← Book details Asp Zarah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 21

Sashe 16

Asp Zarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dake saurayin irin masu surutun nan ne bai tsaya wani dogon nazari ba ya fara labarta mishi abinda ya faru awanni uku da suka wuce, na yadda Zarah ta jagoranci jami'i sukayi basaja suka kama mutumin da babu wanda zaiyi zaton mai laifi ne, ya daɗe yana zayyano mishi kyawawan halinta tun daga kan shiga har fannin aiki, ganin saurayin bashi sa niyar dakatawa ne yasa Abdallah miƙewa tare da ajiye musu rafar kuɗi akan teburin da suke zaune ya wuce sama.
Murmushi yayi mai cike da ma'anoni, tabbas bazai gayawa M.J wani abu da ya sani akan Zarah ba, zai barshi har zuwa lokacin da zai gano da kanshi, a wannan lokacin zai taya Zarah ramuwar abinda ya mata amma duk da haka yana fatan ya saduda da wuri kafin dare yamai nisa.

Ko da ya kuma É—akin bai nuna mishi wata alama dazai gane yana cikin wani yanayi akan abinda ya faru ba, hirarsu suka cigaba dayi har zuwa lokacin da aka kira sallar magrib suka fito masallacin dake farfajiyar hotel É—in domin sauke farali.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Duk yadda taso taƙi saka abin a ranta ta kasa, kusan kwana tayi a zaune tana tunanin mafita babu shawarar da zuciyarta bata raya mata ba daga mai kyau har wanda bai dace ba, daga ƙarshe dai ta yanke shawarar ɗaukar lamarin a duk yadda yazo mata, zata karɓi tayin kowane irin zama da yakeso suyi, damuwarta ɗaya ce kuma ya magance mata wato cigaba da aikinta, bata da wani sauran abinda zata damu dashi matuƙar zai yarje mata cigaba da aiki.
Washe gari idonta yayi luhu-luhu saboda rashin baccin da bata samu ba ga kuma kuka da tayi sosai, hakan ya haddasa mata ciwon kai mai tsanani har taji bazata iya fita gurin aiki ba, tana kwance akan sallayar da tayi sallar asuba ta kasa miƙewa ta koma kan gadon.

Ganin har ƙarfe takwas Zarah bata sauko ba yasa Baaba miƙewa da kanta ta haura saman domin duba lafiyarta, da sallama ta shigo saidai duhun dake ɗakin bai barta ta hangi komai ba, lalubawa tayi har Allah ya bata sa'ar samun switch ɗin ta kunna haske ya gauraye ɗakin, kalle-kalle ta farayi ganin bata ganta kan gadon ba har Allah yasa ta hangota acan kusurwar da take sallah. Da hanzari ta ƙarasa inda take tare da tattaɓa jikinta ganinta a duƙunƙune.

"Subhanallahi Zara'u baki da lafiya shine baki faɗa ba tuntuni a kaiki asibiti, saiko zauna da ciwo a jikinki haba sai kace ƙaramar yarinya."

Cike da juriya da ƙarfin hali tayi ƙoƙarin miƙewa zaune tare da jingina bayanta a jikin gado tace.

"Ba wani abu ke damuna ba fa Baaba, kawai ɗan ciwon kai ne daya haddasa min zazzaɓi amma yanzu zanyi wanka nasha magani."

"A'a Zara'u ban yarda da wannan ba ki lallaɓa kiyi wankan sai a rakaki asibiti, ko kuma zaki jira su Muhammadu suzo ne saisu kaiki naga kamar zaifi."

"Baaba nace miki karki damu ba wani abu bane fa zansha PCM yanxu zai sauka."

"Tunda haka kikace ai shikenan Allah ya baki lafiya, dama naga baki sauko bane nazo faÉ—amiki cewa É—azu Babanku ya kirani wai sun fasa bari sai wani sati saboda Sadiku ya matsa sai sun dawo shine yau zasu biyo jirgin yamma su dawo."

Wanj irin zabura tayi kamar ba mai jinya ba tace.
"Da gaske Baaba.?"

