← Book details Asp Zarah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 21

Sashe 17

Asp Zarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Amaryarmu ni dai yunwa nakeji ki rabu da wannan angon naki ki ceto rayuwata."
Taƙaitacciyar dariya tayi har kyawawan haƙoranta suka bayyana sannan dimple ɗinta ya lotsa, ta gefen ido ya kalleta cikin rashin sanin dalilin dazai saka yaji haushin fara'ar da takeyi ma Abdallah.
Kallo ya bita dashi lokacin data miƙe har ta shige kicin, tsaki ya kuma ja sannan ya kalli Abdallah yace
"Akan wani dalili zaka dinga sake mata fuska haka.?"

Dariya yayi harda buga ƙafa kana yace.
"Ikon Allah! Tunda baza kayi mata fara'a ba ai saika bar masu yimata koh bawai ka dinga jin haushin mu ba."
Bai kulashi ba sai miƙewa da yayi ya nufi ɗakin Baaba, shima miƙewa yayi tare da bin bayan shi domin zuwa gaida Baabar.
Ganin basa cikin falon yasa ta shirya musu komai a dinning, ɗakinta ta kuma ta ɗau mayafi da makullin mota ta fita domin zuwa kasuwa tayi cefanen abubuwan da zata buƙata na girkin tarbar ɗan uwanta da kuma mahaifinta. Yayanta nason masa sosai shiyasa zata fita da kanta ta siyo sauran abubuwan buƙata na miya da basu dashi.
Tare suka fito falon da Baaba inda suka nufi dinning table yin breakfast.
"Bari na kirata ta zuba muku, Zara'u" cewar Baaba, Raliya ce ta taho da sauri ta iso gabansu tare da cewa
"Hajiya Baaba bari na zuba musu, Anty Zarah ta fita."
"Ina taje kuma."
"Wallahi bata faÉ—amin ba amma kaman ba nisa tayi ba, naga batayi shiri ba."
"Ai shikenan zuba musu, amma zata fita shine bazata sanar da ni ba."

Ranshi ne yaji ya ɓaci saboda mummunan zaton da shaiɗan ke kitsima mishi na cewar gurin wani ta tafi domin suyi lalata, baice komai ba ya cigaba da cin abincinsa batare da ya kula Abdallah dake cewa.
"Ko dai anyi mata kiran gaggawa ne."
"Ina tunanin haka nima, kasan Zara'u da ƙulafucin aiki bataji bata gani idan aka kira ta wannan aikin nasu duk wani abu da takeyi saita ajiye ta tafi."

"Yanayin aikin nasu kenan Baaba sunyi rantsuwar kare haƙƙin mutane."

"Toh Allah dai ya tsare."

"Ameen" Inji Abdallah

Ko da suka gama cin abincin falon suka dawo suka zauna, hira suka cigaba dayi da Baaba wanda yawanci akan dawowar da su Daddy zasuyi ne.
"Gashi shigowar yamma zasuyi kuma mu yau mukeson tafiya saboda aiki."

"A'a ku tsaya mana dai ku gana duk da ma zaku haÉ—u acan amma ya kamata ace kun tsaya an tarbesu da ku."

"Shikenan saidai muma muyi tafiyar jirgin kenan, bari na duba ko za'a samu jirgin dare."

"Mezai hana ku ƙara kwana?."

"Baaba nace miki fa akwai aiki."

"Ku zama na'ura saboda aiki idan kun so."

Dariya M.J yayi yace
"Duk rashin son magana da nakeyi sai kinsa ni."

"Yo me za'ayi da mutum miskili."

"Ba zaki gane bane ai Baaba, babu fa'ida ace mutum ya kasance mai yawan surutu."

"Shiyasa ma aka haÉ—a ka da wacce ta dace dakai gurin rashin son magana."

Bai kuma magana ba illa cigaba da danna wayar shi da yayi, itama Baaba miƙewa tayi ta nufi kitchen.

💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

"Raliya! Raliya!! Raliya!!! sau nawa na kiraki?" ya faÉ—a cikin fusata.

Cikin shessheƙar kuka ta amsa mai da "Sau uku ranka ya daɗe."

