Sashe 19
Asp Zarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ayya bari na haɗo saƙon Momi naje muyi sallama, suna ina ne."
"Suna can falon baƙi."
"Ina zuwa."
Ta faÉ—a tana haurawa sama da gudu, É—akinta ta shiga tare da nufar inda ta ajiye jakar tsaraba data tanadar musu da wacce takeso a kaiwa Momi, rufuwar jakunkunan ta gyara sannan ta É—aukosu ta fito falon, kallon Baaba tayi tace.
"Dan Allah Baaba Raliya ta kaiwa Yayana fresh milk karya fito yaga ban kai mishi ba."
"ÆŠaukomin ni na kai mishi."
"Yauwa" ajiye kayan tayi akan kujera sannan ta nufi kitchen ta ɗauko fresh milk ɗin da cup ta miƙa mata, kayan ta ɗauka ta nufi falon baƙin ita kuma Baaba ta miƙe ta nufi ɗakin Sadiq ɗin.
"Ahh Baaba da kanki kuma, ita little ɗin me takeyi da bazata iya kawomin ta koma ba.?" cewar Sadiq dake ƙoƙarin fitowa daga bedroom sanye da farar jallabiya.
"Bakaji daÉ—i bane da ni na kawo."
"A'a kawai naga kamar ba aikinki bane."
"Sai kuma kayi idan bazaka sha bane na maida, ita wacce kake magana tana gurin mijin da zata aura zasuyi sallama domin zai koma inda ya fito."
"Yi haƙuri Baaba, dama Bro ɗin yau zasu wuce shine basu faɗan ba."
"Gashi ni na faÉ—a maka ai."
"Ehh to nima inaga yakamata naje muyi sallama ko."
"Yakamata gaskiya."
"Bari naje na dawo sai muyi hirar soyayya."
Dariya tayi kawai shi kuma ya fice a É—akin.
Ƙoƙarin riƙe handle ɗin yake domin shiga falon saidai maganganun dake tasowa yasa ya jinkirta domin jin cigaban zancen, muryar M.J ya kuma ji yana faɗin.
"Idan kinsan da kuÉ—in karuwanci kika siyama uwata waÉ—annan tarkacen ki tattara kayanki ki koma dasu domin rashin arzikina bai kai matakin da zan iya barin uwata tayi amfani da abin haram ba."
"M.J wai meke damunka ne akan yarinyar nan, wai ko mantawa kake itace wacce ake ƙoƙarin ɗaura muku aure nan da satikai uku masu zuwa.?"cewar Abdallah.
"Abdallah kenan ina sane da duk abinda nakeyi, wannan da kake magana akanta bana mata wanj kallo da ya zarce na mazinaciya, karuwa, sannan kuma fasiƙa mai aikata abinda Allah ya haramtashi, bana mata kallon matar da nake shirin aura domin bata cancanci a alaƙanta ta dani ba bare kuma aje batun aure, ina mata kallo ne na wacce ake ƙoƙarin kawomin domin na horata akan abinda da ta daɗe tana aikatawa." sannan ke kuma, ya waiwaya ga Zarah dake zaune zuciyarta na barazanar faso ƙirjinta ta fito saboda baƙin cikin daya turnuƙeta
"Ina ƙara jan kunnenki tare da baki shawara da ki zubar da duk wasu mugun nufinki nason cigaba da bin maza a gidana domin bazan lamunci hakan ba, a cikin gidana dana gina da tsarkakkun kuɗi bana haram ba a dinga aikata saɓon Allah a ciki, mazinaciyar banza mazinaciyar wofi, wa ya sani ma ko a gada kikayi kika tsotso a no..."
Tasss!!! Ta katseshi ta hanyar baiwa fuskarshi wadataccen mari zazzafa domin zuwa yanzu bazata iya jure cin mutuncin nasa daya bar kanta ya koma kan iyayanta da basa duniyar ba ma.
Baki buɗe suke kallonta, a ɓangaren Abdallah tsantsar farin ciki da mamakin abinda Zarah tayi ne ya hanashi magana, shikuwa M.J baƙin ciki da mamakine suka turnuƙeshi lokaci guda.
"Ni kika É—aga hannu kika mara.?" Ya faÉ—a yana huci.
