Sashe 10
Asp Zarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kiran wayar daya shigo ne yasa ta saka hannu ta jawo wayar daga inda take, numbar Daddy da tagani ne yasa bata É—aga ba har saida ta yanke sannan ta maida kiran.
"Assalamu alaikum."
"Wa'alaikumus salam daughter barka da safiya."
"Daddy ina kwana."
"Lafiya lau kun tashi lafiya koh.?"
"Lafiya kalau Daddy ya Momi."
"Gata nan lafiya lau, yasu Baaban dai da mutanen turai."
"Duk suna lafiya Daddy."
"Kin fita aiki ne yau.?"
"Ehh ina office."
"A'a toh bari na bari ki koma gida kar na katse miki aiki, dama nayi tunanin kina gida ne shiyasa na kira muyi magana."
"Bakomai Daddy ba aiki nakeyi ba dama, zamu iya magana babu damuwa."
"Toh Masha Allah, nace ko Baaba ta isar miki da saƙo na.?"
"Ehh Daddy ta gayamin kuma na amince."
"A'a Zarah idan kina da wani ki faÉ—a kar na tauye miki."
"Babu kowa Daddy."
"Toh nagode kwarai Allah yayi albarka."
"Ameen Daddy."
"Sai anjima ki gaishe da su Baaban."
"Zasuji insha Allah."
Nan suka yi sallama ta aje wayar a gefenta tare da sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi.
"Oh ni Fatimaj Zarah, aure da mijin da bansan shi ba."
Sai kuma tayi murmushi ita kaÉ—ai tare da kaÉ—a kai.
.........
Shi kuwa Alhaji Mai Riga bayan fitarsa daga office ɗin Zarah cike da takaicin rashi haɗin kai da bata bashi ba, kai tsaye gidan alƙalin kotun da aka shigar da ƙarar ya nufa.
Bai wani sha wahala ba aka shigar dashi cikin gidan, bayan sun gaisa da alƙalin ne yake faɗa mishi abinda ke tafe dashi nason kar a yankewa yaronshi hukunci tare da korar ƙarar gabaɗaya.
Toh ƙasar tamu dai ta ɓaci kowa son kuɗi kawai, babu ɓata lokaci alƙalin ya amince gani irin maƙuda kuɗin da aka aje a gabansa.
Sallama sukayi zuciyar Alhaji Mai Riga fal da farin ciki.
*By*
*Jasmine*🌸
*ASP ZARAH*👩â€âœˆï¸
_Paid book_.
_Domin samun damar cigaba da karantawa batare da É—aukarwa kai alhaki ba ki/ka biya N300 kacal na normal group, VIP group kuma N500 amma dan Allah idan so samu ne karki biya VIP idan baki da aure saboda darussan da ake gabatarwa a ciki._Za'a turo kuÉ—i ta wannan asusun 0153109156 Union Bank, sannan a turo shaidar biya ta 07048961623._
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*Page 9*
*ALPHA VILLA*👽
Kamar koda yaushe ba'a taɓa ganin daga inda yake magana saidai a jiyo sautin muryar sa.
"Raliya ki kula sosai banaso a samu wata matsala, yanzu idan kuka bar nan za'a kaiki filin jirgi inda daga can zaki wuce Gombe, kiyi amfani da adireshin dana baki ki isa zuwa gidan kamar yadda na tsara miki, ki tafiyar da komai cikin tsari kada ki bari a gano ki. Gobe da safe ne zaki isa zuwa gidan bayan ta fita zuwa gurin aiki. Kin fahimce ni."
"Na fahimta Oga zanyj komai yadda kace." Raliya dake rakuɓe a gefen ɗaya daga cikin kujerun ɗakin ta faɗa kanta a sunkuye.
"Banason rawar kai Raliya, samo masaniyar inda lu'u lu'un yake shine kawai aikinki, ban baki damar kiyi yunƙurin sacewa ba wannan aikin ba naki bane. Ina ƙara jaddada mi ki."
"Ba za'a samu matsala ba Oga."
"Ki tashi kije ki gama kintsawa ƙarfe biyar za ku wuce."
"Toh na barka lafiya yallaɓai." ta faɗa tana mai miƙewa daga durƙushen da ta ke sa'an nan ta nufi ƙofar da zata fidda ta daga cikin falon.
........................................
