Sashe 6
Asp Zarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru ya biyo baya na wani lokaci kafin Alpha yace.
"Ku bar batun saka camera É—in tukunnan zanji da lamarinta a garin Abujan."
Ya kashe wayar batare da yayi magana ba.
Ƙayataccen ɗaki ne wanda yaji kayan alatu masu matuƙar kyau da tsada, tsaruwar ɗakin kaɗai zaisa mutum yayi tunanin na wani hamshaƙin shugaban ƙasa ne amma idan aka ƙurewa fitilun dake kawowa da ɗaukewa idon za'a gane mamallakin ɗakin sakamakon sunan Alpha da suke rubutawa a kowani kawowa da suke yi. A tsakiyar ɗakin wani haɗaɗɗen gilashi ɗauke da kyawawan kifaye a saman shi cikin ruwa suna ta shawagi yayinda ƙasan gilashin ke ɗauke da wasu kyawawan halittun ruwa da bazan iya tantance sunayensu ba.
Maganganun ke tashi a cikin falon saidai banga alamun ta inda nake jiyo maganar ba, muryar namiji ne ke maganar inda yake cewa.
"A matsayin marainiya mai neman aiki domin tallafawa mahaifiyarki zakije gidan, sannan ki tabbatar bata cikin gidan yayinda zakije neman aikin saboda kaucewa matsala."
Har zuwa wannan lokaci mai maganar bai bayyana ba illa wata matashiyar yarinya da tafito daga wata kusurwa a cikin falon, kyakkyawa ce daidai gwargwado sannan fatarta ta kasance kalar chocolate.
Kallo É—aya mutum zaiyi mata ta gane tana cikin damuwa sosai sakamakon idanunta da sukayi jazir saboda kukan da tasha.
Ƙofar dazata sadata da farfajiyar gidan ta buɗe tare da fita a falon, babban fili ne sosai dake ɗauke da gine gine a wani gefe sannan shukoki kala daban daban da suka ƙawata wajen ciki harda manyan bishoyin kwakwa wanda su sukafi yawa a wajen. Sai ƙananun shukoki da aka tsarasu tamkar a ƙasar turai, a ƙasa kuwa wasu kyawawan duwatsu ne masu haske da sheƙi waɗanda ke ƙara bayyana kyawu da tsarin farfajiyar wannan gida da ya kasance tamkar na sarauta. Jefi-jefi mutane na shawagi a farfajiyar inda yawancinsu suka kasance mata sa'an masu ƙananun shekaru.
Tafiya tayi sosai kafin ta iso wani keɓaɓɓen guri da ruwa ke gudana tsakanin waɗansu matsakaitan duwatsu, wasu mata ne ke zaune su uku suna ɓare kwakwa. Ta farko keyin hanya a jikin kwakwar, ta biyu kuma ke ƙarasa barewa yayinda ta ukun cikinsu ke ɗauraye jikin kwakwar bayan a ɓare tare da jerasu cikin wani kyawawan kwando.
Zama matashiyar yarinyar tayi a gefe tare da jingina kanta a jikin wata ƙaramar bishiya.
GabaÉ—aya suka maida hankalinsu kanta, kafin wacce ke wanke kwakwar tace.
"Meke faruwa ne Raliya, wani abinda ya miki ne.?"
ÆŠago kanta tayi tare da maida kallonta garesu tace.
"Zanso ace wani abu ne ya shiga tsakanina dashi saidai babu abinda yamin illa aiki dazai turani a gidan da waÆ´annan lu'u lu'un suke."
"Raliya wani lokacin kina saka mana shakku akanki, dukkan mu anan fata muke mubar cikin wannan azzalumin gida ke a lokacin ne keki fatan kasancewa da mai gidan ki dinga aikata haramtaccen abu dashi." Fadin ɗaya daga cikinsu bayan ta maida hankali kan ɓarar kwakwar da takeyi bayan jin furucin Raliyan.
"A yanzu bana fatan barin wannan wajen saboda waƴanda nayi fatan ƙara kasance dasu basa duniyar zan fiso na cigaba da kasance anan saboda ko bana nan ɗin zaiyi wuya na tserewa *ALPHA* tunda na rigada nasan wasu sirrika nashi, bazai taɓa barina a raye ba tunani zaiyi asirin shi zan tona." Faɗin Raliya
ÆŠayar da tun fara maganar bata tofa ba tace.
