ga Baaba dake shigowa bakinta ɗauke da sallama. Amsa wa tayi tare da faɗin.
"Wannan tsohuwa me zakiyi min a É—aki ne haka daya saki haurowa sama, dan wannan zuwan naki kam akwai abinda ta kawoki tunda nasan ba haurowa sama kikeyi ba."
"Yo idan ba wani abu ba mai zanzo nayi a bene nikam salon watarana na faÉ—i a garin sauka." Baaba ta faÉ—a tana mai zama a gefen gadon Zarah.
Sai da suka gama barkwancin jika da kaka sannan Baaba tayi gyaran murya tace.
"Zara'u."
ÆŠagowa tayi ta kalleta, gani yanayin fuskarta ne yasa tagane magana ce mai mahimmanci zasuyi.
"Na'am Baaba."
"Kin sani Zara'u kin kai mun zalin daya kamata ace kema kinyi aure kamar ƴar uwarki Jidda, aure shine darajar duk wata ƴa mace koda kuwa tana da tarin dukiya, kyau, muƙami ko nasaba. Ba mu da yawan zuri'a Zara'u kune muke fatan ku hayayyafa ku sama mana masu yi mana addu'a damu daku gaba ɗaya koda bama a raye, shekarunki na haihuwa fa yanzu 23 yakamata ace kinyi aure kin sama kanki daraja musamman a irin yanayin aikin da kikeyi da ake tunanin duk wata mace da takeyin shi bata da kamun kai. Dan Allah ki siya mana mutunci da kanki kar a fara maganar a gari ana cewa mun barki sakaka."
Shiru Zarah tayi batare da tayi magana ba, Baaba ce ta kuma cewa.
"Munyi magana da babanku Sulaiman yace nagaya miki ki turo mishi wanda kika tsayar domin manya su shiga maganar."
"Baaba bawai auren ne banaso ba, akwai burika na da nakeson cikawa wanda nasan va kowani namiji dazan aura bane zai bani damar cikasu, shiyasa ma bana saka auren cikin lissafina a yanzu amma idan lokaci yayi zanyi insha Allahu." Ta faÉ—a alamun maganar Baaba bata wani dame ta ba.
"Toh akwai wani wanda kuka sasanta ne ko kuma kukeson ku sasanta tsakaninku dashi.?"
"Dan Allah Baaba ki barni ni babu wani da nakeso ko muke soyayya, aikina shine a gabana yanzu." Cewar Zarah da ta miƙe ta nufi gaban durowar kayanta.
"Nima ai ina fatan ki kasance tare da aikinki kodan kawo ƙarshen waɗanda azzaluman mutanen, amma ki dawo ki zauna muyi magana domin bankai ga faɗin sakon da aka aikoni na isar ba."
"Waye kuma ya aikoki.?"
"Toh da farko dai mai saƙon yace bazai zo da kanshi bane gudun kada kiji nauyin shi kiyi abinda bashi ranki ke so ba, alfarma ce yake nema a gurin ki nason haɗa zuri'a dake, ma'ana dai yana neman alfarmar ki akan yanason ya haɗaki da ɗansa ku raya sunnar manzo S. A. W a ƙarƙashin inuwa ɗaya. Kuma yana fatan ace wani bai riga shi ba sannan yace a barki kiyi shawara kafin ki bada amsa."
Wani kallo Zarah ta mata kafin tace.
"Waye da wannan doguwar wasiƙa kuma Baaba."
Miƙewa tayi kana tace.
"Doddon ku mana Sulaimanu yace yana neman alfarmar ki amince da auren É—an sa Muhammad Jawwad."
Dariya sosai Zarah tayi jin yadda Baaba ta kira Daddy wai Doddo kana ta tsagaita ganin har Baaba takai kusa da ƙofa, ƙarasa wa tayi inda take sannan tace.
"Ban fahimce ki sosai ba Baaba."
"Ke dai ba kurma bace sannan kuma ke ba mahaukaciya bace bare nace bakya fahimta, abinda dai kikaji shi nake nufi idan kuma kina tantama ne to ki ɗau waya ki kirashi ya miki ƙarin bayani." ta faɗa tana mai ficewa a ɗakin.
Ta daɗe tsaye a inda Baaba ta barta tana sakawa da kuncewa akan maganganun Baaban, lokaci ɗaya kuma ta watsar da zance daga tunaninta sannan ta nufi durowar ta ɗauko wata doguwar rigar atamfa super ta zura. Mai kawai ta shafa a leɓanta kana ta zura takalmi ta fice zuwa falo inda tasan Jidda na jiranta.
A zaune ta same su ita da Saleem sun tasa laptop a gaba da alama abu suke gani a ciki mai mahimmanci.
Jidda ce ta É—ago ta kalleta tace.
"Madam ASP tun ɗazu muke jiranki anan munkawo ƙara.''
