← Book details Asp Zarah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 21

Sashe 11

Asp Zarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mintuna talatin ana fafatawa tsakanin ɓangare biyun inda Saleem ke gabatar da zafafan shaidun daya tada hankalin Alhaji Mai Riga da muƙarrabansa, domin hatta inda yake cewa Zarah tabbas ɗan shi ya aikata laifin da ake zargin shi saida aka gabatar a gaban kotu. Nan fa kotu ta rikice kowa na faɗin albarkacin bakinsa musamman ƴan adawan Alhaji Mai Riga.

Hutun rabin lokaci aka alkali ya bayar, gaba É—aya jama'a aka fita waje.
Duk yadda Mai Riga yaso ganin alkalin a wannan lokacin abu ya gagara, hankalin shi ne yaji ya tashi amma tunawa dayayi da irin maƙudan kuɗin da ya bawa alkalin sai ya ɗan samj nutsuwa tare da tabbatarwa kanshi samun nasara.

A daidai wannan lokacin kuwa Baaba tana zaune a falo tana kallon wa'azi a sunna TV, ɗaya daga cikin masu tsaron ne ya shigo tare da shaida mata cewa tana da baƙuwa, batare da dogon tunani ba tace ya shigo da ita.
Jim kaɗan ya dawo tare da Raliya wacce ta ɓadda kama sosai tamkar ba ita ba, wasu tsofaffin kayane a jikinta wanda a kowani lokaci zasu iya yagewa sai wata ƙaramar Ghana-Must-Go itama ta tsofa sosai.
Da sallama ta ƙarasa cikin falon sannan ta zauna ƙasa nesa da inda Baaba take.

"Ki hau saman kujerar mana baiwar Allah." Inji Baaba.

"A'a nan ma yayi Hajiya, ina wuni." FaÉ—in Raliya.

"Lafiya lau sannu da zuwa, sai dai ban shaida fuskar taki ba kodai gurin Zara'u kika zo ne."

"A'a Hajiya dama nazo neman aiki ne."

"Wane irin aiki kuma daga ina kike.?"

"Ni marainiya ce a garin Tilden Fulani nake, iyayena sun mutu ne sanadiyyar gobara da ta cinye gidan mu tun daga lokacin kuma na rasa masu taimakamin. Toh akwai wata Mata a can gurin namu da take shigowa birni tana aiki shine ta bani shawarar na shigo na zaga gidan masu hali na nemi aikin yi saboda nasamu abinda zan dinga rufawa kaina asiri dashi."

"Duniya ta lalace mutane basason taimako, ai shi maraya idan ka taimaka mi shi tamkar ka zuba adashe ne da zaka kwashe ranar lahira. Kada ki damu insha Allahu za'a baki aiki koda na goge-goge ne."

"Nagode Hajiya Allah ya saka da alkhairi."

"Amin babu komai ai hakkin maraya ne mukeson saukewa."Inji Baaba.

Sun ɗan jima suna taɓa hira kafin Baaba ta miƙe ta shige ɗaki bayan tabar Raliya a falo tana kallo, da sanɗa tabi bayan Baaba dan ganin mai zatayi a ɗakin, ganin shigewarta banɗaki ne yasa tayi saurin komawa falo tare da buɗe jakarta ta ciro wani abu kamar bead na kitson yara ta nufi saman bene. Bata sha wuyar gane ɗakin Zarah ba saboda taswirar gidan da ta haddace a kanta, ɗakin a buɗe yake dan haka tana shiga ta nufi gaban durowar kayan Zarah, wannan abun ta ajiye acan saman durowar ta yadda babu wani mahaluƙin dazai iya cewa akwai wani abu a gurin idan ba anfaɗa ba.
Komawa falon tayi cikin sanɗa tamkar ɓeran dayayi sata yana tsoron a kamashi.

A can kotu kuwa bayan mintuna talatin sun cika aka koma aka cigaba da fafatawa tsakanin ɓangarorin guda biyu, domin dai da alama shari'ar ta kwana ɗaya ce.