"Mtsww! Iskancin banza, ni ina nan na ɗaga hankali na baki da lafiya ashe ƙarya kike yi tunda har zaki iya wannan zaburar."

"A'a fa Baaba, kinsan daÉ—ewar da nayi banga É—anuwana ba dole nayi É—oki yanzu da naji zai dawo."

"Shikenan ai kiyi wanka kizo ki karya saiki sha maganin."

"Toh yanzu zan sauko."

"Karma ki sauko yanzu inkin so." Ta faÉ—a tana mai ficewa daga É—akin.

Miƙewa tayi dakyar saboda sarawa da kanta keyi ta shige banɗaki, ruwa mai ɗumi ta tara ta shiga ciki, ta daɗe a kwance cikin ruwan kafin ta canja shi ta tare wani kana ta ɗauki sponge ta fara murzawa jikinta a hankali har ta gama ta ɗaureye jikinta kana ta fito a ruwan ta ɗaura towel tare da ficewa a banɗakin.
Zama tayi gaban dressing mirro tana ƙarewa kanta kallo ganin yadda damuwar dare ɗaya ke neman ramar da ita, ya zama dole tayiwa kanta alƙawarin cire duk wani damuwa dake ranta akan wannan auren ta maida hankalinta wajen binciken inda zata nemo _Alpha_ domin zuwa yanzu tanajin wani irin kwarin gwiwa akan binciken da take a kanshi, tana iya gudanar da komai batare da tsoro ko shakkar wani abu zai faru da ita, hakan na ƙara bata tabbacin cewa lallai ta kusa tozarta Alpha a idon duniya. Abu ɗaya yanzu takeson sani shine haƙiƙanin inda yake rayuwa, zata iya riskar kowani haɗari matuƙar zata gano inda yake, hanya ɗaya gareta yanzu, hanya ɗaya tak! Wato Raliya. Ta hanyar Raliya ne kawai zata iya gano inda Alpha yake, dole tasan yadda zatayi ta samu duk wasu bayanai a gurin Raliyar.

Tunanin damuwar Alpha da tayi ne ya mantar da ita badakalar auren dake gabanta, mayukanta ta shafa tare da wadata duk wata gaɓa na jikinta da turare, gaban wardrobe taje ta tsaya tare da kallon tulin kayanta dake ciki, idonta ne yakai kan kayan sports ɗinta dake can gefe a ninke, zaro su tayi tare da ƙura musu ido tana tuna lokacin baya da kowace ranar lahadi sai sunyi wasanni kala-kala da yayarta Rahama saboda haka ma Abba ya saka aka ƙawata musu wani sashi na cikin garden dinsu da kayan wasanni, wasu lokutan ma hatta Abban yakan kasance tare dasu domin shima yana matuƙar son wasan Table Tennis. Wasu marayun hawaye ne suka zubu daga idonta, hannu tasa ta share tare da yiwa iyayen nata addu'ar samun Rahamar ubangiji, kayan ta mayar ma'ajiyarsu kana ta ciro wata material kalar blue da golden, ɗinkin riga da skirt ne wanda ya matuƙar karɓan jikinta.
Wayarta kawai ta É—aukan sannan ta fice a É—akin.
"Ya jikin dai" Baaba ta tambaya bayan saukowarta cikin falon.

"Da sauƙi." ta faɗa a hankali.

"Allah ya ƙara afuwa, ga kalaci akan dinning idan kin gama saiki sha magani."

"Toh" ta faɗa tare da miƙewa ta nufi dinning ɗin da Raliya ke gurin tana ƙara ƴan goge-goge, kujera ta jamata ta zauna tare da cewa.
"Ina kwan Anty."

