Sashe 2
Asp Zarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Alhaji Sulaiman, wato É—an'uwan mahaifin Zarah nada tarin dukiya sosai da baisan adadinta ba. Babba kuma sanannen kamfaninshi shine _M.J JEWELS_. Kamfanin ya samu sunan ne daga Muhammad Jawwad wato É—an shi na fari.
Ana sarrafa duk wasu nau'ika na kayan ƙaleƙale a wannan kamfani kama daga kan ƴan kunnaye, sarƙa, awarwaro, zobuna, agogo da sauransu wanda ake sarrafasu daga ma'adanai daban daban danginsu zinari, azurfa, lu'u lu'u da dai sauransu.
A shekarar data gabata ne yasamu nasarar mallakar lu'u lu'u wanda ya siya a hannun turawa da darajarshi takai dallar amurka miliyan talatin, an sakashi a wani akwatin tsaro na musamman wanda babu wani abu dazai iya fasashi koda guduma ne da bindiga dole sai mabuÉ—in shi wanda yake tamkar flash na jikin laptop. Kasancewar sai yayi shekaru da dama a ajiye kafin a iya sarrafashi yasa ya É—aukeshi daga gidanshi inda yake da farko aka maida kamfaninshi saboda hare-haren Æ´an fashi. Inda aka ajiyeshi a wani É—akin sirri dake kamfaninshi, amma duk da hakan ba'a daina barazanar satar shi ba.
Ganin hakan ne yasa shida ɗan'uwan shi Alhaji Abdul_Jalal suka yanke shawarar maida shi gidansa dake bauchi bayan an damƙa tsaronshi a hannun Zarah.
Hatta iyayen basuda masaniyar a inda lu'u lu'un da akwatin tsaronsa suke tun bayan da aka damƙa mata ajiyarshi.
*ALPHA*👽
Alpha wani taƙadirin ɗan ta'adda ne dayayi ƙaurin suna a Nigeria dama maƙotanta, ya shahara sosai wajen sace-sace da fashi gami da kisan kai. Saidai abinda yake matuƙar damun al'umma shine babu wanda ya sanshi bare inda yake zaune domin yanada yara da dama masu yimasa aiki saidai hatta wasu daga cikin masu yimai aiki basu sanshi ba.
A duk lokacin da suka yi wani gagarumin laifi suna barin tambarinsu wanda yake sunan ALPHA ne haÉ—i da zanen bishiyar kwakwaðŸï¸, ta hakane ake ganewa idan sun aikata laifi saidai har yanzu Æ´an sanda sun kasa kama koda É—aya ne daga cikin masu yimasa aiki sakamakon manyan gwamnati da suke tare dashi.
Tun bayan daya samu labarin wannan lu'u lu'u daga bakin wani yaronshi na sirri wanda yake aiki a _M.J JEWELS_. Yasha alwashin sace shi saidai matakan tsaron dake jikin akwatin ne ya hanashi samun damar satarshi amma yana kan shiri wajen ganin ya mallaki wannan kadara tare da É—aiÉ—aita kamfanin _M.J JEWELS_.
Bayan ya samu labarin inda aka maida lu'u lu'un sai yafara kiran Alhaji Abdul_Jalal tare da yimasa barazanar kashe wani nasa muddin bai sanya Zarah ta damƙa mishi akwatin da lu'u lu'un ke ciki ba, ganin bai samu nasara ba sai ya maida akalar barazanar shi ga Zarah ganin ita mace ce saidai yayi mamakin taurin kai irin nata domin akoda yaushe idan ya kira musayar maganganu marasa daɗi ne yake wakana a tsakaninsu duk da barazanar dayake mata na rasa wani daga cikin danginta.
Dalilin dayasa ya yanke shawarar taɓa wani a cikin danginta ko zata saduda.
_____________________________
Ciwon ciki mai tsanani ne yake damun Rahma wanda yayi sanadin harta kwanta a gadon asibiti, satinta biyu aka sallamota bayan jikinta yayi sauƙi sosai.