Kyaɓe baki tayi kana ta gaishe da Saleem sannan ta kalli Jidda ta kuma cewa.
"Ace mutum shi kullum cikin zolaya kamar mara damuwa."
"Wace damuwa ne dani nikam, ga mijina a gefe ai sai farin ciki ko da yaushe." Jidda ta fada.
Bata kulata ba sakamakon abinda Saleem yake nuna mata a cikin laptop É—in, shiru sukayi gaba É—aya suna mai maida hankalinsu kan laptop É—in.
"Na rigada na gama bincike kuma na tabbatar shi ne mai laifin shaidune kawai suka rage mana, sannan nayi magana da babban likitan asibitin da yarinyar take akan Jidda zataje ta gudanar da duk wasu bincike da rahoton likita da za'a buƙata a kotu, yanzu binciken ya rage na ɓangarenki daga nan kuma a shigar da ƙara kotu." Cewar Saleem
"Abun zaizo da sauƙi ai, nima yanzu nake so na fita na gudanar da wasu bincike na saboda gobe nakeson a shigar da ƙara kotu." Faɗin Zarah.
"Yanzu baiyi yamma ba Zarah.?" Cewar Jidda.
KaÉ—a kai tayi kana tace.
"Inason zuwa ofishin ƴan sanda da suka fara kai ƙara ne domin haɗuwa da Inspector ɗin wajen, na samu labarin yafi zama a office a irin wannan lokaci."
"Ki tsare shi ya faÉ—a miki gaskiya fa Zarah kuma ya gayamiki nawa a bashi ya danne gaskiya." Jidda ta faÉ—a cike da takaicin abinda aka aikatawa Fahima.
Dariya Zarah tayi sannan ta maida kallonta ga Saleem tace.
"Gaskiya Sa.Jid ina tunanin kwanan nan zan shigar da matar ka aikin ƴan sanda ita ma, naga alama ta fini zaƙewa akan aikin nan."
"A'a ki rufamin asiri, ai aikin Æ´an sanda sai irinkj jajirtattu bana su Jidda bane." FaÉ—in Saleem cike da zolaya.
Dariya suka yi duka kafin Zarah ta miƙe ta koma ɗakinta inda ta ɗauko mayafi da jaga, sallama ta musu sa'an nan ta fice domin zuwa inda ta faɗa musu.
A hankali take driving har ta iso bakin ofishin, kallon gurin tayi wanda ke tsabtace sosai sai Æ´an sanda da mutane dake shawagi É—aÉ—É—aya.
Kasancewae gilashin motar mai duhu ne yasa jami'an basu gane wacce ke ciki ba har saida ta fito, nan tsirarun da suke farfajiyar wajen suka ƙaraso gabanta da hanzari suka sara mata.
Kai kawai ta jinjina sannan ta fara tafiya a hankali inda suke take mata baya har zuwa ofishin Inspector É—in.
MiÆ™ewa yayi da sauri daga kishingiÉ—en da yake tare da miÆ™ewa...... *MANAZARTA WRITTERS ASSOCIATION*📚🖊ï¸
*M*. *W*. *A*
_Putting smile on our readers face_
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsapp
___________________________________
*ASP ZARAH*👩â€âœˆï¸
_Daga AlÆ™alamin_âœðŸ»
_Asmau Bint Abubakar_
_Jasmine_🌸🌸
*Da sunan Allah mai rahma mai jinƙai, dukkan yabo da godiya su tabbata gun Allah maɗaukakin sarki daya bani lafiya, ilimi, basira da kuma lokaci dana samu daman rubuta wannan littafin. Allah yaƙara dubun salati a gun mafificin halitta annabinmu Muhammad S. A. W da ahlinsa da sahabbansa dama dukkan masu bin tafarkinsa har zuwa ranar tashin alqiyama.*
*Ina roƙon Allah ya tsaremin alƙalamina daga rubuta duk wani abu dazai kawo ɓatanci a cikin al'umma. Allah ina roƙonka yadda nafara rubuta wannan littafi lafiya Allah kabani ikon gamashi lafiya, kurakuran dazanyi ciki Allah ka yafemin da wanda nasani da wanda bansani ba.*
*Littafin ASP ZARAH na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da biya ba. Idan kinji kinason cigaba da karantawa toh ki biya kuɗi N300 kacal domin karantashi cikin kwanciyar hankali, idan kinsan zaki dinga yimin sharing ɗin littafi dan Allah kada ki biya kuɗin banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntu6eni a 07048961623 domin biya da kuma shiga group*.
*Jan Hankali*: _Ƙirƙirarren labari ne. Ban yarda a canjamin littafi ta kowace siga ba batare da izinina ba. A bi doka a zauna lafiya_ .
👩â€âœˆï¸
👩â€âœˆï¸
👩â€âœˆï¸
👩â€âœˆï¸
👩â€âœˆï¸
_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_
*Free Page 7*