Shiru ya ratsa cikin kotun bayan shuɗewar wasu mintuna, duk wannan abu dake faruwa Alhaji Mai Riga lokaci zuwa lokaci yake ɗagowa ya kalli ɓangaren da Zarah take yana yi mata murmushin ƙeta domin dai zuwa yanzu ya gama tabbatarwa kanshi cewa shi ɗin mai nasara ne sannan baza a yankewa ɗansa hukunci ba.
Ita kuwa Zarah zancen zuci take a duk lokacin daya kalletan sai tace.

"Shi dai mutum mara basira ko ina yake ana ganewa."

Alƙali ne ya fara magana kamar haka.

"Bayan sauraron shaidu da ɓangare biyu suka gabatar tare da hujjoji wanda suka gamsar da kotu da kuma kundin tsarin shari'a na ƙasa, kotu ta yankewa Kabeer hukuncin zama a gidan kaso na shekaru goma tare da aiki mai tsanani sa'an nan zai biya tarar miliyan biyar domin nemawa Fahima lafiya, Alhaji Nuhu Mai Riga kotu ta kama shi da laifin yunƙurin baiwa ɗan sanda cin hanci, dan haka kotu ta yanke mishi hukuncin zama gidan horo na wata biyar ko kuma tarar miliyan ɗaya." yana gama faɗin haka ya buga gudumarsa wanda ke nuna alamar ya gama aikin shi na wannan rana.

Kotu fa ta rikice inda Alhaji Mai Riga keta zage-zage tamkar mai taɓin hankali ana riƙeshi, nan fa ƴan jam'iyun adawa da ƴan jaridu suka samu inda sukayi ta ɗaukan hotonan shi, wasu harda yi mashi video.
Haka yana ji yana gani aka wuce da ɗanshi ɗaya tilo tamkar rai zuwa gidan kaso, take kuma ya zube a ƙasa tare da sakin kuka mai tsanani.

"Jidda mu wuce gida kawai ki rabu da Saleem ɗinki da ƴan Jaridun nan." cewar Zarah bayan ta janyo hannu Jidda zuwa wani keɓeɓɓen waje a bayan kotun.

"Mene ne haka wai Zarah ki barni mana a haskani a jarida tare da hubby na."

"Mtssww mu wuce Jidda banason dogon zance, jikina na bani wani yanayi da ban gamsu dashi ba." ta faɗa tana tura Jiddan cikin motar ta, wuta ta baiwa motar bayan ta shiga itama, nan suka bar farfajiyar kotun zuwa gida...... ✍🏼

*By*
*Jasmine*🌸

*ASP ZARAH*👩‍✈️

_Second to the last free pages._

_Paid book._
_Domin samun damar cigaba da karantawa batare da ɗaukarwa kai alhaki ba ki/ka biya N300 kacal na normal group, VIP group kuma N500 amma dan Allah idan so samu ne karki biya VIP idan baki da aure saboda darussan da ake gabatarwa a ciki. Ku tuntuɓeni a 07048961623 domin biya._

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*
*M*. *W*. *A*.

Gudu takeyi tamkar zata tashi sama, yayinda Jidda ke mata ƙorafin karfa tayi sanadin tafiyarta lahira bata shirya. Ko kulata batayi ba har suka iso bakin gate ɗin gidan, horn tayi aka buɗe mata ta shigar da motar ciki, sai a lokacin ta samu nutsuwa amma duk da haka tanajin wani irin yanayi a tattare da ita.

''Haka kawai kin rabo ni da mijina, toh wallahi garin ma zamu bar miki tunda mun gama yin abinda ya tsaida mu." Inji Jidda.

"Ba iya garin nake so ku bari ba, dan Allah ku bar ƙasar ma baki ɗaya." Zarah ta faɗa cike da tsokana lokacin da take fita a cikin motar.

Da gudu Jidda ta bita suka nufi hanyar babban falo tamkar wasu ƙananan yara.

"Allah ya shirye ku, wannan ai sai kusa nima na ruga da gudu, manya daku kuna wasan guje-guje, ke Hauwa idan ita bata rigada ta gama girma ba ai ke kam kin girma saiki daina biye mata." FaÉ—in Baaba wacce ke zaune a falo lokacin da suka shigo da gudu.

"Kai Baaba kin manta wai nafi Jidda shekaru ne.?" Inji Zarah.

"Yo idan kin fita shekaru ai yanzu kam ta fiki tunda a É—akin mijinta take."

"Saboda kawai tayi auren.?"

