Sashe 20
Asp Zarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wata irin shaƙa Zarah takai mata saidai cikin zafin nama ta kauce tare da hankaɗa Zarah ta faɗi ƙasa sannan ta nufi hanyar matattakalar da zai sadata ƙasa, ganinta tayi a gabanta tamkar wacce aka jefo kafin ta ankare taji saukar duka ta ko ina a jikinta ta yadda babu ta inda zata iya kare kanta, dukanta takeyi sosai tamkar wacce ta kama ɓarawo a bayan kanta.
"Baki da hankali ne Zara'u me tayi miki kike dukanta? Ki sake ta tun kafin raina ya ɓaci." Baaba kenan ke faɗi bayan ta fito taga abinda ke faruwa, shikuwa Sadiq yana gefe a tsaye bai tanka ba domin yasan hakan nan Zarah baza ta yiwa Raliya wannan dukan ba idan ba wani mumminan laifi ta kamata dashi ba.
Saida taga ta daina motsi kafin ta sassauta duk kuwa da hargowar da Baaba keyi mata akan ta rabu da ita, hannu ta saka ta fincike hijabin dake jikin Raliyan saidai ga mamakinta ba hijabi ɗaya bane a jikinta, saida ta cire hijabai uku kafin tayi tozali da jikinta kai tsaye hannu ta saka ta juyata daga kwancen da take kamar gawa ta duba gefen wuyanta, kamar yadda tayi tsammani kuwa zanen tatto ne a gefen wuyan nata, bishiyar kwakwa ne da sunan Alpha da aka ƙayata ta hanyar zanen, ɗaki ta shiga ta ɗauko wayarta ta ɗauki hoton gurin kana ta danna kiran waya tana karawa a kunnenta.
"Kuzo da mota biyu gidan mu." shine kawai abinda ta faÉ—a kafin ta juya ga Baaba wacce ke sharar kwalla tana sambatu.
Hannunta ta riƙo suka koma cikin ɗakin ta zaunar da ita a gefen gadon itama ta zauna tare da karɓar ruwan da Yayanta ke miƙa mata tasha sannan ta maida kofin yaƙara tsiyayawa ta miƙa ma Baaba itama.
"Shikenan kin ja mana zagi a gari Zara'u za'ace mun kasa riƙe waɗanda ke ƙarƙashin mu."
"Baaba tun ranar da kika gayamin kin É—auki yarinyar nan aiki na nunq miki banso ba, haka ne."
"Eh sai me dan bakiso ba ai ni inaso, shiyasa kike neman ki mata lahani tana marainiya."
"Wai ke waya gaya miki wannan yarinyar marainiya ce Baaba? Spy ce fa aka turo mana a matsayin mai aiki."
"Mene ne haka.?"
"Ƴar leƙen asiri mana, Alpha ne fa ya turota.?
Wani zabura duka su biyun sukayi a tare suka kuma haÉ—a baki wajen faÉ—in
"Alpha.???"
"Kwarai kuwa."
"Kin tabbata little.?"
"Sosai na daÉ—e da tabbatar da haka banaso na kamata a bisa zargi ne shiyasa amma da ta daÉ—e da zama a kurkuku, zo muje É—akinta ka gani."
Miƙewa sukayi duka suka nufi ɗakin Raliyan, sosai Baaba tasha mamakin abubuwan da Zarah ta nuna musu a ɗakin wanda babu ko tantama duk wanda yaga wannan yasan akwai abinda ake ƙullawa.
"Tabbas ɗan adam na da wuyar fahimta, ki duba kiga yadda yarinyar nan ta ɓadda kama ta zo min a maraice tana roƙon abata aiki ashe cutar mu tazo tayi, Allah ya toni asirinta. Allah sarki Zara'u shiyasa sam baki yadda ko gurin zama ku haɗa ashe kinsan abinda kika gani, ni kuma duk da haka ban fahimci komai ba."
"Gaba saiki kiyaye kisan waɗanda zaki dinga zaɓa kuyi mu'amala tare..." Ringing ɗin wayarta ne ya hanata kai aya a zancen nata.
"Ehh ku shigo falo" haka kawai ta faÉ—a ta kashe wayar.
"Jami'ai sun iso muje."
"Ina za'a kaita ne little."