"Ki dinga yiwa kanki kyakkyawan fata Raliya idan ba haka ba zuciyarki zata iya rikeÉ—ewa ta koma irin tasa na marasa imani."
"Hauwa kenan ai yanzu haka banajin akwai abinda zuciya da gangar jikina zasu kasayi indai umarnin Alpha ne. Ku da iyayenku kawai ya rabaku ya kawoku nan amma nifa? Da hannayena guda biyu yasa na kashe iyayena, zuciyata ta gama bushewa tun a waccan ranar. Zan iya raba kowaye da jindaÉ—in sa kamar yadda akasa na raba kaina da nawa jindaÉ—in." Ta faÉ—a tana mai maida kanta ga kishingiÉ—ar da tayi a jikin bishiyar.
Babu wanda ya kuma tankawa a cikinsu domin dai sun saba da jin kwatankwacin wannan furuci a bakin Raliyan tin bayan da tasamu kusanci da Alpha lokacin da tayi nasarar ganin yatsun hannunshi, mutum ne shi mai matuƙar taka tsantsan kasancewar shi wanda jami'ai ke nema ido rufe shiyasa baya taɓa bada damar a ga wani sashi na jikinshi koda kuwa farce ne. Idan kuwa kayi nasarar ganin wani abu nashi to daga wannan lokaci zaka zama makusancin shi bayan an shiga dakai wani ɗaki mai taken _Kusanci da Alpha_, wata ɗaya cur ake kwashewa ga duk wanda ya samu nasarar shiga wannan ɗakin saidai mutum yakan fito ne a galabaice. Idan mai tsawon kwana ne zaiyi dogowar jinya, idan yazo da ƙarar kwana kuma saidai a wuce da mutum kabari. Babu wanda yasan abinda akeyiwa mutum a cikin wannan ɗakin domin hatta Raliya da aka shigar da ita tace bazata iya tuna komai da ya faru ba.
Ko bayan mutum ya samu kusanci dashi bazai ƙara samun damar ganin wani sashi na jikinshi ba saidai zai kasance yana kasa saɓa umarnin Alpha ɗin koda kuwa umartarka yayi da kashe kanka.
*Abuja*
Cikin kwanciyar hankali da tsari ake gudanar da taron na ƙarawa juna sani a harkar aiki inda Zarah tayi zarra kwarai wajen baiyana dabaru da koma salon aiki da kowani jami'i ya kamata yayi amfani dasu, a cikin kwana huɗun da tayi a gari Abuja an samo nasarar zaƙolo manyan masu laifi da aka daɗe ana nema, hakan yasa aka shirya karramata a ranar ƙarshe da za'a kammala taron a matsayinta na jajirtacciyar ƴar Sanda da hukuma ke son irinta.
Kasancewarta mace kuma kyakkyawa yasa manyan masu muƙami a rundunar Ƴan Sanda ke ƙoƙarin janta a jiki amma taƙi bada damar hakan, domin hatta ɗakin da aka kama mata a hotel ɗin da aka sauki baƙi irinta wanda sukazo daga wani gari taƙi karɓa. Gidan wata abokiyar karatunta na sakandire dake zaune da mijinta a cikin garin Abujan nan ta sauka.
*Bauchi*
A yau ne akayi addu'ar kwana bakwai na rayukan da aka rasa a farfajiyar gidan marigayi Alhaji Abdul_Jalal, inda akayi saukar alqur'ani mai girma tare da yiwa mamatan addu'o'i.
Ƙarfe biyu jirginsu Ammi ya ɗaga zuwa Cairo ita da maigidanta da kuma Rahma da suka wuce da ita domin cigaba da duba lafiyar saboda har zuwa wannan lokacin bata magana tun bayan farfaɗowarta.
Daddy da Momi ma bayan sallar la'asar suka É—auki hanyar tafiya Bauchi. Sai gidan ya ragw daga Baaba sai Muhammad Jawwad da wata tsohuwa da Daddy ya samu domin tayasu zama sannan jami'an tsaron da Mustapha ys É—auki nauyin ajiye musu guda biyar.