"Wai ke wace irin daƙiƙiyar yarinya ce da batasan abinda takeyi ba, duk tsawon lokacin nan da kika ɗauka a cikin wannan gidan aikin me kikeyi da har yanzu kika kasa samo wani gamsasshen bayani .?"

"Kayi haƙuri yallaɓai wallahi ina ƙoƙarin ganin na samu masaniyar inda lu'u lu'un suke."

"Kullum abinda kike faÉ—amin kenan, amma sai yaushe ne zaki kawo min wani bayani mai amfani eye.?"

"Fashi da makami."

"Ke Raliya! Baki da hankali ne, kada ki kuskura ki fara aikata wannan mummunan kuskuren, wannan hanyar ba mai billewa bace. Da mai amfani ce bazamu kai war haka batare da mun mallaki wannan kadarar ba, ko zamu kuma aikata hakan ba nan kusa ba akwai sauran lokaci."

"Amma yallaɓai naji kamar batun aurenta akeyi."

A kishingiɗe yake amma jin wannan batun yasa shi miƙewa batare da yasani ba, cin hargagi yake faɗin.
"Aure! Aure dai? Meyasa baki faɗan hakan tuntuni ba Raliya, sai zuwa yaushe ne ƙwaƙwalwarki zata dinga yin abinda ya kamata ne."

"Kayi haƙur..."

"Hell with this fucking word Raliya! Hakurin me zanyi, abubuwa na shirin lalacemin kice wai nayi hakuri."

"Amma yallaɓai naga wanda zata aura ɗan gida ne shiyasa banyi tunanin komai."

"Wanene wanda zata aura É—in."

"M.J ne."

Wani murmushi yayi mai sauti kana yace.
"Woow! Komai ya kusa zuwar mana da sauƙi, kin tabbata shine wanda zata aura."

"Na tabbata ranka ya daÉ—e yanzu haka ma yana garin Bauchi yazo ganinta."

"Ki tsaya ki saurareni dakyau Raliya, wannan ne lokacin mu na samu ko rashi, a yanzu ne muke da damar yin duk wani abu da muka daɗe muna shiryawa, inaso ki lura sosai da duk wani motsinta daga yau, saboda inada tabbacin cewa nan bada jimawa ba za'a nemi sauyawa diamonds ɗin nan wajen zama, ki sanar dani duk wasu bayanai da zaki samu, zan organising team ɗin da zakuyi aiki tare da zarar angano inda suke kiyi ƙoƙarin samu mana bayanai kawai."

"Zan kula sosai yallaɓai."

"Ohk" kawai ya kuma faÉ—a tare da kashe wayar.

Shiru tayi bayan gama wayar tasu tana tunani, tabbas wannan ita kaɗaice damar da take da ita domin ƙara samun kusanci da Alpha, ya zama dole yanzu ta shirya ɗamarar yin fito na fito da Zarah akan Diamonds ɗin nan, ba damuwarta darajarsu ba ko kuɗin da za'a samu akansu, babban abinda ya dameta shine ta wannan hanyar ne kaɗai Alpha zai dinga ganin ƙimarta har ta samu nasarar cusa soyayyarta a cikin zuciyarsa, saboda sanin yadda yake da babban buri akan Diamonds ɗin.
"Lokaci yayi da zanja ragamar wasan nima." ta faÉ—a cikin wani shu'umin murmushi.

💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫

Gefen hanya ta samu tayi parking motarta saboda kiranta da Jidda keyi a waya, hannu tasa ta É—auki wayar tare da maida kiran daya kuma katsewa.

"Ina kika shiga ne nake kiranki bakya É—agawa."

"Toh shugabar masu ƙorafi tuƙi nakeyi."

"Kin fita aiki ne?."

"Aa cefane naje yi inaso na shiga kitchen da kaina na shiryawa Big Bros abincin."

"Nima ai naso zuwa wallahi Sa.Jid ne ya hanani wai saura kwana nawa ne ma da duk zaku dawo Gomben."

"Saboda ke gaki mai ƙafar yawo ko.?"

"Hmm! Kin cika ni da surutun ku na Æ´an sanda baki barni na faÉ—i dalilin kiran nawa ba."

"Wato surutu ma na cika ki dashi ko.?"