"Lafiya" ta amsa a taƙaice kana ta kuma cewa.
"Jeki kawai." ganin Raliyan na ƙoƙarin zuba mata abincin.
Tea kawai tasha sha sai dankali da ta ɗan tsakura, sannan ta miƙe ta koma cikin falon ta kwanta a doguwar kujera, tana daga kwance take ƙarewa Raliya dake zirga-zirga kallo, tabbas akwai abinda take ɓoyewa domin tun zuwanta gidan bata taɓa ganinta babu hijabi ba kullum cikin saka hijabai take kowani irin aiki da takeyi ko yanayi da ake ciki. Toh mene ne Raliyan bataso a gani??? Ta tambayi kanta, shiru tayu na wasu mintuna kafin ta saki wani murmushi mai sauti wanda har saida ya jawo hankalin Raliyan dake moping, tabbas ta samu amsa.
Lallai akwai tatto É—in Alpha a wuyanta wanda batason a gani shiyasa ko da yaushe take cikin hijabai.
Wayarta da tayi ringing ne ya katse mata tunanin da takeyi, da murmushi a fuskarta ta É—aga tare da karawa a kunnenta.

"Amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida." Jidda ta faɗa daga ɗaya ɓangaren.

"Dama nasan idan bake ba babu mai kirana da sanyin safiyar nan."

"Saboda baki da aurene yasa kike ganin yanzu yayi safiya, toh yakike ya angon namu? Kun gana dai koh?"

"Yanzu wace tambaya zan fara amsa miki maganaÉ—isu."

"Duka nake buƙatar sani."

"Alright to duka lafiya lau."

"Hmm to ya angon kun sasanta dai koh."

Shiru tayi batare da tace komai ba, hakan yasa Jidda cewa.
"Wato É—an iskan maganganu yazo ya faÉ—a miki koh? Kuma shine kika zuba mishi ido batare da kin É—au mataki ba, wai ke wace irin mace ce habibaty."

Batayi mamakin jin abinda ya fito a bakin Jiddan ba domin idan da sabo ta saba da wannan halin nata, sau da dama ko bata faɗa mata abu Jidda na iya fahimtar hakan a yanayinta, da fari tayi tunanin ko Jidda nada aljanu akanta ne masu gayamata sai daga baya ta gano nature ɗinta ne hakan da kuma tsantsar ƙaunar da takeyi mata shiyasa take iya karantar ko wani yanayi nata, ƙwafa tayi kana tace.
"Toh madam mai gani har hanji ya kikeso nayi idan ba shirun ba."

"Wato abinda ya faru kenan dai, ke kuma saboda gaki mai biyayya kika zura ido kina kallonshi yana gasa miki maganganu, toh wallahi ki kiyayeni tun kafin nakai maƙura na shiga lamarin da bai shafeni ba."

"Kiyi hakuri Mama" Zarah ta faÉ—a cike da zolaya.

"Toh na haƙura ƴar nan, yanzu ya ake ciki wasu event zamu shirya ne naga alaman idan aka biyewa ra'ayinki bazamu gwangwaje."

Dariya tayi sosai kana tace.
"Kinsan nifa ustaziya ce."

"Matar uztazu koh, shikenan ma bazan kuma yi miki magana ba zanjira Ammi su shigo next week sai mu tsara komai da Sis Rahama."

Miƙewa tayi zaune daga kwancen da take tace
"Wace Ammi."

"Ammi nawa muke dasu dama.?"

"Wato saboda anjireni a cikin dangi yasa duk wanda zaizo kasar ba'a faÉ—amin koh".

"Ke kika sani nikam na tafi gurin habibi na."
Kafin ta kuma magana kashe wayar, miƙewa tayi da nufin zuwa ɗaki sai....✍️

*VIP ayimin haƙuri dan Allah jiya banji daɗi ba shiyasa banyi typing ɗin ba. Sorry dan Allah*👏

*ASP ZARAH*👩‍✈️

Shigowarsu ce ta dakatar da ita daga ƙoƙarin miƙewa da take domin zuwa ɗakinta, sallamar da Abdallah keyi ta amsa ɗauke da murmushi a fuskarta.
Bakj M.J ya kyaɓe lokacin daya zauna a kujera tare da faɗin
"Mutum a fuska kamar na Allah saidai a baɗini ɓarnar da ake aikatawa ko kare bazai shinshina ba, Allah dai ya shirya wanda ya mayar da kanshi kwarkwar."

"Ameen kuma gani kuturwar uwa zama dani dole." ta faÉ—a cike da basarwa kamar ba ita tayi zancen ba.
Chapter 16 · 0% Book details