← Book details Asp Zarah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 21

Sashe 12

Asp Zarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kamar ya baki yarda da girkin ba? tsabtar shi ko me.?"

"A'a bansan hanyoyin da aka bi aka sarrafa shi ba ne shiyasa, da ace ina gida ma babu wata Æ´ar aiki da zamu É—auka saidai mu jira har zuwa lokacin da Iya delu zata dawo."

"Ƙyanƙyami ne kawai irin naki amma kina ganin dambun nan ai kinsan an tsabtace shi, nikam banga ƴar aiki da ake magana akanta ba ma."

"Ƙila tana ɗakin da Iya Delu ta zauna. Mu haɗa Jallof ɗin cous-cous kawai nima yunwar nakeji sosai."

Cikin ƙanƙanin lokaci suka haɗa lafiyayyen cous-cous da yaji kayan haɗi da nama, sai lemun citta da fruit salat da suka yi. A faranti suka jere komai, inda Jidda ta ɗauka domin zuwa ta jere a dinning, ita kuwa Zarah fruit salad ta ɗeba a plate ta nufi cikin falon.

Baaba na nan zaune inda ta barta, saɓanin ɗazu da take ita kaɗai yanzu tare suke da wata da bata ga fuskarta ba, remote ta ɗauka tare da canja tasha daga Sunnah TV zuwa TVC News kana ta zauna a kujerar dake fuskantar Raliya dake zaune a ƙasa rakuɓe a jikin kujera.

"Ya zaki canja mana tasha muna kallon wa'azi zuwa tashar arna." FaÉ—in Baaba a hassale.

"Kiyu haƙuri Baaba ta ki daina wannan fushin da ni kinji, labarai kawai zan kalla na tashi."

Sai a wannan lokacin Raliya da tayi nisa a cikin tunani ta lura da shigowar Zarah, kallonta tayi ta ƙasan ido, ai nan dake ta ɗauke kanta daga kanta saboda wani irin kwarjinin Zarah da ta hango.
Cikin dakiya da dauriya tace.

"Ina wuni ranki ya daÉ—e."

Kafeta da ido Zarah tayi tana son gano wani ɓoyayyen abu a tattare da ita.
Ita kuwa Raliya kai ta sunkuyar cikin ruÉ—u tare da tunanin ko Zarah ta gane ta ne.

"Banason haka fa Zara'u kin kafe baiwar Allah da ido tamkar mai laifi a bayan kanta."

"Marabar kaÉ—an ne." cewar Zarah a cikin ranta duk da batada wani tabbaci akan yanayin rashin gaskiya da zuciyarta ke gayamata akan Raliyan.

"Lafiya." ta faɗa a taƙaice tana mai cigaba da cin fruit salad ɗin.

Sunanan a zaune a falon har lokacin da Saleem ya dawo, Baaba ce take tambayar Saleem É—in yadda shari'ar ta kasance, baki ya buÉ—e da nufin labarta mana amma saidai kallon da Zarah ta mishi ne yasa shi cewa.

"Baaba munyi nasara." yafaÉ—a a takaice domin ya gane ma'anar kallon Zarah a gareshi, nufinta karya faÉ—i yadda shari'ar ta kasance.

"Hubby kai muke jira tun ɗazu, mu ƙarasa dinning yunwa mukeji."

Su uku suka miƙe suka nufi dinning ɗin, Jidda ce tayi serving ɗinsu, nan suka fara cin abincin.

Kamar wacce aka tsikara haka ta miƙe da sauri ta nufi ɗakinta batare da ta amsa tambayar da Jidda ke mata ba......

