Sashe 4
Asp Zarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Zaka iya bata damar tafiya yanzu mun gama aikinmu sannan ka duba wayarka akwai saƙon kuɗi dana turama a asusun bankin ka."
Abinda aka faɗa kenan daga ɗaya ɓangaren sannan aka kashe wayar batare da jiran amsar da kwamishinan zai bada ba.
Kallon shi ya maida kan Zarah yace" ASP zaki iya tafiya. "
Cike da mamaki ta miƙe tare da sara mishi sannan tafice a ofishin, jikinta taji ya mata wani iri ga zuciyarta dake bugawa da ƙarfi tamkar zata faso ƙirjinta.
Shigarta cikin mota yayi daidai da katsewar kiran wayarta dake ringing kafin shigowarta, sai da ta zauna kafin ta sa hannu ta É—auki wayar.
Ido da zaro ganin anyi mata kira har 66, take ta duba domin ganin masu kiran, 35 missed calls daga Rahma, 6 missed calls daga Mustapha, 15 missed calls daga Daddy sai sauran kira 10 daga mutane daban daban.
Da sauri ta shiga danna kiran Rahma saidai har ta gama ringing ba'a É—aga, haka tayi ta kira ba'a É—agawa kafin ya danna kiran Daddy sai dai wayarsa bata shiga.
Ganin haka yasa ta canja akalar kiran ga wayar Mustapha.
Bugu biyo ya É—aga tare da faÉ—in" Zarah kina inane haka ake ta kiran wayarki bakya É—agawa."
"Na shiga ganawar sirri ne da kwamishina kuma wayar na cikin mota, meke faruwa ne.?" tafaɗa cike da zaƙuwar son jin abinda ke faruwa domin a lokacin bugawar da zuciyarta keyi ya ƙaru.
"Babu komai ki taho gida anason ganinki." yafaÉ—a gami da kashe wayar baki É—aya.
Cikin sauri ta taÉ—a motar tare da harbawa kan titi bakinta É—auke da kalmar hasbunallahu wa ni'imal wakil saboda yanayin da take jinta a ciki.
Tun daga farkon shigowar anguwansu take ganin jerin motoci har zuwa gaban gidansu data tara cike da jama'a, nan zuciyarta ta ƙara tsinkewa gami da tabbatar mata lallai wani abu ya faru, horn ta danna a ƙofar gidan saidai a maimakon taga mai gadinsu sai taga Alhaji Sulaima na buɗe mata ƙofar.
Bata ko gama parking ɗin motar ba ta fito da sauri, hannunta taji an riƙo hakan yasata tsaya wa daga tafiyar data fara tare da waigowa Daddy ta gani a tsaye.
Kallo É—aya ta mishi taga alamun kuka a fuskarshi.
"Daddy meke faruwane dan Allah ka faÉ—amin."
Batare da yayi magana ba yaja hannunta suka koma jikin motar, ƙofar baya ya buɗe mata tare da gyaɗa mata kai alamun ta shiga sannan shima ya shiga ya zauna.
"Zarah." ya faÉ—a bayan ya zauna
Cike da rauni ta amsa da" Na'am Daddy".
"Nasan kinyi karatun islamiyya har zuwa matakin da kika sauke alqur'ani koh.?"
Kai kawai ta iya gyaÉ—a mishi.
"Inaso ki nutsu wasu tambayoyi zan miki."
"Toh Daddy."
"Inaso ki gayamin abinda Allah yace a cikin suratul Baqara a ƙarshen aya ta ɗari da hamsin da biyar zuwa aya ta ɗari da hamsin da shida(2:155-156) tare da ma'anar shi."
Kai ta jinjina sanna tace" Allah maÉ—aukakin Sarki yana cewa
Ùˆ بشر الصبر ين(155) لَّذÙينَ Ø¥ÙØ°ÙŽØ§Ù“ أَصَٰبَتْهÙÙ… Ù…Ù‘ÙØµÙيبَةٌ قَالÙوٓا۟ Ø¥Ùنَّا Ù„Ùلَّه٠وَإÙنَّآ Ø¥ÙÙ„ÙŽÙŠÙ’Ù‡Ù Ø±ÙŽÙ°Ø¬ÙØ¹Ùون(156)
Fassarar shine
"Kuma kayi bishara ga masu haƙuri(155) Waɗanda suka kasance idan wata masifa ta same su sai su ce _Lallai ne mu ga Allah muke, kuma lallai ne mu, zuwa gare Shi muke komawa._
A taƙaice ayar na nufin idan Allah ya jarabci bawa da wanu abu na baƙin ciki sai ya kasance mai yawan furta kalmar "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un".
