← Book details Asp Zarah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 21

Sashe 5

Asp Zarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da Ameen sika amsa gabaɗaya kafin kowa ya miƙe domin zuwa kwanciyar bacci wanda a zahiri ba haka bane domin raba dare suke gaban mahalicci suna kai mishi kukansu.

Washegari tun ƙarfe bakwai Zarah ta fito cikin shirinta sanye da kakinsu na ƴan sanda, baƙin wando da shuɗiyar riga, inda ta ɗora baƙar Abaya mai ratsin shuɗi a saman kayan sannan tayi rolling da gelen rigar.

Ammi kaɗai ta tarar zaune a falo tana jan carbi, ƙarasawa tayi tare da zaunawa a ƙasan kujerar da Ammin ke zaune.

"Barka da safiya Ammi."

Kanta Ammin ta kwantar akan cinyarta tare da shafawa a hankali.

"Ina fatan kintashi lafiya.?"

"Lafiya lau Ammi, zan wuce aiki ina barar addu'a." cewar Zarah lokacin da take gyara kanta a cinyar Ammin.

"Allah ya kareki daga dukkan sharrin masu sharri, Allah ya nesanta zuciyarki da aikata abinda ba daidai ba, Ina roƙon Allah ya baki nasara ga duk abinda kikasa a gaba. Allah ya albarkaci rayuwarki."

Cike da jindaɗin addu'o'in Ammin take amsawa da Ameen kafin ta miƙe tare da mata sallama ta nufi hanyar fita daga cikin falon.

Gurin motarta da yaran Mustapha suka wanke mata ta nufa domin masu yi musu aiki tun bayan faruwar wannan lamarin suka aje aiki saboda tsoron kada a ƙara kawo wani harin a haɗa dasu tunda na farko dai hodar saka bacci aka shaƙa musu basusanai zai iya faruwa ba nan gaba.

Cikin mintuna ƙalilan ta isa ofishin nasu, tun kafin ta ƙarasa parking sergent Bala ya iso inda motar take ya buɗe mata ƙofa bayan ta gyara tsayuwar motar.
Ƙamewa yayi har saida ta fito sannan ya kulle motar.

"Ranki ya daɗe barka da safiya. Ya ƙarin haƙurin mu."

"Barka dai Bala, haƙuri mungode Allah." ta faɗa tana mai fara tafiya domin isa ofishinta.

Karbar jakarta yayi bayan yace" Allah ya gafarta musu."

"Ameen." tace a taƙaice.

Haka ƙananun jami'an suka jigaba da mata gaisuwa harta ƙarasa cikin ofishin ta.

Tana ƙoƙarin ajiye wayarta akan tebirinta kira ya shigo, ganin mai kiran ne yasata sakin wani kyakkyawan murmushi.

"Assalamu alaiki ya habibaty." abinda aka faÉ—a kenan bayan ta kara wayar a kunnenta

"Wa'alaiki salam Dr. Jiddah amaryar Bar. Saleem." Zarah ta faÉ—a tanamai zama a kujerarta

''Ki faÉ—awa wanda bai sani ba, naga alama tsokanar da bakiyi kwana biyu ba kikeson yi kuma ba kulaki zanyi ba. Dafatan kin tashi lafiya yasu Ammi."

"Lafiya lau suke duka."

"Ya ƙarin haƙuri kuma."

"Alhamdulillah."

"Allah ya musu Rahama."

"Ameen Ameen. Ina kika baro maƙalematan naki banji motsinsa ba." Zarah ta faɗa cike da barkwanci.

"Ke dai bari habibaty, jiya kwana nayi ina mishi kukan nagaji da zama a cikin masu jajayen kunnuwa shine yau ba shiri ya fita domin fara haÉ—a tarkacensa." Jidda kenan take maganar cikin sanyi murya.

"Babu kyau abinda kike aikatawa fa, ki dinga damun bawan Allah yana miki abinda kikeso koda shi bayaso É—in."

"Auren kenan ai kema kiyi kigani ko baza'a miki abinda kikeso ba."

Kafin tayi magana aka kwankwasa ƙofar ofishin nata da haka tace.

"Zamuyi magana anjima SA.JID zan fara aiki a ofis."

"Innalillahi! Yanzu Zarah tun ba'a sadakar bakwai bama har kin fara fita wannan ƙaddararren aikin, so kike ki jama kanki zance a gari."