Haka Alhaji Mai Riga yayi ta zagawa yana siye bakin waɗanda ke da masaniya akan case ɗin hatta lauyan bogi da Zarah ta ɗauka saida ya bashi maƙudan kuɗi akan ranar da za'a shiga kotu yayi tawaye yace shi lauya ne mai kare wanda ake zargi.
Yau ta kama ranar lahadi inda gobe ranar litinin za'a shiga kotu, dukkan su suna zaune a falo suna hira jefi- jefi wanda akasarin hirar tsakanin Jidda ne da Baaba domin Saleem da Jidda suna gaban na'ura mai kwakwalwa suna gudanar da aiki.
Baaba ce ta kalli gefen da su Zarah suke kana tace.
"Zara'u ince dai mahaifin naku ya faÉ—a miki matsayar da ya yanke game da bikin ku."
Kallonta Zarah tayi batare da ta tanka ba ta maida hankali kan abinda ta keyi, Jidda ce ta maida hankalinta wurin Baaba tace.
"Wace matsaya kuma Baaba tunda ta rigada ta amince.?"
"Ai uban nasu yace nan da watanni biyu za'ayi bikin, shima Muhammadun ya kusa dawowa gida domin fara hidimar bikin." inji Baaba
"Lallai kice mu ma mu fara shiri kenan Baaba mun kusa zama amare." Jidda ta faÉ—a cike da zolaya.
"Sosai ma kuwa." FaÉ—in Baaba.
"Amma Yaya Sadiq zai dawo bikin koh.?"
"Ehh naji Sulaimanu na cewa sun gama karatun zaije da kanshi ya taho dashi, kinsan tunda yaji labarin rasuwar nan shima yake ta noƙe noƙen son cigaba da zama a cikin turawa."
"Gaskiya kam ya dawo bikin ƙanwa babu babban Yaya ai ba zaiyi armashi ba."
"A toh su daÉ—i su keji ganin kansu a tsakiyar arna suna shawagi."
"Kai Baaba bafa duka bane arna akwai musulmai sosai."
"Duk jirgi É—aya ya kwaso ku ai."
"Baaba watarana dai zamu kaiki ƙasar turawan nan kiji yadda akeji idan ana can."
"Allah ya tsareni ni Faɗimatu, bana fatan gani ko a mafarki na. Zara'u wani irin aiki ne kuke yi haka da baza ki bari kizo kiyi karin kumallo ba, ina fa lura dake kwana biyun nan sam bakyason cin abinci, shiyasa kike ta ƙarewa kamar kazar mayu." Ta ƙarashe maganar hankalinta na kan Zarah.
"Baaba ko kece kika tsinci kanki halin da take ciki baza ki samu nutsuwa ba sai kin kai ga ci." FaÉ—in Jidda
"Yoo wani hali ne take ciki banda na sama kanta damuwa sai an daina cin hanci a ƙasar nan, waɗanda suka fita ma sun gwada sun ƙyale."
"A'a fa Baaba case ɗin fyaɗe ne a hannunta kuma gobe za'a shiga kotu, shiyasa take ƙoƙarin tara duk wasu hujjoji gudun kada aka dasu, gashi dama iyayen yarinyar ba masu hali bane."
Salati Baaba ta shiga dokawa harda Æ´ar guntuwar kwalla kafin tace.
"Ashe har yanzu ana wannan rashin imanin a ƙasar nan, shikenan dai shi talaka bazai taɓa hutawa ba. Yanzu mene ne ribar yiwa mace fyaɗe, kawai saboda tsantar zalunci da son rugujewa mutum rayuwa. Insha Allahu duk asirin su saiya tuno an hukunta su, shiyasa nake son aikin Zara'u saboda gaskiyar ta. Nayi ma Muhammadu magana ma dole zai barta ta cigaba da aikinta saboda rashin ta zai iya saka al'umma cikin wani hali."
"Baaba ƙasar tamu yanzu ai sai dak kawai mu cigaba da addu'ar samun gyara, amma kullum lamura ƙara taɓarɓarewa suke yi."
"Kullum cikin addu'a muke kuma bazamu taɓa gajiya wa ba."
Nan suka cigaba da tattaunawa akan matsalolin dake addabar ƙasar ta mu har zuwa lokacin da su Saleem suka gama aikin suka dawo cikin falon aka cigaba da hirar da su.