Murmushi yayi wanda iyakar shi fuska sannan yace" Masha Allah, to me Allah ya sake cewa a cikin suratul Ankabut aya ta hamsin dashi.?"
Allah yace"
ÙƒÙلّ٠نَÙْس٠ذَآئÙقَة٠ٱلْمَوْتÙÛ– Ø«Ùمَّ Ø¥Ùلَيْنَا ØªÙØ±Ù’جَعÙونَ
Fassarar ayar
"Kowani rai mai É—anÉ—anar mutuwane, sa'an nan zuwa gare Mu ake mayar daku."(Q29:57).
"Alhamdulillahi tunda kin kasance mai ilimi, kinga kenan duk abinda yasamu bawa to ƙaddararre ne sannan da mutuwa da rayuwa duk na Allah koh.?". Daddy yafaɗa yana mai yimata kallo irin na tausayawa.
"Ehh hakane Daddy."
"Toh Zarah inaso ki kasance mai haƙuri tare da rungumar ƙaddarar data same mu duka, kiyi haƙuri ƴan fashi sun shigo gidannan sannan sunyi kisan kai kafin su tafi."
A ruÉ—e ta kalli Daddy tanason gane inda maganarshi ta dosa.
Tace" Ƴan fashi, kisan kai.? Wa suka kashe mana.?"
Ganin tana shirin ficewa a hayyacinta ne yasa ya riƙo hannayenta biyu tare da faɗin" Ki nutsu Zarah sannan ki cigaba da faɗin kalmar Innalillahi wa inna ilaihi raji'un."
Haka yayi ta maimaita mata har zuwa lokacin da ta ɗan nutsu kafin ya fito ya zagaya ya buɗe mata ƙofar motar ta fito sannan yajata zuwa inda aka ajiye gawarwakin kafin a fita dasu a sallace su domin farfajiyar gidan bazata ɗauki mutanen da sukazo jana'izar ba.
Dangin mamatan ne a gurin kowa yana karantu musu addu'a tare da kallon ƙarshe.
Abinda ta hangone ya sata sulalewa a ƙasa batare da sun ƙarasa ba, da sauri Ammi data hango lokacin faɗowarta ta nufi inda butar Baba me gadi take ta ɗauko tare da watsa mata ruwan ciki a fuska.
Shidai Daddy yana tsaye yakasa koda motsawa domin zuwa yanzu shima ya fara rasa jarumtar shi.
Tsiyaya mata ruwan Ammi ta farayi ganin bata farfaÉ—o ba.
Cikin sa'a kuwa taja numfashi mai ƙarfi.
_Cigaban labari_.
Zuwa ƙarfe bakwai na dare gidan ya ƙara cika sosai saboda ƴan uwa da abokan arziki na nesa da suka ƙaraso, domin hatta dangin Babansu Shahid dake Taraba duk sunzo kasancewar dayawa daga cikinsu jirgi suka bi.
Haka akayi ta koke koke kafinan suka saurara aka cigaba da karɓan gaisuwa.
A daren ranar dai babu wani daga cikin wannan ahalin daya samu damar runtsawa, kwana sukayi suna raya wannan dare da yiwa matattun addu'o'i tare da fatan Allah ya basu juriyar rashin da sukayi.
Daddy ne ya hana a sanar da Sadiq dake ƙasar Singapore yana rubuta jarabawarshi ta ƙarshe na zama cikakken likitan zuciya wato *Cardiologist Consultant* sakamakon asarar shekaru da zaiyi inhar baici jarrabawar.
Muhammad Jawwad kuwa sai ranar da akayi sadakar uku Daddy ya sanar dashi, shima dai kuka yayi tayi saida Daddy ya rarrashe shi. Nan yace ma Daddyn zai nemi biza ya taho bayan yayi ƙorafin rashin faɗa mishi da ba'ayi da wuri ba.
Bayan kwanaki ukun ne baƙi suka rago a gida amma kullum wuni suke karɓar gaisuwa daga mutane daban daban, masu kwana ne dai babu.
A cikin kwana ukun nan duk wanda yaga halin da suke ciki saiya kuka, Baaba kawai mai ƙarfin hali a cikin su.
Ga Rahma da har yanzu bata farfaÉ—o ba.
GabaÉ—aya suna zaune a falo a daren ranar ukun harda Daddy da Mustapha da shima kullum baya rabo da gidan.
Zarah na kwance saman dogowar kujera yayinda tayi filo da ƙafar Baaba.