"Baza dai ki barni na faÉ—i abinda zan faÉ—a ba kenan.?"

"Ohh sorry ina jinki."

"Akwai matsala fa"

"Wacce irin matsala kuma."

"Jiya naje gidan Momi take gayamin wai a ɗaya part ɗin nan zaki zauna kafin a ƙarasa muku gyaran gidan da zaku zauna."

"Yanzu ya za'ayi kenan."

"Baki zaki buÉ—e ki gayawa Daddy kin fiso a gyara muku gidan tukun, idan babu hali ma sai a É—aga bikin tunda kinga abu ne mahimmaci zamuyi."

"Haka za'ayi zamuyi maganar."

"Toh shikenan sai anjima ki gaishemin dasu idan sun sauka."

"Ok bye."

Motar ta kunna bayan ta ajiye wayar sannan ta nufi gida kai tsaye, M.J kaÉ—ai ta tarar a falon bayan shigarta ciki da sallama, bata kulashi ba ta nufi hanyar kitchen, juyuwa tayi tare da aika mishi wani sihirtaccen kallon jin abinda yake faÉ—a.
"Allah yasa dai kin wanke najasar tun a waje baki dawo dashi cikin tsarkakken gidan nan ba."
Shigewa tayi batare da tace komai ba, shikuwa tsaki ya furzar mai sauti tare da miƙewa ya bar cikin falon.

A zaune ta tadda Baaba a kitchen ɗin tana yankan ɗanyar kuɓewa, ledojin hannunta ta ajiye tare da faɗin
"Me zakiyi da kuɓewa kuma Baaba.?"

"Babanku ne yace yanaso a mishi shine nafara gyarawa kafin ki dawo, ina kikaje ne.?"

"Kasuwa naje na siyo sauran abubuwan da bamu dashi a kitchen É—in."

"Gashi ki ƙarasa wannan bacci ne yaketa ƙoƙarin kamani tun ɗazu zanje na ɗan kwanta, saiki kira Raliya ta kama miki wasu aiyukan."

"Toh" tace tare da karɓar rubar da kuɓewar ke ciki, ita kuma Baaba ta fice a kitchen ɗin, saida ta gyara komai tare da fitar da duk wani abu da zata buƙata kafin itama ta wuce ɗakinta tayi wanka da sallah kafin ta fara aikin.

Tun ƙarfe biyu ta shiga kitchen ɗin tafara hada-hadar haɗa abincin tarbar baƙin nasu, ita kaɗai takeyin duk wasu aiyuka ba kamar yadda Baaba tace ta nemi taimakon Raliya ba, a dole ne kawai take haƙuri Raliy na kusantar inda take bawai dan tanaso ba, saboda tsanar da takeyiwa Alpha da duk wanda ya dangance shi.
Kasancewarta mai saurin aiki yasa kafin la'asar harta gama haÉ—a komai illa kawai masa É—in da bata soya ba wanda shima rashin tashin da baiyi ba ne ya hanata soyawa. Baaba ce ta kuma shigowa kitchen É—in da sallama tana faÉ—in.
"Yanzu Zara'u da nace ki kira Raliya ta kama miki wannan aikin shine kika ƙi koh.?"
Sai a lokacin Zarah ta lura da Raliya dake bayan Baaba, kau da kai tayi tare da faÉ—in.
"Naga aikin ba mai yawa bane shiyasa."

"Allah ya kyauta wannan halin naki, saka min tuwon nikam idan kin gama."

"Toh kije zan kawo miki."

"Ban yarda ba sakamin na tafi dashi ko kibawa Raliya ta kawomin."

Ba yadda ta iya haka ta saka mata malmalar tuwon guda biyu a plate sannan miya a ƙaramin glass bowl, a wani ƙaramin faranti ta jere mata tare da ɗora mata kwalbar soyayyen man shanu ta miƙawa Raliya farantin suka fice tare.
Saida ta wanke abubuwan da tayi amfani dasu kafin ta nufi É—aki saboda kiran sallar la'asar da akeyi, cikin sauri ta watsa ruwa ta fito bayan shigarta banÉ—akin sannan ta shimfiÉ—a darduma tare da tayar da sallah.
Chapter 17 · 0% Book details