Shima Muhammad Jawwad a washegarin ranar zai wuce Abuja ya ziyarci wani abokinshi dake aiki acan, sa'an nan daga can ya wuce ƙasar England domin haɗo takardunshi tare da takardar shaidar aiki da yakeyi acan saboda samun sauƙin cigaba da aikinshi a Nigeria.
Washegarin kuwa shima ya wuce garin Abuja, kasancewar su Daddy basuyi mishi batun Zarah ba shiyasa baisan tana garin ba.
Ƙarfe 12:30nr ya isa garin Abujan inda abokin nashi yazo ta taryeshi a airport ɗin, daga nan kai tsaye gidanshi suka nufa.
Bayan yaci abinci ya huta ne ya buƙaci su fita domin zaga gari.
Ta fito da nufin tafiya gurin da suke ƙaddamar da taron kiran wata abokiyar aikinta Toyin wacce suka haɗu wajen taron ya shigo wayarta inda ta buƙaci ta biyo ta hotel ɗin da take domin su wuce tare.
Agogon hannunta ta kalla taga akwai sauran mintuna 45 kafin a fara taron hakan yasa ta yanke shawarar tsayawa a wani resturant da tagani domin siyan burger da ta tashi da marmarin ci a yau.
Suna ƙoƙarin fitowa daga *Koise Delicies* ita kuma tana ƙoƙarin shiga waya kare a kunnenta, karo sukayi da Abdallah wanda ke gaba yayinda Muhammad Jawwad ke bayan shi.
"Sannu dan Allah." shine abinda ta furta sannan ta cigaba da tafiya tana mai magana a waya inda takw cewa.
"Jirani a reception na hotel É—in bansan É—akin ba."
Dogon tsaki Muhammad Jawwad ya saki bayan sun shiga mota kafin yace.
"Suna fakewa da aikin Æ´an sanda suna abinda suka ga dama, yanzu menene abin burgewa ga mace a aikin Æ´an sanda kuma musulma.?"
Dariya Abdallah yayi sannan yace.
"Nikam naga abin burgewa sosai, ka dubi yadda tayi shiga cikin kamala ba kamar wasu matan dake irin aikinta ba, sannan maganar hotel da kaji tanayi ƙila wani aikim zai kaita can kasan su aikinsu babu inda bayakai mutum."
Baki kawai ya taɓe batare da ya kuma magana ba....
*ASP ZARAH*👩â€âœˆï¸
_Daga AlÆ™alamin_âœðŸ»
_Asmau Bint Abubakar_
_Jasmine_🌸🌸
*Da sunan Allah mai rahma mai jinƙai, dukkan yabo da godiya su tabbata gun Allah maɗaukakin sarki daya bani lafiya, ilimi, basira da kuma lokaci dana samu daman rubuta wannan littafin. Allah yaƙara dubun salati a gun mafificin halitta annabinmu Muhammad S. A. W da ahlinsa da sahabbansa dama dukkan masu bin tafarkinsa har zuwa ranar tashin alqiyama.*
*Ina roƙon Allah ya tsaremin alƙalamina daga rubuta duk wani abu dazai kawo ɓatanci a cikin al'umma. Allah ina roƙonka yadda nafara rubuta wannan littafi lafiya Allah kabani ikon gamashi lafiya, kurakuran dazanyi ciki Allah ka yafemin da wanda nasani da wanda bansani ba.*
*Littafin ASP ZARAH na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da biya ba. Idan kinji kinason cigaba da karantawa toh ki biya kuɗi N300 kacal domin karantashi cikin kwanciyar hankali, idan kinsan zaki dinga yimin sharing ɗin littafi dan Allah kada ki biya kuɗin banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntu6eni a 07048961623 domin biya da kuma shiga group*.
*Jan Hankali*: _Ƙirƙirarren labari ne. Ban yarda a canjamin littafi ta kowace siga ba batare da izinina ba. A bi doka a zauna lafiya_ .
👩â€âœˆï¸
👩â€
Free Page
Alhamdulillahi taro yayi kyau an watse lafiya bayan kyaututtuka da aka rarrabawa jami'ai tare da karrama wasu daga ciki inda Zarah ta kasance cikin waÉ—anda aka karrama.
Saida ta ƙara kwana biyu cikin garin Abuja sakamakon jirginsu Jiddah dazai sauka ta garin bayan ya taso daga ƙasar Malasia.