← Book details Asp Zarah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 21

Sashe 13

Asp Zarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

____Raliya ta gani riƙe da wani abu da take da tabbacin camera ne tana ƙoƙarin mannawa a gefen inda wani babban family photo ɗin su yake, take ta samu duk wasu amsoshin da take buƙata akanta domin tun kallon farko da tayi mata ta hango alamun rashin gaskiya a tattare da ita. Rakuɓewa tayi a jikin window bayan ta hangota ta nufi ƙofar fita daga cikin falon, tana tsaye harta wuce ta shiga ɗakin da aka bata a matsayinta na ƴar aiki, shiga tayi cikin falon batare da ta kunna wutan da ta kashe ba ta nufi inda taga ta ajiye abun, kamar yadda tayi tsammani camera ce da zata iya ɗaukan duk wani shige da fice a falon sannan idan ba mutum ya sani ba babu wanda zaiyi tunanin akwai camera a gun. Ɗauka tayi tare da nufar ɗakin Raliyan, ta wani ɗan rami dake jikin ƙofar ta leƙa ga mamakinta sai ganinta tayi zaune akan katifar ɗakin da ƙaramar laptop a gaban wanda tana iya hangar abinda ke wakana a cikin laptop ɗin, ido ta waro gani hoton ɗakin ta ya bayyana a ciki tare da duk wani abu da ta gabatar tun daga dawowarta har zuwa yanzu.
Kunnenta ta kara a jikin ƙofar ganin Raliya ta ɗauki wayarta ta kara a kunne. Batasan me aka faɗa ba daga ɗaya bangaren sai amsar da ta bayar.
"A'a ranka ya daÉ—e, ina tunanin sun chanja tsarin gidan ne domin gabaÉ—aya an canja tiles É—in da muka sani an saka wasu shiyasa bangane wanda zai kaini underground din ba."

"Alpha." Zarah ta furta a hankali. Tabbas yanzu zarginta ya tabbata Alpha ne wanda ya turo Raliya tayi basaja a matsayin ƴar aiki, bayan sun tabbatar da bata gida a lokacin domin tabbas da tana gida baza a ɗauki Raliya aiki ba. Rufe na'urar taga tayi tare da kwanciya akan katifar, wani murmushi ne ya suɓuce mata bayan ta gama haɗa wasu abubuwa a cikin kwaƙwalwarta, hanyar ɗakinta ta nufa cikin sassarfa.
Tsayawa tayi a tsakiyar dakin tana tunanin ta ina zata fara bincikar cameera din, wardrobe, haka taji tamkar anyi mata raɗa a kunne da sauri ta nufi wajen ta tsaya tare da karema wajen kallo sosai har lokacin da idonta ya hasko mata karamar camera acan saman wardrobe din, murmushi tayi tare da jawo stool ta hau sannan ta ciro camera ɗin. Jujjuyashi tayi a hannunta kafin ta ciro wani ƙaramin box ta saka a ciki, ruwan da ta ɗauko ta zauna tasha kana ta koma ta kwanta.

Washegari bayan tayi sallar asubahi da kanta ta shiga kicin ta haɗa musu abin karyawa saboda tafiyar safe su Jidda zasuyi zuwa Bauchi, ƙarfe bakwai na safiya ta gama shirya komai a dinning kana ta nufi ɗakinta domin yin wanka kasancewar itama zata fita aiki.
Cikin shirinta ta fito ta samesu a falo harda Baaba suna zaune, gaishe da Baaba tayi kana suka gaisa da Sa.Jid.

"Ina kwana Anti." Raliya ta faɗa lokacin da take goge TV stand, sai a lokacin Zarah ta lura da ita, cikin wani ƙayataccen murmushi ta amsa wanda ya saka Raliyan shiga kogin tunani na dalilin yin murmushin nata.

Dinning suka nufa duka harda Baaba da bata cika cin abincin acan ba, Jidda ce tayi serving É—insu duka sannan suka fara cin abincin.

"Yauwa Zara'u, munyi waya da mahaifinku ɗazu yake gayamin Muhammadu zai iso anjima sannan zuwa jibi zai ƙaraso nan ku zanta akan shirye shiryen da zaku gabatar." cewar Baaba.

"Uhmm." shine abinda kawai ta furta bayan ta saka tissue ta goge bakinta.

