← Book details Ajiya A Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 148

Sashe 95

Ajiya A Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖6️⃣1️⃣

______________

.........Wannan karon ma dai Giro suka koma suna, sai dai babu wanda ya nuna murna da wannan haihuwa kamar ta Amaal daga Baba Haruna sai uban jegon sai kuma su Shahidah dake murna an haifa musu ƙanwa. Wannan karon dai Gwaggo babu damar aibanta yarinya tunda tana kama da ubanta a abubuwa da dama. Amma hakan bai hana sako batun haihuwar ɗa namiji ba data fahimci yana tasiri a zuciyar ɗan nata. Haka dai akai bikin sunan babu wani armashi sosai sukai shirin komawa Sokoto amma sai Gwaggo ta hana wai su zauna anan suyi wankan jego. Ganin yanda bata kawo tashin hankali ba a sunan yada baba Haruna tunanin ta sauya ne. Dan yanzu ta ɗan rage wasu abubuwan a zahirance saboda tsoron kada ta tsinke ƴar sauran igiyar ɗaya dake a tsakaninsu. Ta koma zuba rashin mutuncinta ta ƙasa, dan Habib ta koma takuramawa akan sai ya ƙara aure, ita kuma Asiya ana mata a kaikaice.
     Shima dai Habib wannan karon bai damu ba ya barsu anan ya kuma yarda da batun ƙara aure, dan ya samu damar sheƙe ayarsa da sabuwar karuwarsa da suka haɗu anan Sokoto ɗin kwanan nan. Zama kamar wasa ya nema zama gaske. Dan bayan gama wankan jegon Maanal Habib bashi da niyyar cewa su shirya komawa Sokoto, sai dai yana zuwa duk ƙarshen wata yay musu weekend ya koma. A haka aka tado batun aurensa. Auren daya bama kowa mamaki ya kuma saka Ammie a tashin hankali. Amma sai Baba Haruna ya dinga kwantar mata da hankali da nasiha ta sakama kanta dangana kuwa ta rungumi ƴaƴanta. Cikin ƙanƙanin lokaci akasha biki kuwa, yarinya ƙarama da bata wuce shekara sha bakwai ba. Inda Ammie ta burge kowa shine tattara komai ta watsar kamar ma ba ita akama kishiyar ba. Sai shima kansa Habib ɗin ya dinga kiyaye duk wani abu da zai taɓa mata zuciya ba kamar yanda Gwaggo taso ba. Itama yarinya da aka ɗoro akan rashin kunya da zata dinga yima Ammie sai ta dinga jin shakkarta. Abinda ya ragema amarya armashi samunta ba'a cikakkiyar mace da Habib yayi ba, dan tun a daren farko sai da tasha maruka a wajensa a ɗaki batare da sanin kowa ba. Ko sati kuma bai cika ba na amarci ya tattara ya koma wajen aiki. Aiko akaita gutsiri tsoma wai Ammie ce tayi wani abu, dan Gwaggo har ɗaki ta sameta ta mata wankin babban bargo. Ita dai batace komai ba. Habib bai zo gida ba sai da yay wata guda kamar yanda ya saba, ya kuma murje idonsa ya sauka ɗakin Ammie, itako tanata roƙonsa bai kulata ba, ana cikin haka sai ga Gwaggo har ɗaki, tas taima Ammie da zaginta akan muna fuka ta tasa ɗanta gaba har ɗakin amarya Sailu. Ai ko ranar ma maimakon ta samu kulawa a wajensa sai duka taci a banza, dan ya fahimci bata da kunya, Habib kuwa irin mazan nan ne da basa ɗaukar raini, shi hatta macen bariki tai masa hauka duka take ci a wajensa, Ammie ce kaɗai ta tsira da irin wannan halin nasa, duk da yana shan marinta itama a wasu lokutan. To ataƙaice dai wannan aure bai rufa wata biyar ba a wani zuwa ya saki Sailuba saki har uku. Nan fa gari ta ɗauka Ammie ce ta koreta. Babu kalar abunda Ammie bata gani ba akan wannan rabuwar auren amarya da mijinta, ƴan gidan suka kara tsananta, na Gwaggo kam ai ba'a magana. Ga Habib bashi da niyyar cewa su shirya subar garin har sai da Maanal ta shiga shekara ɗaya da rabi sannan akaima Habib transfer zuwa Kano. Aiko Baba Haruna da'a yanzu ya fahimci Habib na neman matan banza yace ya tattara matarsa da iyalansa su wuce tare. Gwaggo ta nuna bata yarda ba, Baba Haruna ya nuna mata shima bata isa ba. Kamar Habib baya so haka ya wuce da su Ammie Kano, dan yasan an rage masa jin daɗinsa ne kawai. Anan ya samu gida ya kama musu haya, daga baya kuma ya saye shi da kuɗin Ammie na gado, shine dalilin komawarsu da zama garin Kano. Tunda suka koma kuma basu sake zuwa Giro ba sai dai shi yazo sau uku sai yanzu shekara kusan shidda kenan dan tun Maanal nada shekara ɗaya da wasu watanni da kaɗan ya rage sukai biyu. Ita dam bata san Giro ba bata san ƴan Giro ba....

________★★★
Chapter 95 · 0% Book details