"Na mare ka kuma in gab da yi maka abinda yafi mari zafi matuƙar zaka taɓa mutuncin iyayena, banza kaw..."
Bata ƙarasa ba itama ya wanke mata fuskarta da mari kafin ta kuma ankara ya ƙara wanke mata ɗaya ɓarin da mari mai zafi, saidai ko kaɗan Zarah bataji zafin shi a fuska ba saboda zafin zagin iyayenta da yayi yafi komai ƙuna a gareta.
"Kina karuwa har kin isa ki ɗaga wannan hannun naki mai cike da ƙazantar zina ki mare ni, wallahi baki isa ba kuma ƙunci yanzu kika fara shiga cikinsa nonsense."
A hankali ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shigo duk da halin da yake cike bai hanashi yin sallama ba, kai tsaye inda take a durƙushe ya nufa batare da yayi magana ba, hannu biyu yasa ya miƙar ta ita tsaye tare da riƙe hannuwanta suka nufi ƙofar fita daga falon, ɗan tsayawa yayi sannan yace
"Dama sallama nazo yi muku, idan kun tafi Allah ya kiyaye hanya."
Yana gama faɗin haka ya ja hannunta suka fice a falon, daga Abdallah har M.J babu wanda ya tanka, shikam Abdallah baƙin ciki yakeji na abinda abokin nasa ya aikata tare da dana sanin wannan rakiya da yayi, a ɓangaren M.J kuwa babu wani abu da yakeji a ranshi face ɓacin ran da Zarah ta sakamai ta hanyar marinshi.
Miƙewa Abdallah yayi tare da ɗaukar kayan da Zarah ta ajiye mai ya fita batare daya kula M.J ɗin ba, bayanshi ya bi ganin bai kulashi ba suka fita tare, sun rigada sun sanar da direban dazai kaisu airport ya shirya dan haka bayan motar suka shiga yajasu zuwa airport ɗin.
Ko da suka isa basu yima juna magana ba har zuwa lokacin da suka shiga jirgi ya keta hazo dasu.
Kuka take me matuƙar ban tausayi da sosa ran duk wani mai sauraro har suka isa ɗakinta, kan gadon ɗakin ta faɗa tana cigaba dayin kukan, shikuwa Sadiq nufar inda hoton mahaifansu dake gefe yayi ya ɗauka tare da rungume hoton a ƙirjinshi, sai a lokacin kukan daya danne ya hanashi fitowa yayi nasarar bayyana kanshi batare dayayi ƙoƙarin dakatarwa ba shima ya fara kukan yana faɗin
"Meyasa zai rabamu daku, me muka mishi zai rabamu daku ya barmu cikin gararin rayuwa da rashin gata, Abba! Mami kuna ganin yadda rayuwarmu ta tagayyara da bakwa tare damu, Abba meyasa bakace mutuwar ta ɗaukeni ba ta barka ka kula da ƙannena, Abba inajin kamar na gaza riƙe amanar ƴan'uwana da kullum kake daɗa jaddadamin, Mami kina gani koh? Ki tayani roƙon Allah yayi gaggawar ɗaukan raina bazan iya jure ganin ƴan'uwa cikin halin baƙin ciki da ƙunci ba alhalin ina raye. Kaicona dana kasa riƙe amanarka Abbana yau ga ƴar'uwata tana zubda hawayen baƙin ciki dana maraici sannan ina kusa na kasa aikata komai, Ya Allah kayi gaggawar ɗaukan ra...."
Hannu aka saka tare da rufe mishi bakinshi, bashi da ƙarfin dazai iya hana hakan shiyasa ya cigaba da rera kukan shima mai ban tausayi.
Zama Baaba tayi a gefen gadon ta É—ora hannun hagunta a bayan Zarah tana bubbugawa alamun rarrashi hannunta na dama kuma na kan Sadiq tana shafawa a hankali.
Sun É—auki tsawon mintuna a haka batare da sun daina kukan ba, ganin haka yasa Baaba tace.
"Idan rai ya ɓaci ambaton Allah akeyi ba kuka ba."