"Kinyiwa Ubanki badani kikeyi ba, mutum sai shegen miskilanci na tsiya." ta kuma faÉ—a.

Idonta ne ya kawo ruwa ta kalli Baaban da nufin yin magana sai ta rigata.

"Sulaimanu nake nufi." ta kuma faÉ—a tana harararta.

Dariya Jidda tayi kana tace.

"Gaskiya Baaba zanyi missing É—in dramar ku da Sahibaty."

"Mene ne kuma meizu.?" Baaba ta faÉ—a cikin gyatsina.

Wannan karon har Zarah da Saleem saida suka dara sosai.

"Rabo da su Baaba kwanan nan zan kaiki London a koya miki turanci kema." cewar Saleem.

"A'a É—an nan meye haÉ—ina da turanci kuma, ku dai da suka asirce ku sai kuyi ta fama."

"Kunga idan kuka biyewa Baaba to tabbas yau zaku rasa flight, ku hanzarta na sauke ku a airport ɗin nima aiyuka gareni sosai a office." cewar Zarah tana miƙewa.
Suma miƙewa sukayi inda Jidda ta shiga ta fito musu da trolleys ɗinsu.

"Mu zamu wuce Baaba sai munzo biki." Inji Saleem.
"ÆŠan albarka mungode Allah yabar zumunci, ai bikin ma a can Gombe za'ayi muma duk zamu tattara mu biyo bayanku acan za'ayi komai."

"Toh Allah ya kawo ku lafiya."

"Ameen yaron kirki, a ƙara hakuri dai da juna."

"Idan ma da ni kikeyi ba kulaki zanyi ba kinga tafiyata." cewar Jidda.

Har gurin mota ta rakasu tana musu addu'ar sauka lafiya har saida taga sun fice a gidan kana ta juya ta koma falo.

Basu daÉ—e da isa airport É—in ba jirginsu ya tashi bayan sunyi sallama cike da kewar juna da zasuyi, zuciyarta gabaÉ—aya babu daÉ—i ta nufi office É—inta. Bata ko yi minti biyu da zama a kujerarta ba Bala ya shigo bayan ya nemi izini, ganin yanayin da take ciki yasa ya ajiye takardun daya shigo dasu ya fice, takardun da ya ajiye ta jawo tare da fara nazartarsu, bayanai ne kan wani da suke zargin yana safarar miyagun kwayoyi wanda zai shigo garin Bauchi nan da kwana biyu, inda ta wannan hanyar suke fatan tabbar da zarginsu tare da kamashi muddin zarginsu ya tabbata.
Tsaki taja mai sauti bayan tayj tunanin hanyar da ita kaɗai ce mafita a garesu batare da sunsha wahala ba, da kanta take so tayi wannan aikin gudun kada a samu matsala musamman yadda yawancin jami'ai yanzu zuciyarsu ta gurɓace da son kuɗi, saidai kuma batason aikin dazai dinga kaita hotel ko kaɗan amma babu yadda ta iya dole wannan karon tayi wannan aikin da kanta.
Gabaɗaya wuninta na yau a office tayi shi ne cikin tsara yadda aikin zai kasance cikin sauƙi batare da sunsha wahala ba, sai ƙarfe shida tabar office ɗin bayan ta zaɓi team ɗin da zasuyi aikin tare.
Bata tsaya doguwar hira da Baaba ba yau saboda a gajiye take, hakan yasa bayan sunci abincin dare ta wuce É—akinta ta kwanta.

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

"Momi zamu wuce." cewar Abdallah da suka fito a sashin M.J cikin shirinsu na tafiya garin Bauchi ganin amarya Zarah, sunyi kyau cikin dakakkiyar farar shadda da suka saka iri ɗaya sai zuba ƙamshi sukeyi musamman M.J da ya fito a asalin ango mai shirin amarcewa da sabuwar amarya.

"Yauwa ƴaƴan kirki ga wannan ku kaiwa ƴar tawa, ku gaishemin da Mamana kuma." cewar Momi dake zaune tana miƙawa Abdallah wata ƙaramar jaka.

"Me amaryar mu ta samu ne haka Momi." ya faɗa yana ƙoƙarin buɗe jakar.
Hannunshi ta buge kana tace.
"Ban yarda a buÉ—e ba, ku bata shi yadda na baku."

