← Book details Asp Zarah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 21

Sashe 18

Asp Zarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko da ta idar gaban dressing mirro ta nufa domin shiryawa, saboda ƙarfe biyar jirginsu Daddyn zai sauka, simple makeup tayi wanda ya matuƙar yi mata kyau saboda yadda ta tsara shi, wardrobe ta kuma tare da zaro wasu rantsattsun riga da siket na wani dark blue ɗin less mai ratsin fari, cikin hanzari ta saka kayan ganin lokaci na ƙurewa, ba ƙaramin karɓar jikinta kayan sukayi ba musamman data yafa farin gyale mai duwatsu sanna ta saka farin takalmi, wayarta ta ɗauka ganin har ƙarfe 4:40pm yasa ta fita da sauri, bata tarar da Baaba a falo ba hakan yasa tabarwa Raliya dake ƙoƙarin shiga kitchen sallahun soya mata sinasir ɗin tare da faɗama Baaba cewar ta wuce airport.

A farfajiyar gidan ta gansu suna ƙoƙarin shiga mota wanda tana da tabbacin suma airport ɗin suka nufa, inda motarta take itama ta nufa batare da ta kuma kallon inda suke ba.

"Amaryarmu irin wannan kyau haka kamar wacce ke shirin zuwa gasar kyau na duniya gabaɗaya." cewar Abdallah daya leƙo da kanshi ta window yana magana.

"Banda zuga dai."

"Da gaske fa, kizo mu wuce tare mana ko ba airport É—in kika nufa ba kema."

"A'a kuje kawai yanzu zan biyo bayanku."

"Sai tayi yawon dandin nata kafin nan, kaga bazata haɗa hanya damu mu hanata aikata kudurinta ba." cewar M.J yana taɓe baki kamar yaga wani abin kyama.

Hawaye taji......✍️

*BY*
*JASMINE*🌸🌸

*ASP ZARAH*👩‍✈️

...Hawaye taji masu zafi suna ƙoƙarin silalo mata, da sauri ta buɗe motar ta shige domin batason M.J ya gano lagonta.
Ta rigasu isa airport ɗin dan haka ta samu guri tayi parking sannan ta fito da jingina da motar ta yadda waɗanda take jira zasu iya hangenta, batayi minti goma da tsayuwa ba jirgin ya fara ƙoƙarin sauka ƙasa daidai lokacin kuma motarsu Abdallah ta iso gurin inda sukayi parking a kusa da tata motar.
Matafiya ne suka fara saukowa cikin takon isa na hamshaƙan da suka baro ƙasar turawa, ɗaya bayan ɗaya suka jero akan matattakalar da zata sauko dasu daga jirgin, ido ta baza sosai ta inda zata gano ɗan'uwan nata. Duk da yawan video call da sukeyi amma dakyar idanuwanta suka iya ganeshi saboda kyau daya ƙara, nufowa suke domin ƙarasowa inda suke tsaye ita da su Abdallah, saidai bazata iya jira su ƙaraso ba dan haka ne ta ruga a guje ta ƙarasa inda suke tare da rungume ɗan'uwan nata cikin tsantsar farin ciki, shima hannayensa biyu yasa ka ya maida mata rungumar tare da ɗan bubbuga bayanta jin tana shessheƙar kuka.
"Bakyason ganina ne na koma inda na fito ko.?" ya tambaya cikin son yaga ta daina hawayen.

Da sauri ta sakeshi tana saka bayan hannunta ta goge hawayen kana tace.
"A'a dear murnar ganinka ce kawai ta saka hakan, idan kace zaka koma to nima binka zanyi mu koma tare."

Daddy dake tsaye yana kallonsu ne yace.
"Wato ni ko sannu fa zuwar ma bazan samu ba duk da ni naje na taho dashi, ai babu damuwa nikam naga warayya ƙarara a fili."Cikin zolaya ya ƙarasa maganar.

Ɗan durƙusawa tayi da hanzari tana faɗin
"Sorry Daddyna ai nafi kowa murnar son ganinka, barka da dawowa ayimin afuwa."

"Babu komai daughter mu hanzarta mu wuce gida naga hadari ya haÉ—o."