*ASP ZARAH*👩‍✈️

_Paid book._
_Domin samun damar cigaba da karantawa batare da ɗaukarwa kai alhaki ba ki/ka biya N300 kacal na normal group, VIP kuma N500. A tuntuɓeni a 07048961623 domin biya._

*🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*📚🖊️
*M*. *W*. *A*

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

*Free Page*

Haka nan taji tamkar ana umartarta ta zuwa ɗakin, da sallama a bakinta ta shiga duk da tasan babu kowa a cikin ɗakin, maida ƙofar tayi ta rufe kana ta jingina jikinta a jikin ƙofar tana mai ƙarewa yanayin ɗakin, yana nan kamar yadda ta barshi. Gaban durowar kayanta ta isa tare da tsayawa tana kallon gurin, tabbas wani ɓangare na umartarta da bincikar gurin saidai ɗaya ɓangare na hanata ƙoƙarin haka. Ƙarar wayar ta ne ya fargar da ita, kallon fuskar wayar tayi taga Ammi ce mai kiran, saida ta zauna a bakin gadon tukun kafin ta ɗaga wayar.

"Ammi na." ta faÉ—a a hankali..

"Na'am daughter ya kuke."

"Lafiya lau Ammi ya jikin Rahma."

"Alhamdulullahi jiki ya fara samuwa, yanzu tana iya yin magana wasu lokutan amma ba sosai ba."

"Allah ya ƙara lafiya."

"Kin fara gyaran jiki kuwa Zarah." cewar Ammi

Cikin son gane mai take nufi Zarah tace.

"Wani irin gyara jiki kuma Ammi.?"

"Zan saɓa miki fa, kina nufin baki fara amfani da kayan da Momin ku ta turo miki ba." cewar Ammin.

Dafe kai Zarah tayi, sam ta manta batun kayan da Momi ta aiko mata dasu.
Jin shiru ne yasa Ammi cewa.

"Kina nufin haka zakije gidan mijin kamar almajira."

"Ni fa Ammi.."

"Ke fa me, toh wallahi ki fara amfani da kayan nan tun wuri, nima ina nan tafe zuwa wani watan domin mu fara shirye shirye da wuri."

"Toh Ammi, Allah ya kawo lafiya."

"Amin ki gaidamin da Baaba, su Jidda sun wuce Bauchi ne.?"

"A'a sai zuwa jibi tukun, akwai wani case da muka gudanar da Saleem ne shiyasa basu tafi ba."

"Ya batun binciken nan Zarah." Ammi ta tambaya cike da rauni.

"Ammi batun bincike ai babu shi tunda an riga da ansan mai laifin."

"Allah ya saka mana wannan zaluncin da ya aikata mana." cewar Ammi cikin rawar murya.

Sallama Zarah tayi mata gudun kada itama ta fara hawayen kamar yadda take da tabbacin kuka Ammi keson farawa.

Miƙewa tayi ta shiga toilet domin yin wanka, jim kaɗan ta fito ɗaure da ƙaramin towel. A gaban madubi ta tsaya, goge jikinta tayi kana ta murza lotion a jikinta sama-sama, hoda ta shafa a fuskarta kaɗan tare da goga lipbalm.
Cikin sauri ta saka doguwar rigar atamfa tare da yana ƙaramin mayafi akanta, wayarta ta ɗauka tare da nufar falon.
Baaba da Jidda ne ke zaune a kujera, yayinda Raliya take can gefe a rakuɓe.
Zama tayi a kusa da kujerar da Jidda take kana tace.

"Barka da yamma Baab."

Kauda kai tayi daga kallo ta kamar ba da ita take magana ba.

Murmushi mai sauti Zarah tayi sannan tace.

"Har yanzu baki gama fushin bane Baaba ta."

Jidda ce ta fashe da dariya ganin yadda Baaba take yatsina tamkar taga abin ƙazanta.

"Ina ganin mu bar yin alkubus din nan sai gobe ko.? Ta faɗa tana ƙoƙarin maida dariyar dake taso mata, tana sane tayi maganar saboda tasan Baaba na matuƙar son alkubus.

"Haba Æ´aÆ´an albarka, kuyi mana shi da dare, na daÉ—e banci ba nima." cewar Baaba fuska a sake.

Dariya sukayi gabaÉ—aya kana Zarah tace.

"Sa.Jid ki kwaɓa mana a saka shi a rana kafin anjima."