"Toh Momi mun wuce."

"Allah ya kiyaye hanya ku gaishesu."

M.J ke jan motar yayinda Abdallah ke gefenshi yana zuba surutu, tun yana kulashi har ya gaji ya daina wanda hakan yasa shima Abdallah ya maida hankalinashi kan wayarsa saboda sanin halin miskilanci irin na M. J.
❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄
Cikin shirinta na ƴan sanda ta sauko ƙasa hannunta riƙe da agogo tana ƙoƙarin ɗaurawa, yayinda take ɗauke da wata jakar baya madaidaiciya mai matuƙar kyau da sheƙi.

"Zan wuce office Baaba." ta faɗa bayan ta zauna a hannun kujera tana ƙarasa ɗaura agogon.

"Yanzu Zara'u mijin da zaki aura zaizo ganinki amma bazaki haƙura da zuwa aikin nan ba yau."

"Aiki mai mahimmanci zan gabatar Baaba sannan bazai wani É—aukeni dogon lokaci ba idan ya iso ki kirani sai na dawo, sannan Raliya ta shirya musu abinda ya dace."

"Shikenan Allah ya bada sa'a ya kuma kare."

"Ameen Baabata nagode sosai." ta faÉ—a tana ficewa a falon.

Kai tsaye office ta nufa, bata wani ɓata lokaci sosai ba suka wuce hotel ɗin da zasuyi aikin acan bayan ta canja kaya zuwa doguwar rigar abaya sannan tayi rolling da gyalen rigar.
Mintuna kaÉ—an suka isa, can nesa da gate É—in sukayi parking, mintuna kaÉ—an sai ga wata tsadaddiyar mota ta shiga hotel É—in.

"Jeka Bala ka tabbatar kayi kyadda ya dace." Zarah ta faÉ—a.

"Toh ranki ya daÉ—e." Ya faÉ—a yana mai fita a motar, tabbas idan bakasan shi ba baza kayi tunanin jami'in tsaro bane saboda kalar shigar da yayi ta Æ´an iska, kai tsaye farfajiyar hotel É—in ya shiga tare da nufar inda motar tayi parking.
Glass ɗin motar ya ƙwanƙwansa, sauke gilashin baya akayi inda wani hamshaƙin mutum ke zaune.
"Lafiya kuwa É—an saurayi." cewar Alhajin.

Waige-waige Bala tayi kamar mara gaskiya kafin ya fara magana irinta Æ´an shaye-shaye yace
"Alhaji naga kamar kazo hutawa ne shiyasa nace bari nayi maka tayin zafafa ko zasu tayaka hutawa."

"Shigo daga ciki." ya faɗa bayan ya buɗewa Bala ƙofar.

"Banason idanun mutane shiyasa nace ka shigo daga ciki, yimin bayani sosai."

"Ya Alhaj akwaisu dayawa fa amma yanzu É—ayace ta rage, sunanta end of discussion saboda zazzafa ce sosai." cewar Bala tamkar me maye.

"Kada kasani asarar kuɗi fa ka kawomin ƙazama kamar ka." ya faɗa yana gyatsina saboda kayan jikin Bala sun matuƙar yagalgale.

"Ina fada maka ya Alhaj, zafafa nake dasu bari na nuna maka hotonta." ya ciro wayarsa a aljihun wandon jikinshi, hoton da Zarah ta É—auka É—azu ya nuna mishi wanda take sanye da doguwar riga.
Laɓɓansa ya lasa bayan yaga hoton kasancewar sa manemin mata yasa babu ɓata lokaci ya fito da rafar kuɗi na dubu-dubu ya ajiye guda biyu a cinyar Bala tare da faɗin.
"Kirata yanzu tazo."
Sowa Bala yayi tare da danna kiran wayar Zarah yana faÉ—in.

"End of discussion harka ta tashi maza kizo yau kakarmu ta yanke saka."

Katse wayar yayi yace.
"Yanzu zaka ganta yanzu ya Alhaj."
BuÉ—e kofar motar akayi inda direban Alhajin ya shigo tare da faÉ—in.

"Na gama komai yallaɓai ga key ɗin ɗakin nan room 234 a sama."

"Ohk" kawai yace tare da karɓan key ɗin.
Chapter 13 · 0% Book details