← Book details Asp Zarah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 21

Sashe 7

Asp Zarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*_Jiddah ƙawace ga Zarah tun zamanin ƙuruciya, tare sukayi makarantar firamari da sakandire inda bayan sun kammala Jidda ta wuce jami'a yayinda itakuma Zarah ta wuce makarantar bada horo na ƴan sanda. Duk wasu sirrika na Zarah Jidda tasansu kamar yadda yake a ɓangaren Zarah itama._
_A shekarar data gabata ne Jiddah tayi aure inda mijin data aura ya kasance Barrister wanda yake aiki a ƙasar Malasia wato Bar. Saleem, dakyar aka rarrashi Jiddah tabi Saleem ƙasar a waccan lokacin bayan tayi iƙirarin ita bazata iya tafiya wata ƙasa batare da Zarah ba, shima dai Saleem ɗin bawai yana ƙaunar aiki a wata ƙasa bane illa dai kawai yanason ƙarasa yarjejeniyar aiki da sukayi da ƙasar. Tun bayan tafiyarsu kuma basuzo gida ba sai wannan karon da suka tattaro gabaɗaya suka dawo ƙasarsu ta gado._"

Sallama tayi da ƙawarta ta tare da yimata godiya sannan ta wuce filin jirgi inda tanan zasubi wani jirgin zuwa Bauchi.

Tana tsaye jirgin ya sauko daga sararin samaniya, bayan wadu mintuna kuma matafiya suka fara fitowa É—aya bayan É—aya, sam bata kula ba sai ji tayi an rungumeta gam tamkar za'a tsaga ta.

"Nayi kewarki sosai sahibaty.''
Jiddah wacce ita ke da alhakin rungumar ta faɗa cike da farin ciki, kana ta saketa tare da ƙamewa ta sara mata kana tace.

"Na gaida ASP da kanta."

Murmushi kawai tayi tare da maida hankalinta ga Saleem dake cewa.

"Zan shigar dake ƙara fa Zarah, ganinki kawai yasa ta mance dani ma gabaɗaya."

Dariya sukayi duka sannan suka nufi gurin da aka tana da domin zaman ma tafiya.
Mintuna kaÉ—an jirgin dazai sadasu da garin Bauchi ya keta hazo.

*England*

Tsaki yaja a karo na ba adadi cike da takaici, tashinsa kenan daga bacci sannan kamar koda yaushe yau ma mafarkinta ya ƙarayi wanda ya haddasa wajabcin wanka ya hau kanshi. Ya rasa dalilin dayasa tun ranar daya ganta kullum dare sai yayi mafarkin yana wani abu da ita wanda hakan ke silar dole idan ya tashi sai yayi wankan tsarki.
Wannan shine dalilin dayasa yake jin wata muguwar tsanarta a cikin ranshi.

Miƙewa yayi tare da shiga banɗaki, bai jima sosai ba ya fito cikin shirinsa na farar riga da baƙin wando.
Wayoyinshi ya ɗauka da niyar ficewa a ɗakin, saidai missed calls din Ammi daya gani a cikin wayar ne yasa shi dakatawa tare da zama a gefen gadonshi yana ƙoƙarin kiranta.

Bugu biyu ta É—auka tana mai sallama, amsawa yayi tare da gaisheta.

"Har yanzu banga wani alert ba fa Jawwad." Ammi ta faÉ—a.

Cikin son gane mai take nufi yace.

"Ammi wani irin alert kuma na mene ne."

"Zan saɓa maka fa, ka maidani sa'ar wasan kace. Ko ba dakai mukayi magana zaka turo kuɗi a fara haɗa lefen ba.?" Ta ƙarasa magana cikin hassala.

Dafe kai yayi saboda tunawa da abinda take nufi, gaba ɗaya ya manta da batun aurenshi da Daddy yace zai haɗa da ƴar marigayi wacce bai ma santa a fuska. Shi a tunanin shi girman kai ne ya hanata zuwa ta gaidashi ko tabari su haɗu lokacin da yaje Nigeria, shiyasa yaji baya ƙaunar yin auren duk da matsalar da yake fama da ita na ƙarfin sha'awa.

"Ayi haƙuri Ammi zan turo insha Allah." Ya faɗa cike da biyayya.