"Mene ne ma'anar wannan sojut É—in da kike kiranta dashi." Inji Baaba.

Dariya Zarah da Jidda keyi sosai har saida Jidda tabar kan kujerar ta dawo ƙasa, tsagaitawa da dariyar tayi tace.

"Ke dai Baaba kowani suna saikin ɓata shi, Sa.Jid fa aka ce ba Sojut ba."

"Mene ne ma'anar hakan.?"

"Yauwa kinga Sa. farkon sunan Saleem ne sai Jid kuma farkon Jidda, shine aka haÉ—a kalmomin biyu ake faÉ—in Sa.Jid."

Taɓe baki Baaba tayi tace.

"Boko dai baiyi muku rana ba."

Miƙewa sukayi su biyun suka nufi hanyar kitchen batare da sun kuma magana ba.

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

Kiran wayar dake shigowa wayarsa ne akai akai ne yayi sanadin tashin shi daga daddaɗan baccin daya ɗauke shi tun bayan da yayi sallar asubahi, hannu ya miƙa tare da jawo wayar dake akan bedsite drawer, tsaki yayi mai sauti bayan yaga sunan wanda yake kiran nashi tare da kara wayar a kunne.

"Dama nasan babu wanda zai dinga yimin irin wannan kiran idan ba kai ba, sarkin naci mai zan maka kake damuna."

Daga ɗaya ɓangaren Abdallah ne yayi dariya kana yace.

"Haba mana M. J kiran arziki na maka fa bana tsiya ba."

"Naji faÉ—i dalilin kiran."

"Yaushe zaka dawo Naija ne mu fara shirye shirye, kasan bamu da wani isasshen lokaci fa."

"Shirye shiryen me kenan."

"Banasan wulaƙanci fa M. J, kana nufin auren naka guda ba zamu gwangwaje ba.?"

"Dalilin kiran naka kenan.?"

"Ehh shi ne dalilin kiran najj yaushe zaka shigo."

"Toh sai anjima, bana da lokacin tattauna magana mara amfani yanzu."

"Zancen auren naka ne babu amfani."

"Sai anjima please." ya faÉ—a yana mai katse kiran.
Tsaki ya kuma yi a karo na ba adadi cike da takaicin wannan auren da za'a yi mishi, duk wasu tsari nashi an rusa mai, babu yadda ya iya dole yayiwa mahaifinsa biyayya amma tabbas yana da shiri sosai akan matar da aka ce za'a haÉ—a shi ta ita.

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

Ƙishin ruwa ne ya damu Zarah wacce ke kwance akan tamfatsetsen gadonta, agogo ta kalla ƙarfe 2:15nd, a hankali ta saukk daga kan gadon tare da zura silifas a ƙafarta ta nufi ƙofar fita daga ɗakin zuwa kitchen domin ɗauko ruwan da yau ta manta bata shigo dashi ba yau, saboda yawan shan ruwan da takeyi duk sanda zata farka da dare.
Gora biyu ta ɗauka bayan ta isa kitchen ɗin tare da apple ɗaya kana ta rufe ƙofar kitchen.

Kamar ance ta waiwaya, haske ta hango a babban falon da Abbansu ke saukar baƙi lokacin da yake raye, cike da mamaki ta nufi hanyar falon domin dai ta tabba ta kashe wutan falon kafin su kwanta bacci.

Abinda ta gani ne ya matuƙar bata mamaki tare da tabbatar mata da duk wani zarginta, Raliya ce....... ✍🏼

_Ku yimin uzuri please, ina shirin rubuta jarabawa ne shiyasa bana samun damar yin long pages. Ur prayers also needed._

By
Jasmine
*ASP ZARAH*

_PAID BOOK_.
_Domin samun damar cigaba da karantawa biya N300 kacal ko kuma N500 na VIP. Tuntuɓi 07048961623 domin biya a saka ki a group._

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*
*M*. *W*. *A*

*Free page*
Chapter 12 · 0% Book details