Hannushi ta riƙe kamar wata yarinya suka ƙarasa wajen motocin, cikin fara'a suma sukayi musu barka da dawowa, nan aka ɗanyi raha irin wacce ke tsakanin uba da ƴaƴansa kana suka fara ƙoƙarin shigar da kayansu mota domin shigewa gida, Zarah kam hannun Sadiq taja zuwa motarta ta buɗe mishi gidan gaba ya zauna sannan ta dawo domin ɗaukar wasu kayan ta saka a tata motar, daidai lokacin daya sunkuya domin ɗaukar wata jaka itama lokacin da sunkuya zata ɗauka, a hankali yayi magana ta yadda ko Daddy dake tsaye agun bazaiji mai ya faɗa ba yace.
"Wato ke a ko ina saikin bayyana salon karuwancin naki ko, saboda asan kin shahara a bariki ne zaki rungume mutum a bainar nasi kuma ki ƙi sakinsa saboda ke ga ƴar bariki ko? Toh Allah yasa dai rungumar iya ta ƴan'uwan taka ta tsaya bata kauce hanya ba."

Da sauri ta ɗaga idonta da sukayi jazir saboda ɓacin rai ta kalleshi, wato cin mutuncin nasa har yakai matakin dazai iya zarginta akan ɗan'uwanta da suka fito ciki ɗaya, abubuwan da M.J yake mata idan ta mutu bata rama ba toh tabbas bata yafe mishi ba, batace komai ba ta ɗauki jakar ta nufi motarta.
Cikin ƙoƙarin danne ɓacin ran da take ciki ta buɗe mazaunin direba ta shiga motar tana faɗin
"Sorry dear na barka kana jira."

Kasa amsawa yayi illa idanunshi daya kafeta dasu yanason gano wani abu tattare da ita.
"Zarahty kina kallon kanki a madubi kuwa.?" ya tambaya da alamun mamaki a tattare dashi, leƙawa tayi kaɗan ta kalli madubi motar sannan ta ɗan juya ta kalleshi tana cewa.
"Nifa Yaya banga inda kwalliyar nan ta ɓaci ba, kawai ka saba da ganin fuskar turawa ne shiyasa komai kake kallonshi sabo."

Wanj murmushi yayi da iyaka fuska ya tsaya yace.
"Ba batun kwalliya nakeyi ba, ke baki taɓa tsayuwa a gaban mirro kin fahimci how not ok are you ba, baki ga irin ramar da kikayi ba kamar wacce ta fito a prison, wai meke damunki ne haka little."

"Ka dawo kenan ai Yaya, toh nidai aikine sukemin yawa bana samun lokacin hutu shiyasa kaga ina ramewa, ni banga ramar danayi ba ma fa."

"Ke kam ai bazaki gani ba, amma nasan tabbas bayan aiki akwai wani abu daban a cikin ranki."

"Uhmm nidai babu komai fa"

"Shikenan I'll figure out myself tunda nadawo ƙasar, ja mota mu tafi gida gashi harsu Daddy sun wuce sun barmu."

"Toh" ta faÉ—a sannan ta tayar da motar suka bar farfajiyar wajen, suna tafe suna hira tamkar wasu sa'anni ko kuma abokai saboda yanayin yadda suke hirar cikin raha da tsokanar juna, wannan na É—aya daga cikin tarbiyar da iyayansu suka basu a zamanin da suke raye, son juna da kulawa ba tare da la'akarin babba ko yaro ba.
Cikin Mintuna ƙalilan suka iso gidan horn tayi aka buɗe ƙofar sannan ta nausa kan motar zuwa ciki, a farfajiyar gidan suka tarar da Baaba tsaye tana jiran ƙarasowarsu.
"Sannu da zuwa angona na kaina." tace lokacin data ƙaraso jikin motar, Sadiq ne ya fara buɗewa ya fita ta gefen da take tsayen, baki ta riƙe tare da zaro ido kamar tsohuwar da ta kama kwarto a ɗakin suruka, saboda mamakin yadda jikan nata ya sauya gabaɗaya duk kuwa da yawan ganinshibda takeyi idan suna video call, dariya yayi mai sauti ganin yanayin Baaban da kuma irin tsayuwar da tayi yace.
"Haba amaryata irin wannan kallon haka, ko kina tsoron ayi saurin kwace miki ni ne.?"

"Kwacewa ta nawa kuma Habu, ai yadda ka rikiÉ—e ka kuma bature nasan baza'a rasa wata baturiyar data kwace ka ba."