"Toh ina jira kada ka sake na ƙara kiranka akan wannan batun idan ba haka ba kuma ranka ɓaci zaiyi." Ta faɗa gami da kashe wayar.

Dafe kai yayi cikin damuwa, shifa yana da ra'ayin irin matar da yakeson aura, amma gashi yanzu Daddy ya ruguza mai duk wasu tsarin shi.

Miƙewa yayi jiki babu laka ya fita domin yana a farkon sabuwar wata da za'a yakeson komawa gida gaba ɗaya, shi da ƙasar turawa kuma sai ziyara ko hutu ko kuma wani abu mai mahimmanci.

.......................

A bakin gate su Zarah suka tarar da wasu mutane biyu da alama dai miji da mata ne sannan marasa ƙarfi.
Ganin motar ne yasa su miƙewa daga durƙusun da suke a gefen gidan.

Tsayar da motar Saleem yayi kamar yadda Zarah ta buƙata, buɗe ƙofar baya ta fito ta nufi inda suke tsaye.

Da sassafar matar ta ƙaraso tare da durƙusawa akan gwiwoyinta tace.

"Ranki ya daɗe ki taimake mu, kwana uku kenan muna zuwa gidan nan amma anƙi bamu damar shiga. Hatta ofishinku ma an hanamu ganinki dan Allah ranki ya daɗe ki sauraremu."

ÆŠagota Zarah tayi kana tace.

"Kada ki bani kunya ta hanyar durƙusawa a gabana domin neman wata alfarma, hakan zai sa nayi tunanin ko baki ɗaukeni a matsayin ƴa ba. Ku tashi mu shiga daga ciki muyi magana a nutse."

Ta ƙaramar ƙofa suka shige bayan su Saleem sun shige da motar tuni.

Falon saukar baƙi ta kaisu kana taje kicin da kanta ta kawo musu ruwa da lemo.

"Bismillah ga ruwa ku sha sai muyi maganar abinda ke tafe daku."
Fadin Zarah bayan ta aje tiren dake dauke da gorar ruwa da lemu a kan ƙaramin teburin dake tsakiyar falon.

"Ranki ya daÉ—e ba zamu iya shan komai ba ahalin da muke ciki." FaÉ—in mijin

"Meke faruwa ne.?" Zarah ta faÉ—a tana mai zama a kujerar dake fuskantarsu.

"Ranki ya daɗe ƴar mu akayi wa fyaɗe, sannan mun tabbatar da wanda ya aikata laifin. Yaron wani ɗan majalisa ne dake maƙobtaka damu amma bayan mun sami mahaifin yaron da batun ya ƙaryata lamarin tare da faɗin zaiyi shari'a damu duk sanda muka nemi ɓata masa suna ko ɗan shi. Yanzu haka yarinyar na gadon asibiti ana neman kuɗin aiki sannan bamu da halin biya." Ya faɗa yana mai fashewa da kuka inda matar ke taya shi.

Sosai zuciyarta ta tsinke da lamarin musamman da taga manyan mutanen da suka haifeta a shekaru suna zubar da hawaye.

"Amma meyasa baku kai ƙara ofishin ƴan sanda dake kusa ba.?" Zarah ta tambaya a raunane.

"Tun faruwa lamarin muka kai ƙara ofishin ƴan sanda dake kusa damu, saidai bayan sun gana da mahaifin yaron suka fatattake mu tare da faɗin sharri mukeson ƙullawa ɗan sa. Wannan dalilin yasa muka garzaya ofishinki bayan wani maƙocin ya bamu shawarar yin hakan, tun kwanaki uku da suka wuce muke zirya a ofishin an hana mu shiga shine mai gadin wajen ya bamu adireshin ki." Matar ke wannan bayanin.

Kai kawai ta jinjina tare faÉ—in.

"Ina zuwa." kana ta miƙe ta fita.

Bata daÉ—e ba ta shigo tare da Saleem da Jidda, zama sukayi tare da gaisa.

"Wannan shine Bar. Saleem tare da matarsa Dr. Jidda, za muje asibitin tare domin ganin halin da yarinyar take ciki kafin shigar da ƙara a kotu." faɗin Zarah bayan tayi nuni da kujerar da Saleem ke zaune shida Jidda.

Godiya su kayi sosai kana suka miƙe gaba ɗaya suka nufi waje.