Washe gari da wuri Zarah ta bar gidan bayan tayi sallama da su Jidda da zasu haÉ—u acan kotun.
Kotun ta cika maƙil saboda ba shari'a ɗaya ake gudanarwa ba, baya ga haka kuma abokan hamayyar Alhaji Mai Riga su ma sunzo dan ganin yadda zata kasance.
Shari'a biyu aka gudanar kafin azo kan case É—in Fahima.
Kamar kowace shari'a, lauyoyin sun hallara a inda aka tanadar musu domin zama. Nan aka umarci su gabatar da kansu.
"Suna na Bar. Labaran Ahmad tare da abokin aiki na Bar. Gideon Wangson mu ne masu kare wanda ake tuhuma." FaÉ—in É—aya daga cikin lauyoyi biyu dake zaune a inda aka tanadar musu.
"Shin Bar. Labaran bakai bane lauyan masu ƙara." Faɗin Alƙalin.
"Bani bane my lord." Inji Labaran.
Jinjina kai kawai alƙalin yayi kana yace.
"Ina lauyan masu ƙara."
Shiru babu amsa.
Alhaji Mai Riga ne ya kalli inda Zarah take tare da yin wani shu'umin murmushi mai cike da ma'anoni, ita ma murmushin ta maida masa mai alamar bakasan me kake yi ba. Kafin ya gama mamakin murmushin daya gani a fuskar ta ya jiyo sautin magana.
"Suna na Barrister Saleem Sa'ad ni ne lauyan masu ƙara, my lord ayimin haƙurin lattin da nayi hakan ya faru ne a sanadin cunkoson ababen hawa da na samu a hanya." cewar Saleem wanda shigowarsa kenan ya nufi gurin zaman lauyoyin.
"Bar. Saleem a kiyaye na gaba." cewar alƙalin.
Ba iya Alhaji Mai Riga bane ya shiga mamaki da ruÉ—un jin abinda ya fito daga bakin Saleem, hatta Labaran saida ya ruÉ—e domin dai ko kafin a fara gabatar da zaman kotun na yau sun tattauna da Zarah a matsayin shi na wanda zai tsayawa Fahima. Lallai ya tabbatar ta samu labarin zaiyi tawaye shiyasa ta tanadi wani lauyan.
Zufa ce ta fara keto masa ta kowani sashi ba jikinshi, É—agowa yayi jin alÆ™ali ya buÆ™aci su gabatar da shaidar su ta farko, sai dai me...............âœðŸ¼
*BY*
*Jasmine*🌸🌸
07048961623.
*ASSALAMU ALAIKUM*
*Uwargida da amarya har yanzu fa ƙofa buɗe take, zaki iya samun damar kasancewa da ni HAJIYA JAMILA SHARE KUKAN MATA a cikin zafafan darussan da nake gabatarwa a ASP ZARAH SPECIAL FANS GROUP, domin samun dabarun zama da miji, ɓoyayyun sirrikan da zakiyi amfani da su wajen mallake mijinki cikin sauƙi, tare da sahihan kayan gyara na musamman sha yanzu magani yanzu. Kada ki bari ƴar uwarki ta labarta miki.*
*Cikin ikon Allah a ƙanƙanin lokaci group ɗin mu na farko ya cika kuma yanzu haka mun buɗe wani sabon group ɗin ga masu buƙatar su shiga a baje wannan kolin dasu. Kada kumanta dai zaku iya samun damar shiga wannan group ta hanyar tuntuɓar wannan number 07048961623. Ina jiran zuwanku, ni ce dai takun da bani da tamka HAJIYA JAMILA SHARE KUKAN MATA*.
*ASP ZARAH*👩â€âœˆï¸
_Paid book_.
_Domin samun damar cigaba da karantawa batare da É—aukarwa kai alhaki ba ki/ka biya N300 kacal na normal group, VIP group kuma N500 amma dan Allah idan so samu ne karki biya VIP idan baki da aure saboda darussan da ake gabatarwa a ciki. Za'a turo kuÉ—i ta wannan asusun 0153109156 Union Bank, sannan a turo shaidar biya ta 07048961623.
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Zarah ya gani ta kafe shi da idanunta masu rikitarwa, nan take ya ruÉ—e har saida yaji Gideon na gabatar da tambayoyi ga Kabeer kafin ya maida hankali.