"Ehh mana ai ko Æ´ar shekara 14 tayi aure yanzu dole za'a kirata da yayarki."

"FaÉ—a mata dai Baaba ko zata daina raina ni." Jidda kenan ta faÉ—i.

"Nima dai auren nan na kusa yinshi na huta." Ta faÉ—a tana zama a kujerar da Baaba take kai.

"Ahh lallai da bamu yi shawarar aurar dake ba gaba bamu san abinda zaki dinga furtawa a gaban mu ba." FaÉ—in Baaba tana tafa hannayenta.

Bata kulata ba saima plate É—in dake gaban Baaban data janyo wanda ke É—auke da lafiyayyen dambun shinkafa da yaji haÉ—i.

"Baaba yau kin tuna da gargajiya ne haka, shiyasa kika kasa jira mu dawo muyi girkin." Zarah ta faÉ—a tana É—ebo dambun a cokali da nufin kaiwa baki.

"Allah sarki bama nina dafa ba, baƙuwa mukayi shine nace ta shiga kicin ta girka mana gudun kada ku dawo a gajiye, kin ganshi nan yanzu aka gama shine na ɗebo naci."

Harta buÉ—e baki da nufin cin dambun da ta É—ebo, amma jin abinda Baaba ta faÉ—a yasata dawo da cokalin tare da maidawa kan plate É—in.

"Wacce baƙuwa kuma.?" Ta tambaya fuska a yamutse.

"Ƴar aiki na samu mana, tunda Iya Delu dai bamusan ranar dawowarta ba."

"Ƴar aiki kuma.?"

"Ehh ko banyi daidai bane uwata.?"

"A'a kawai nayi mamakin inda kika samo Æ´ar aikin ne bayan ba fita kikeyi ba."

"Nan tazo neman aikin, toh ganin muna buƙata yasa na ɗauketa, kuma naga tana da hankali da nutsuwa shiyasa bayan haka kuma marainiya ce."

"Ana É—aukan aiki batare da bincike bane Baaba.?"

Harara Baaba ta wurga mata kana tace.

"Nasan ki ai da shigen bin ƙwaƙƙwafi shiyasa ma na nemi wacce ta kawo ta birnin muka zanta, bayan haka kuma ga lambar ta nan na karɓa idan kinason jin ƙarin bayani, mtsww."

"Me yayi zafi Baaba tunda ke zata dinga taimakawa, nikam ai bani da matsala tunda ba gidan nake wuni ba."

"Yo ai nayi tunanin koh kulle ni zakayi tunda nayi abu batare da izinin ki ba."

Ita dai Jidda bata saka baki ba, tana zaune a kujera ta kurɓar fresh milk ɗin da ta ɗauko, saboda surutunta ne ma yasa bata saka baki ba domin dai Baaba batasan a fara magana a bari ta daɗi ba, shiyasa ta barta da Zarah sanin da tayi cewa Zarah bata da magana sosai, tasan zancen bazai yi nisa ba za'a ƙarƙareshi.

"Kin ci dambun ne Baaba.?" Zarah ta tambaya fuska babu walwala.

"Na É—ebo kenan zanci ai kuka shigomin a birkice."

Batace komai ba ta É—au plate É—in dambun ta nufi hanyar kicin.

"Ina zaki kaimin abincin kuma.?''

"Yau ba dambu na tsara zamu ci a gidan nan ba, dan haka babu mai ci. Habibaty taso mu dafa wani abu mai sauƙi kafin SaJid ɗin naki da baya jurar yunwa ya dawo." ta faɗa tana mai shigewa corridor ɗin dazai sada ta da kitchen.
Jidda ma tashi tayi da sauri ta bita tun kafin Baaba tayi magana.

"Ki kiyayeni fa Zara'u wallahi zan saɓa miki, ki kawomim abincin nan tun kafin na iso gurin na sameki." Faɗin Baaba dake ƙoƙarin tashi ta nufi kitchen ɗin.

"Kulle ƙofar nan SaJid karta zo ta dame mu."

"Toh ke wai meye dalilinki na hanata cin dambun ne, nima wallahi ya bani sha'awa so nake naci."

"Kawai naji ban yarda da girkin bane, dan haka babu mai ci."
Chapter 11 · 0% Book details