Lokaci ɗaya ta miƙe a firgice.
Kallonta Daddy yayi tare da faÉ—in" Lafiya kuwa Zarah.?"
"Daddy CCTV , na jona CCTV a duka falon dake gidan nan." Ta faɗa lokacin da ta miƙe sannan da gudu ta nufi hanyar ɗakinta......
Da gudu ta nufi cikin ɗakin tare da nufar inda ƙaramar na'urarta take ajiye, sashin abubuwan da suka faru a cikin satin ta shiga tare da playing daga ranar farko.
Daddy da sauran mutanen gidan ne suka shigo É—akin, gabaÉ—aya suka zauna domin kallon abinda ke wakana a cikin na'urar.
Saidai gabaÉ—aya babu abubuwan da suka faro a kwanaki uku da suka wuce wanda hakan ya tabbatar mata da cewa akwai wani wanda ya shaidama Alpha na'urar da ta saka.
Cike da takaici ta rufe na'urar tare da kwanciya akan gadonta.
Babu wanda ya tanka duk suka fice a É—akin.
Babu daÉ—ewa kira ya shigo wayar Zarah, hannu ta kai ta janyo wayar tare da kallon fuskar wayar domin ganin mai kira. Æoyayyiyar number ce ke kira, tamkar bazata É—aga kiran ba saida ta kusa yankewa kafin ta É—aga tare da karawa a kunnenta batare da tayi magana ba.
"Na tabbatar yanzu kin fara gaskata abinda Alpha yake da damar yi ga duk wanda ya shiga gonarsa." Daga ɗaya ɓangaren aka faɗa
Zaune ta miƙe batare da tayi magana domin ta gane wanda yake maganar.
Magana ya cigaba dayi ta hanyar faÉ—in "Kada kiyi saurin karaya ta hanyar ajiye aikinki Zarah domin kin riga kin shiga wasan da baki da damar fita, ba'ayi komai ba tukun. Kin shirya bada kadarar ko baki shirya.?"
Mamaki ne ya cikata jin abinda ya faɗa, tabbas Alpha ba ƙaramin shiri yayi akanta ba domin da Daddy kaɗai tayi maganar ajiye aiki kuma shiɗin ma bai goyi bayan hakan ba sannan tanada tabbacin cewa ba wajen Daddy yaji wannan batun ba. Ajiyar zuciya ta sauke a ɓoye kafin tace
"Bana zuwa akan lokaci amma tabbas idan na iso waje ina jan ragamar kowani wasa tare da kasancewa mai nasara, ka faÉ—ama kowaye ya sanar dakai cewa Zarah zata ajiye aiki da yaje ofishinta a gobe ranar litinin domin ya samu maka cikakken bayani."
Bata jira mai zaice ba ta kashe wayar gabaÉ—aya.
Takalmi ta zura tare da fita zuwa falo, dukkan su suna zaune kamar yadda suke da farko.
Zama tayi kusada ƙafafun Daddy tare da faɗin
"Daddy inaso gobe zan koma bakin aiki."
"Zara'u wace irin magana kikeyi haka, kodai kema ƙwaƙwalwarki ta taɓo ne kamar yadda ƴar uwarki ta samu.?" Faɗin Baaba wacce maganar da Zarah tayi ya tadata Zaune daga kishingiɗen da take.
Sunkuyar da kai tayi batare da tayi magana ba.
Daddy ne yayi gyaran murya tare da cewa.
"Baaba ina ganin mu barta ta koma bakin aikinta ƙila akwai wani muhimmin abu da zata gudanar ne bayan haka kuma zamanta a gida bashine zai dawo mana da waƴanda muka rasa ba. Hasalima aikin nata zai taimaka wajen binciko da masu hannu akan wannan lamarin."
Jinjina kai Baaba tayi cikin gamsuwa da maganganun Daddyn sa'an nan tace.
"Toh yaya batun Rahmatu kuma.?"
"Ehh Amminsu zata wuce da ita can Cairo a cigaba da duba lafiyarta tunda maigidan nata ya amince, Zarah kuma zata zauna anan saboda binciken da zata cigaba da gudanarw. Sannan ina neman alfarmarki Baaba da ki cigaba da zama anan tare da ita, kasancewar mace bai kamata ta zauna ita kaɗai ba saboda kare mutuncinta. Insha Allahu kuma zamuyi ƙoƙarin ziyartar ku lokaci lokaci kamar yadda muka saba." Cewar Daddy
"Babu damuwa Sulaimanu Allah yayi albarka ya albarkaci zuri'a."