"Za'a cigaba da tsaronta har zuwa lokacin da za'a kama maigidan nasu a yanke musu hukunci."
"Kina ganin hakan bazai janyo wata matsalar ba."
"Babu abinda zai faru Yayana da izinin Allah."
"Toh Allah yasa."
"Amin " suka haÉ—a baki wajen faÉ—a ita da Baaba, sannan suka bar É—akin zuwa falo inda jami'an suke.
"Ku tafi da ita Nura a fara kaita asibiti a duba lafiyarta daganan sai a wuce da ita station a rufe ta, ban yarda ko waye yazo a fito da ita ba, sannan duk wanda yazo belinta indai ba jami'i bane to a haÉ—a dashi a rufe, kuna jin abinda na faÉ—a koh."
"Zamu kiyaye ranki ya daÉ—e."
"Joy da Halima ku É—auketa ku kaita mota sai ku wuce."
Sara mata sukayi duka sannan sukayi kamar yadda tace suka fita a falon.
"Allah ya kyauta ya daÉ—a karemu daga kaidin wannan mutumin."
"Amin thumma Amin.'' cewarsu duka.
"Yauwa Baaba sai batun auren Little da M.J gaskiya za'a janye ba za'ayi wannan auren ba."
"Akan wani dalili za'a janye batun auren? Toh indai akan abinda Muhammadu yakeyi ne wannan auran babu fashi sai anyi shi, watarana ko kuÉ—i aka bashi yayi wannan abun bazai iya ba."
"Amma fa kinajin irin alwashin da yake É—auka akanta muddin ta amince akayi auran."
"Naji tun ba yau ba nasan duk abubuwan da yake faÉ—a game da ita wanda nasan ba haka bane amma inaso mu tura mishi aniyarsa ayi auran. Duk abubuwan da suke faruwa fa bai sani ba na tabbata ranar dazai san wani abu a game da abinda takeyi zaiyi nadamar komai daya aikata a gare ta, dan haka aure nan da sati biyu babu fashi."
"Shikenan Allah yasa haka shine mafi alkhari."
"Amin ai addu'ar daya kamata kayi kenan Allah ya zaɓa mata abinda yake shine alkhairi a wannan auren."
"Uhmm! Little me kuka shirya game da events ne."
"Babu abinda zamuyi Yaya."
"Bai kamata ba gaskiya, ko sports daya ai zamuyi."
"Hakane fa Bro kuma kamar kasan mun daÉ—e bama yin sport wallahi."
"Eh nasan Sis Rahama zataso hakan sosai."
Murmushi kawai tayi mai kama dana ciwo domin duk sanda za'ayi maganar sports sai ta tuna mahaifanta.
"Wani wasa kika zaɓa."
"Dear inajin volley ball zaifi tunda kaga harda mata a ciki."
"Hakane amma gidan Daddy akwai pitch ne."
"Ehh mana ai saboda mu yasa akayi sports garden tun waccen lokacin idan mukaje muna playing dasu brother Adil da Nusaiba..." sai kuma hawaye shar ya biyo bayan maganarta ta.
"Bana sonki da yawan kukan nan fa little, addu'a kawai zamu cigaba dayi musu, ko kinaso ki haifi yara a rasa gane wacece uwar idan kuna kuka dukanku."
Hannayenta ta saka ta rufe fuska tana faÉ—in.
"Kai Yaya."
"Ehh mana, tashi muje kitchen mu haÉ—a dinner kafin Daddy ya dawo."
"Ohh kasan na manta da Daddy na gidan nan, ina yaje ne."
"Ya fita yun É—azu zai haÉ—u da wani abokin kasuwancinsa."
"Nagode wa Allah da bayanan wannan abu ya faru."
"Muje kitchen É—in."
"Yaya akwai abinci fa."
"Ni dai muje muyi ko ma mene ne, da kwaɗayi na dawo ƙasar."
Hanyar kitchen ɗin suka nufa suna hira kamar wasu ƙawaye.
''Allah ya shirya ku."