Motar Zarah suka shiga duka inda Saleem ke tuƙin.

Mintuna kaÉ—an suka iso asibitin, kasancewar Zarah Æ´ar sanda shiyasa basu wani sha wuya ba wajen isa É—akin da yarinyar take.

Ita kaÉ—ai ke kwance a gadon jikinta rufe da zani yayinda acan kusurwar dakin wata ke zaune kan dadduma da alama dai itace mai jinyar.

Bayan sun mata ya jiki ne suka zazzauna inda Saleem ya ciro ƙaramar sound recorder tare da jan kujera ya ƙarasa bakin gadon yace.

"Baiwar Allah da farko dai ina ƙara jajanta miki akan wannan lamari da ya afku dake sannan inason sanin ko ke wacece.?"

"Da farko dai ni suna na Fahima ina zaune ne tare da iyayena a anguwar bakin kura dake nan jihar Bauchi. Sannan mahaifina mai ƙaramin ƙarfi ne." magana take a hankali alamum dai tana jin jiki.

"Meya jawo afkuwar wannan lamarin a gareki."

"Ina aikine a gidan wani ɗn majalisa dake nan anguwar mu wato Alhaji Nura Mai Riga. Tun lokacin da nafara aiki a gidan ɗan sa Kabeer ke yawan shigemin tare da nuna alamun yanaso muyi sabo sosai saidai ban bada damar hakan ba. To a ranar larabar data gabata ne bayan na kai masa abincinsa na rana kamar yadda na saba kowani lokaci bayan na gama girki ina kai masa nashi bangarensa. Bayan na ajiye abincin ne ya miƙomin kofin dake hannunshi wanda ke ɗauke da lemu ya umarceni da na shanye, naso nayi jayayya saidai yace idan ban sha ba bazai barni na tafi ba shiyasa na karɓa na shanye tare da miƙewa da nufin tafiya sai ya kuma cewa na share mai falon shi yayi ƙura. Tunda nafara sharar nakejin bacci na fizgata kafin nagama kuma bansan inda kaina yake ba sai farkawa nayj na ganni akan gadonshi ya ketamin haddi..." Ta ƙarasa faɗa tana mai fashewa da wani marayan kuka wanda ke nuni da ciwon abin da takeji.

Kashe recorder ɗin Saleem yayi kana ya miƙe ya fita yana musu alama da ido.

Zarah da Jidda ma miƙewa sukayi kana Zarah tace.

"Insha Allahu za'a bi miki haƙƙinki sannan kafin mu tafi za'a sa hannu a shigar dake aikin da za'a miki na matsalar yoyon fitsari da kika samu."

Godiya suka ƙara yi musu sosai.
Sanna su Jiddan suka bar É—akin.

Saida suka biya kuÉ—in aikin da za'ayi wa Fahima sannan suka bar cikin asibitin.

A hanyarsh da zuwa gida ne Jidda dake gaban motar ta waiwayo ta kalli Zarah data jingina kanta a jikin kujerar bayan motar tace.

"Zarah kina ganin ba muyi ganganci ba wajen shiga cikin wannan case É—in daya shafi Alhaji Nura Mai Riga.?"

"Banason halinki na saurin karaya Jidda, kada ki manta Allah yana tare da msi mai gaskiya." Ta faÉ—a tana mai É—agowa daga jinginawar da tayi jikin kujerar.

"Waye ne Alhaji Nura Mai Riga.?" Saleem ya tambaya hankalinshi na kan hanya.

*ASP ZARAH*👩‍✈️

_Daga Alƙalamin_✍🏻
_Asmau Bint Abubakar_
_Jasmine_🌸🌸

*Littafin ASP ZARAH na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da biya ba. Idan kinji kinason cigaba da karantawa toh ki biya kuɗi N300 kacal domin karantashi cikin kwanciyar hankali, idan kinsan zaki dinga yimin sharing ɗin littafi dan Allah kada ki biya kuɗin banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntu6eni a 07048961623 domin biya da kuma shiga group*.

*Jan Hankali*: _Ƙirƙirarren labari ne. Ban yarda a canjamin littafi ta kowace siga ba batare da izinina ba. A bi doka a zauna lafiya_ .
👩‍✈️
👩‍✈️
👩‍✈️
👩‍✈️
👩‍✈️
Chapter 7 · 0% Book details