"Baaba na gaji bazan iya jure wannan baƙin cikin ba, na gaji ta dalilinsu fa muka shiga wannan halin amma abinda zasu saka mana dashi kenan, bazan iya jure wannan cin mutuncin da akeyiwa iyayena ba zan maida musu da Diamonds ɗinsu ko zamu huta da wannan takaicin." Zarah ta faɗa cikin fitar hayyaci, da sauri ta miƙe ta nufi gaban dressing mirro ɗinta tana watsi da duk wasu abubuwa dake kai batare da ta kula da irin ɓarnar da takeyi ba. Sai da zuba komai na kan wajan a ƙasa kafin da fara ƙoƙari tura dressing mirro ɗin gefe.
"Me kike ƙoƙarin aikata ne haka Fatimah?" Baaba ta faɗa a fusace.
"Bazan iya ba Baaba zan basu Diamonds ɗinsu kawai na huta." ta ƙarasa fada lokacin da tayi nasarar tura dressing mirror ɗin gefe, tsugunnawa tayi a gaban wani tiles a wajen, hannu takai da nufin taɓawa sai dai kamar a danna mata remote ta dakata saboda jin kamar anayi mata raɗa a kunne.
"Raliya!!! Batula Raliya na waje." haka taji a kunnenta tamkar wani ke magana, da hanzari da nufi ƙofar fita bata ko ganin gabanta saboda tsananin tashin hankali, da mugun ƙarfi ta buɗe ƙofar.
Rasss! Rasss!! Rassss!!! Haka ƙirjin Raliya ya bada sauti wacce ke tsaye a jikin ƙofar riƙe da sound recorder da kuma ƙaramar camera tana ɗauka duk wani abu dake faruwa ta ɗan ramin ƙofar data buɗe kaɗan ganin mutanen ɗakin basa cikin hayyacinsu bare su lura da ita, tsananin tashin hankali da firgici ne ya ziyarceta lokaci guda ta fara ɗika saboda zufar da tayiwa jikinta ƙawanya lokaci ƙanƙani..
Wata irin shaÆ™a Zarah takai mata........âœï¸
😱😱😱😱😱😱😱
*YANZU NE FA ZA'A FARA ASALIN LABARIN _ASP ZARAH_👩â€âœˆï¸ MATAR MUHAMMAD JAWWAD KAWAR JIDDAH MATAR SALEEM. LOKACIN DA ZAMUGA ÆOYAYYEN SIRRIN DAKE TATTARE DA JIDDAH YAYI FA🤔*
*SHIN ZARAH ZATA MAIDAWA DADDY DIAMONDS ÆŠINSA KO KUWA ZATA BARSHI A WAJENTA HAR SAI ZUWA LOKACIN DA ZATA KAUDA ALPHA.???*
*ME ZAI FARU TSAKANIN ZARAH DA RALIYA NE A WANNAN FITO NA FITO DA SUKAYI.???*
*WANI MATAKI DADDY ZAIYI NE IDAN YAJI LABARIN ABINDA ƊANSHI YAKE AIKATAWA GA YARINYAR DATA SADAUKAR DA KOMAI NATA DOMIN KARE DUKIYARSA WACCE TA DALILIN HAKANE TA RASA IYAYANTA SANNAN ƳAR'UWARTA TA FICE A HAYYACINTA.???*
*AURAN MUHAMMAD JAWWAD DA FATIMAH ZARAH NA YIWUWA KUWA.???*
*SHIN ALPHA YANA SAMUN NASARAR MALLAKAR WAƊANNAN LU'U LU'U MASU MATUƘAR DARAJA.???*
*YA BATUN RAHAMA A CAIRO. INA MUSTAPHA KUMA???.*
*SHIN TANA SAMUN NASARAR KAMA ALPHA KAMAR YADDA TASHA ALWASHI.???*
*MEZAI FARU NE IDAN M.J YA GANE IRIN SADAUKARWAR DA ZARAH TAYI AKAN DUKIYAR MAHAIFINSHI.???*
*INA BATUN ALMAJIRAR DA ZARAH TA TAÆA HAÆŠUWA DA ITA NE.???*
_DUK AMSOSHIN TAMBAYOYIN DAMA WASU NA TARE DA JASMINE🌸🌸 A CIKIN LITTAFIN ASP ZARAH👩â€âœˆï¸, YANZU AKA FARA_.
*BY*
*JASMINE*🌸🌸
*ASP ZARAH*