Shiru Zarah tayi na wani lokaci kafin tace" Jiddah ya zanyi to, *Alpha* kinsani Idan ban kasance a ofis ba na wani lokaci mutane da dama zasu rasa abubuwa masu mahimmanci sanadin wannan mutumin."

"Shikenan Allah ya taimaka, nima dai Insha Allah zuwa wani watan zamu dawo." Jiddah ta taÉ—a cike da tausayin Zarah.
Sallama sukayi sannan suka katse kiran lokaci guda.

Umarni ta bada a shigo lokacin da take ajiye wayar a kan teburinta.

Sergent Bala ne ya kuma shigowa hannunshi É—auke da farar takarda, saida ya sara mata kafin ya fara magana.

"Ranki ya daɗe wannan saƙo ne daga ofishin mai girma kwamishina, jiya da yamma ya aiko tare da bada umarnin lallai akai miki saboda abune mai mahimmanci. Dama yau nakeson kawo miki idan na tashi a aiki sai kuma gaki kinzo."

KaÉ—a kai Zarah tayi kafin tace" Sau sa dama Bala ina gayamaka ka koyi saka maganganu a cikin kalma É—aya, basai kayita dogon sharhi ba a matsayinka na É—an sanda. Anaso maganar jami'i ta banbanta dana sauran mutane, anfiso idan kayi magana sai mutane sunyi nazari sosai kafin su gane ainahin abinda kake nufi ba kamar yadda kake magana yanzu ba."

Ƙamewa ya kuma yi kafin yace.

"Ayimin afuwa ranki ya daÉ—e zan gyara."

Bata kula da maganarshi ba tace.

"Me takardar ta ƙunsa."

"Ranki ya daÉ—e bani da damar buÉ—ewa saboda a kulle take cikin envelop."

Hannu tasa ta karɓi takardar tare da buɗe envelop ɗin ta cirota.
Mintuna biyu ta ɓata wajen nazartar abinda ke cikinta.

ÆŠagowa tayi daga kallon takardar tare da maida kallonta ga Sergent Bala sa'an nan tace.

"Taron ƙarawa juna sani a harkar aiki ne ake umartana naje wanda za'a gudanar a garin Abuja. Cikin sati ɗaya za'a gama gudanar da taron wanda zai fara ranar alhamis, sannan kaida Jennifer ne zamu kasance tare."

Bata jira mai zaice ba ta bashi umarnin tafiya.

Jingina kanta tayi da jikin kujerar sannan ta lumshe idanuwa.

Haka ta wuni a ofishin sam takasa taɓuka komai bayan kuma da shirin yin aiki ta fito saidai ta danganta hakan da saƙon kwamishina daya risketa.

Cikin kwana ukun ta kammala duk wasu shirye shiryen ta na tafiyar.

A gefe guda kuma su Ammi na shirye shiryen tarban Muhammad Jawwad da shima zai iso ƙasar ranar Alhamis wanda rabonshi da ita tun yana ɗan shekara 14.

Jirgin ƙarfe tara Zarah zatabi zuwa garin Abuja yayinda jirginsu Muhammad Jawwad zai sauka ƙarfe takwas da rabi.

"Daddy ina jin ku wuce kawai zanbj ta ofishin kwamishina kafin mu wuce." Zarah kenan ke faÉ—i bayan ta gama amsa wayar da Sergent Bala ya bugo mata.

"Babu rabon zaku haɗu da ɗan'uwan naki kenan saboda shima kwanaki biyar zaiyi ya koma saboda inaso ya dawo ƙasarshi ya cigaba da aiki." cewar Daddy

"Banji daɗin haka ba gaskiya amma tunda zai dawo ƙasar gabaɗaya zamu ga juna."

"Shikenan Allah ya kiyaye hanya."

"Ameen Daddy."

Sauran iyayenata ma addu'ar sauka lafiya suka mata kafin ta shige motarta ta fice a gidan.

Daddy, Momi da Ammi sune sukaje airport tarbar É—an nasu domin Baaba batada damar fita saboda halin takaba da take ciki.

Basu jima da isa ba jirgin ya sauka, dubawa suke domin ganin ta inda zai ɓullo amma basu ganshi ba.
Wani kyakkyawan bature ne suka ga ya nufo inda suke tsaye, basu ankara ba suga ya rungume Daddy tare da faÉ—in" Nayi kewarka Daddyna."

Salati Ammi ta shiga rafkawa tana faÉ—in.

"Jawwad kaine haka.? Shikenan masu jajayen kunnuwa sun canja ka, ka koma jinsinsu."