Kasancewar lokaci ne na hutu yasa Ammi dake ƙasar Cairo ta yanke shawarar zuwa duba jikin Rahman tare da samarin ƴan biyunta, a garin Gombe jirginsu ya sauka hakan yasa dole suka ƙarasa garin Deba domin kwana washegari sai su wuce Bauchi.
Bayan gaishe-gaishe da hirar yaushe gamo ne suma tsoffin suka yanke shawarar ayi tafiyar dasu domin suma dai basuje dubata ba tunda tayi rashin lafiyar, nan suka yanke cewa zasuyi sammako gabaɗaya suje domin a ranar tsoffin sukeson suje su dawo saidai tafiyar bazata yiwu da Baba Faɗimatu ba sakamakon ciwon ƙafa da take fama dashi.
Da daddare Momi matar Alhaji Sulaiman ta kira Ammi tayi mata ban gajiya inda ta roƙeta akan tabar tata tafiyar sai jibi domin su tafi tare saboda gobe zataje ganin likitan ido akan matsalar ido da take fama dashi. Nan Ammi ta yanke shawarar barin tafiyar sai jibi kamar yadda ta buƙata wanda hakan zai bata daman zama da Baba Faɗimatu da za'a bari a gida ita kaɗai a ranar.
Washegari kuwa kamar yadda suka tsara ƙarfe takwas suka ɗauki hanyar zuwa gari Bauchi bayan sun tsaya a cikin garin Gombe sun ɗauki Nusaiba a gidan Alhaji Sulaiman wacce itama za'ayi tafiyar tare da ita, Shahid ne ke tuƙa motar Adil na gefenshi yayinda Malam Usmanu, Malam Adamu, Baba Aisha da Nusaiba ke baya. A haka suke tafiya lokaci zuwa lokaci suna ɗan taɓa hira.
Safiyar yau bayan Zarah tayi shirinta na tafiya aiki kamar koda yaushe akan kayan aikinta ta ɗaura Abaya sannan tayi rolling da mayafinta, fara ce kuma kyakkawa ce ajin ƙarshe daga kyawun fuska har na jiki, tana da tsayi amma ba sosai ba. Kyakkyawar fuskarta na ɗauke da dara-daran idanu wanda suke cike da gashin gira dana ido, dogon kuma matsakacin hanci ta da kuma ƙaramin bakinta suke ƙara bayyana kyawun da take tattare dashi.
Kai tsaye falon Abbansu ta nufa, a zaune ta same su shida Maminsu alamun magana suke mai mahimmanci, bayan ta gaishesu ne ta sanar dasu zata wuce gurin aiki. Abban ne ya dakatar da ita daga shirin miƙewa da take sa'an nan yace "Zarah inaso na ƙara jaddada miki cewa duk rintsi kada ki maidawa Daddyn ku Sulaiman ajiyarshi kowani hali kika tsinci kanki ciki matuƙar bashi ya buƙaci ajiyarsa ba."
"Toh Abbah insha Allahu zanyi yadda kace." Ta faÉ—a cike da ladabi
"Allah ya muku albarka gabaɗayan ku ya ƙara haɗe kanku ko bayan bama nan."
"Ameen Abbah."
Daganan ta miƙe ta musu sallama tare da barin falon hakan takejin wani irin yanayi a tare da ita.
Bayan fitarta ne Alhaji Abdul_Jalal ya kalli matarshi yace" Ina tsoron abinda taƙadirin nan zai aikata ga yarinyar."
"Babu abinda zai sameta da yardar Allah."
"Ameen dai amma wannan mutumi abun tsorone."
Haka suka cigaba da tattaunawa game da lamarin Alpha É—in har zuwa wani lokaci.
Ƙarfe sha biyu a cikin Gombe tayi musu kai tsaye suka nufi Gwallaga Inda anan gidansu Zarah yake.
Cike da farin cikin ganin juna aka tarɓesu sannan aka cika musu gaba da abubuwan motsa baki. Hira aka cigaba dayi har zuwa lokacin sallar azahar Inda mazan suka wuce masallaci matan ma suka miƙe domin gabatar da tasu.