"Amin" Zarah ta faÉ—a daga kitchen É—in...âœï¸
*Ayimin uzuri da wannan pls banjin daÉ—i ne, ayi haÆ™uri.*ðŸ‘ðŸ‘ðŸ‘ðŸ‘
*Jasmine*🌸🌸
*ASP ZARAH*
_Duk abinda aka sama lokaci..._
Kamar yadda yau ta kasance saura kwanaki biyu kacal a ɗaura auran Zarah da angonta M.J, baƙi na nesa da na kusa duk sun hallara, inda Ammi da Momi suka dage wajen gyara Zarah sosai tamkar wacce zata auri shugaban ƙasa. Babu wasu events da akayi sai sports day da sukayi sai kuma walima da za'ayi bayan ɗaura aure.
Suna zaune su uku a wani keɓaɓɓen guri a cikin garden ɗin gidan Daddy, Sadiq ne a tsakiya sai Zarah da Rahama da suke a gefensa kowaccensu ta ɗaura kanta a kafaɗarsa, kallo ɗaya zakayi musu duka ka tabbatar da cewa suna cikin damuwa sosai, idan ko mutum yasa da mutuwar mahaifansu toh tabbas za'ace maraici ne ke damunsu. Sadiq ne yayi gyaran murya yace.
"Sis kinji abinda ke shirin faruwa da little fa kuma Baaba ta hana a dakatar da bikin nan, ni banaso taje tana shiga damuwa ne kinsanta da rauni."
Rahama wacce tun bayan abinda ya faru ta zama miskila ta wucin gadi, shiru tayi na mintoci kafin tace.
"Dakatar da auren bashi ne mafita ba Yaya, mu bari muga idan anyi auren yana cutar da ita sai mu nemi mafita."
"Bakomai amma indai ya cutar da ita sai na bi mata haƙƙinta ko da kuwa igiyar zumuncin dake tsakanin mu zata tsinke."
"Haka ma bazata faru ba."
"Toh Allah yasa, little tashi kije Daddy na nemanki tun É—azu mantawa nayi ban gaya miki ba."
Cikin sanyin jiki Zarah ta miƙe tana faɗin
"Ku jira ni fa yanzu zan dawo."
"Mu ma yanzu zamu shigo gidan."
"Toh sai kunzo".
Kai tsaye falon Daddy ta nufa inda yake zaune shi kaɗai da alama ita yake jira, gaishe shi tayi sannan ta zauna a gefe, bansan me suka tattauna ba sai dai daga ƙarshe muryar Daddyn naji yana ta godiya tare da samata albarka.
"Daddy ka daina bani kunya ta hanyar gode min, idan kana hakan sai naga kamar baka É—auke ni a matsayin Æ´arka bane."
"Har abada zaki cigaba da kasancewa Æ´ata, amma kinsani cewa godiya wajibi ne ga wanda aka kyautatawa, Allah ya miki albarka ya baki zaman lafiya a É—akin aurenki."
"Amin Daddy."
"Babu wani abu da kike buƙata ko."
"Babu komai."
"Tashi ki kuma cikin Æ´an uwa da iyayenki."
Cikin rashin kuzari ta miƙe tare da ficewa a falon, wata hanya ƙarama tabi sai gata ta ɓullo a wani babban falo wanda aka wadata da kayan alatu na more rayuwa tamkar ɗakin shugaban ƙasa, Jidda kaɗai ta gani a falon tana duba wasu takardu, zama tayi a gefenta tace.
"Ya naga gidan yayi shiru haka."
"Ehh duk suna backyard wajen gyaran naman nan, saboda Momi tace kar a barwa Æ´an aiki aikin zasu lalata shi."
"Ok nima daga falon Daddy nake."
Kallonta Jidda tayi na wasu sakanni kafin tace
"Ina fata komai ya zama steady."
"Ehh babu wata matsala yanzu."
"Wa kun haÉ—u da angon kuwa.?"
"Uhmm tun ranar daya bar Bauchi ba mu ƙara haɗuwa ba, Abdallah ne ke jigilar zuwa da kuma kira."
"Sai kinyi haƙuri da lamarin angon nan naki idan ba haka ba zai ɓata mana shirin mu."
"Dole zan kula domin nima jikina yana bani cewa na kusa kama Alpha da hannuna."
"Nima inajin hakan, ya batun Raliya kuwa."
"Na saka an ɓoyeta a wani keɓaɓɓan guri sai ranar da burina ya cika zan fito da ita."
"Hakan yayi kyau, ya kukayi da oganki ne da kikaje neman transfer."