Dariya sukayi gabaÉ—aya sannan suka nufi gurin da motarsu take, ita kuwa Momi kunyar fulani da kawaicin É—an fari ne ya hanata magana.
Mota suka shiga tare da nufar gida.

A ɓangaren Zarah kuwa koda kwamishina ya gama zayyana mata tsarin yadda taron zai kasance saita miƙe domin tafiya, har ta kama hannun ƙofar da nufin buɗewa ta fasa tare da waiwayowa ta kalli kwamishinan da hankalin shi ya koma kan takardun dake saman teburinsa tace.

"Yallaɓai nace ba."

Kallonta yayi batare da yace komai ba.

Murmushi tayi mai cike da ma'anoni kafin tace.

"Yallaɓai idan ba damuwa ka faɗawa wanda ya baka umarnin wakiltani a matsayin wacce zata halarci wannan taron cewa _Babu ma'ajiyar CCTV a ofishin ASP Zarah sannan baya buƙatar na'ura mai ɗaukan sauti domin sanin abubuwan da nake gudanarwa a cikin ofishina._

Bata jira mai zaice ba ta buɗe ƙofar tare da ficewa a ofishin........ ✍🏼

*Jasmine*🌸🌸

*TALLA*! *TALLA*!! *TALLA*

*Uwargida!!! Shin ko kinsan zaki iya magance matsalolin da suka daÉ—e suna ci miki tuwo a kwarya cikin gidan aurenki.???*
*Uhmm riƙe sirri sai mai sirri, shin kinada labarin shahararriyar matar nan wacce ta shahara wajen ganin cewa mata basu wulaƙanta a gidan mazajensu ba.!? Wacce ta kware wajen gyara amarya har ma da uwargida.? Ita ɗin dai dake siyar da kayan gyara na musamman masu sauƙin kuɗi amma akwai aiki, mai kawo muku sirrika da dabarun gamsar da miji ta kowani fanni.*😍

*Kardai na cika uwar gida da surutu, nice dai HAJIYA JAMILA SHARE KUKAN MATA. A wannan karon nazo ne da zafafan darussa da zan gabatarwa mata tare da kayan gyara na musamman. Bari dai na lasa muku zuma a baki, kaÉ—an daga cikin darussan da zan gabatar a wannan karon:*

*Sirrin TomTom*
_Shidai tom tom da kika sani uwargida, matsalar ki ta wajen kasa gamsar da mai gida ta ƙarw idan kika riƙe wannan sirri._

*Zuba ki lashe*

_Bazance komai ba a wannan fannin idan kinason sani to ki kasance tareda ni a cikin sati ukun dazan gabatar da darussa_.

*Kayan gyara na musamman zai iso ki har garin da kike idan kinyi odarsu, domin sanin kalar su da amfaninsu to ki kasance dani cikin zazzafan darussa na sati uku da zan gabatar a Special Group na ASP ZARAH FANS.*

*Kada ki bari ƙaramin kuɗi ya saki zama mara gata gidan mijinki.*

*Ki tuntuɓi wannan number 07048961623 domin samun damar shiga ASP ZARAH SPECIAL FANS GROUP, Inda ni HAJIYA JAMILA SHARE KUKAN MATA zan kasance daku.*
*Kada ki bari Æ´ar uwarki ta baki labari*.
*SAI KUNZO*

Ya kasa koda motsa yatsa ne saboda kaÉ—uwa da yayi da zancenta, yanzu kam ya fara zargin ko Zarah tana da aljanu masu faÉ—a matan idan anyi maganarta.
Kiran wayar sirri sukayi da Alpha lokacin da yake shaida mishi ya tura Zarah garin Abuja domin halarta taron ƙarin ilimi a fannin aiki, hatta da wayar da yayi amfani da ita tana killace a ɗakin barcinshi na gida.
Duk tunanin dayayi bai samar mishi da amsar inda Zarah taji labarin za'a sanya CCTV a ofishinta ba, yanke shawara yayi na kiran Alpha domin shaida mishi abinda ya faru.

Saida ya kira sau biyu kafin aka É—aga kiran.

Cike da jimami kwamishina ya karanto mishi abinda ya faru a ofishin nashi kusan mintuna goma da suka wuce.

"Ya akayi tasan da batun CCTV.?" Alpha ya faÉ—a cike da masifa

"Kayi haƙuri Alpha nima bansan ina ta samu labarin ba." Ya faɗa kai a sunkuye tamkar yana gabanshi.
Chapter 5 · 0% Book details