Bayan anyi sallah ne kuma aka zauna cin abincin gargajiyar da Mami ta shirya, cike da barkwancin da kakannin keyiwa jikokin nasu.
Haka suka kasance cikin farin ciki har zuwa lokacin da sukayi haramar tafiya.
Baba Lado mai gadi na zaune akan wani benci dake jikin gate yaji anyi horn, koda ya leƙa bai gane na cikin motar ba sai ya tsaya batare daya buɗe gate ɗin ba, wani ne ya fito daga cikin motar sanye da manyan kaya ya iso jikin ƙofar inda Baba Lado ke tsaye.
"Baba dan Allah me gidan yana ciki kuwa.? "
Kafin ya samu damar amsawa yaji an rufe mishi fuska da wani abu, tun daga lokacin bai kuma fahimtar komai ba.
Mutumin da kanshi ya buÉ—e gate É—in motar tazo ta shige sannan ya kulle.
"Bari naje bayi na dawo Inna sai na baki saƙon da zaki kaiwa kishiyar tawa." Faɗin Rahmah dake ƙoƙarin shiga banɗakin dake can gefe a cikin falon.
Dariya sukayi gabaÉ—aya domin dai Rahma akwai barkwanci dason ganin duk wanda ke tare da ita cikin farin ciki.
Shigewar Rahma keda wuya aka buɗe ƙofar falon, inda wasu mutane dake sanye da baƙaƙen kaya fuska rufe suka shigo. Adadin su bakwai ne sannan kowanne a cikinsu na riƙe da bindiga.
"Kada wanda ya motsa ko ya mana hargowa."
Babu wanda ya motsa a ciki saidai Idan mutum ya lura da bakinsu zai gane addu'o'i sukeyi.
Babbansu ne ya bada umarnin a É—auresu gabaÉ—aya tare da kulle musu sannan a bincika sauran É—akunan ko akwai wani a ciki, dukkan sashe na gidan suka duba amma ba suga kowa ba.
Kasancewar sai an ɗaga labule Kafin aga ƙofar banɗakin da Rahma ke ciki yasa sam basuyi tunanin akwai wata ƙofa a falon ba sakamakon labulayen da suke a jere har gaba da ƙofar bayin, Idan ba ɗan gidan bama babu wanda zai san akwai banɗaki a wurin.
Waya wani ya ciro tare da karawa a kunne.
"Shugaba rayuka takwas ne cikin gidan a yanzu."
Jim akayi daga É—aya bangaren kafin akayi magana.
"Su faÉ—a muku Inda akwatin yake da mabuÉ—insa idan kuma sunyi taurin kai to ku tabbatar babu wanda ya rayu cikin takwas É—in.".....
Bayan ya kashe wayar ne ya juyo tare da maida hankalinshi inda suke, umarni ya bada aka buÉ—e ma Abba bakin shi dake É—aure.
"Alhaji inaso ka faɗamin inda akwatin da lu'u lu'un ke ciki da kuma mabuɗinsa, ba tashin hankali ya kawo mu ba ku bamu abinda mukeso mu tafi batare da cutar da wani ba." Ya ƙarasa faɗa yana mai saka bindiga a goshin Abban.
Motsa jiki da Malam Usmanu keyi ne ya hana Abba magana ganin Ogan nasu ya nufi wajenshi tare da kunce masa É—aurin dake bakinsa.
"Abdul_Jalalu a matsayina na mahaifinka ban yarda ka faɗamusu idan ajiyar da ɗan'uwanka Sulaimanu ya baka ba, idan kayi hakan kuma bazan taɓa yafe maka ba ko bayan raina." Faɗar Malam Usmanu bayan an kunce masa ƙullin dake bakinsa.
"Ba muzo nan domin jin musayar kalaman da zakuyi ba, zaka faɗa mana ne ko bazaka faɗa ba.?" Ya maida akalar tambayar shi ga Abba bayan ya ƙara ɗaure ma Malam Usmanu bakinsa.
"Bazan iya faÉ—i inda yake ba." Abban yafaÉ—a
"Shikenan bazamu ɓata lokaci ba zamuyi abinda ya dace."