"Toh ki kwantar da hankalinki ni É—in naki ne ke kaÉ—ai kinji my one and only kakaty."

"Nifa banason wannan salon iskanci, daga dawowa zaka fara zagina tun daga kan iyaye da kakannina da wannan É—an iskan yaren."
Dariya yayi sosai kafin ya dakata yace
"Toh yi haƙuri rabin raina, mu ƙarasa ciki sai muyi magana."
Juyawa yayi yana waige-waige yace
"Little ta shige ta barmu a tsaye ashe."

"Wannan mai baƙin miskilancin ai ba tsayawa zatayi ba."

"Ohh tana nan da halin ashe."

"Sai abinda ya ƙaru."

"Little ba dama Allah ya yaye mata."

"Amin idan mai barin ta ne."

Nan suka shige falon suka samesu idan Zarah ke zaune a ƙasan kujerar da Daddy yake kai ta ɗaura kanta akan cinyarshi, Abdallah da M.J kuwa suna zaune ne a kujera two seater. Zama sukayi aka shiga gaisuwar yaushe gamo da kuma ƙarin ta'aziyar da aka yiwa juna, sun jima suna hirar kafin Baaba ta umarci duk su miƙe domin zuwa dinning, Zarah ce tayi serving kuwa da abinda yakeso sannan suka fara cin abincin cikin nutsuwa da yadda addini ya koyar.
Ko da suka gama ita ta tattare gurin ta kimtsa shi yabkoma kamar ba'aci abinci a gurin ba, falon ta kuma inda ta samu Daddy ya wuce sashin baƙi domin hutawa, zama tayi a gefen Baaba akan doguwar kujera tace.
"Dear ba zakaje kayi wanka ka huta ba kaima."

"Ke Zara'u kowa saikin ɓata mishi suna ne, mene ne kuma giya ɗin da kike kiranshi dashi."
Dariya sukayi gabaÉ—ayan su har M.J da hankalinshi yake akan wayarsa saida ya É—an murmusa, tsagaitawa Sadiq yayi yace
"Gaskiya ba ƙaramin wauta nayi ba na barin Nigeria ko wannan comedy ɗin da kike cirewa ai ya ishi mutum farin ciki na sati guda, Little jeki haɗamin ruwan wanka ganinan zuwa."
Miƙewa Zarah tayi cikin dariya tabar falon.

"Turanci bai yi muku rana ba tunda kun zubar da al'adun ku."

"Kakaty kenan, bari naje nayi wanka na huta sai na dawo mu cigaba."
Shima miƙewa yayi tare da bawa Abdallah hannu sukayi musabaha, hannu kawai M.J ya ɗaga mishi lokacin daya miƙa mishi hannu da nufin yin musabahar, baiyi mamaki ba domin tun zuwanshi ya fahimci ɗabi'un M.J ɗin musamman a gareshi da yake ganin tamkar baiyi farin ciki da dawowar tasa bane, kaɗa kai kawai yayi sannan ya nufi hanyar side ɗinshi.
A tsaye ya tadda ta tana ƙara kimtsa mishi ɗakin, murmushi yayi mai sauti yace.
"Ke dai bakya iya zama bakiyi aikin komai ba."

"Tab! Ina hutawa mana, kawai naga baka da wanda zai maka ne shiyasa nakeyi."

"Ai kuwa nagode na kusa kawo miki Anty ki huta."

"Da gaske Yaya." ta faÉ—a da É—oki

"A'a bance ba karki kaini gaba." dariya sukayi duka sannan ya shige banÉ—akin yana faÉ—in.
"Idan kin gama ki É—aukomin fresh milk."

"Toh"
Sai da ta kimtsa É—akin sosai duk da jiya ta shigo ta gyara amma tana ganin abubuwan da yakamata ta gyara musu waje, fita tayi domin zuwa É—auko fresh milk É—in.
Baaba kaÉ—ai ta tarar a zaune tana kallo sai Raliya dake Æ´an goge-goge a gefe.
"Yauwa Zara'u yanzu nake shirin aika Raliya ta kiramin ke."

"Me zanyi miki kuma."

"Bani ke nemanki ba, Abdullahi ke nemanki zakuyi sallama domin daga masallaci zasu wuce."
Chapter 18 · 0% Book details