← Book details Ajiya A Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 148

Sashe 100

Ajiya A Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

       Alhamdullah su Aba sun iso Kano lafiya. Duk da a lokacin anata shirin shiga sallar isha'i ne. Dan basu baro Sokoto ba sai da akai magrib. ALLAH ne ya taimake su suka samu jirgi mai zuwa Kano a daidai lokacin. Tuni Maanal tayi barci a jirgi, dole Ajwaad ya goyota suka fito tana a bayansa, sai Aba riƙe da ledar tsarabarsu dan ma sunƙi ɗakko kayan da yawa. Dan dama jirgi suka bi da zasu je. A sokoton ne abokinsa kuma ɗan uwansa ƙanin Oum amma cousin da suka fara sauka a gidansa ya bada mota driver ya kaisu Giro dan shi anan Sokoto yake zaune da iyalinsa. Aiki ne ya cillarosa nan kuma.
     Alhamdullah nan ma sun samu babban yaya (Fadeel) da drivern dake kaisu school na jiransu a airport ɗin.  Yana hangosu yay saurin nufosu, shima baida yawan fara'a, dan halinsu kusan ɗaya da Ajwaad. A fuska ma sunfi kamanni, duk da dai su duka ukun suna tsananin kamanni da Abba da Oum, kasancewar su ɗin iyayen nasu aurene na zuminci, zumuncin ma na kusa kusa sosai, shiyyasa suke kamanni ɗaya, dan duk family ɗinsu haka suke da wannan kamannin. Su har alfahari suke indai ɗa na tsatsonsu ne koda an auro uwarsa bare baya ɗakko kamanninta sai nasu saboda ƙarfin jininsu. Koda Babban yaya ya gaishe da Aba ya maida hankalinsa akan Ajwaad da son taimaka masa ya amshi Maanal ɗin dake bayansa kansa ya girgiza alamar ya barta.
    Hakan ya saka Babban yaya da Aban yin murmushi kawai. A haka suka ɗinguma zuwa ga mota. Driver ya gaida Abba cike da girmamawa sannan suka shiga, Abba da Ajwaad da Maanal dake barci a kusan jikinsu su biyun na baya. Shi kuma babban Yaya ya shiga gaba kusa da driver. Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso gida, inda suka samu tarba daga Oum da Mamy da Fawzan. Sai dai Oum tayi mamakin ganin harda Maanal, dan batai tunanin zasu bari a taho da itan ba kamar yanda Ajwaad ke faɗin da ita zai dawo gida. Mamy dai bata tanka ba, dama kuma babu wanda yay tunanin tankawar tata dan dama haka take ita shiru-shiru. Ba komai ne zakaji bakinta a gidan ba. Garama idan suna hira da Oum ko Aba zaka jita cike da nishaɗi kamar ba ita ba. Amma akan yaran babu ruwanta da sabgarsu. Sosai take nuna kawaici da kara bama zaka taɓa tunanin tana da wata alaƙa da su ba...
       Ɗakin Oum Ajwaad ya kai Maanal, Oum ta taimaka masa ya kwantar da ita bisa gado. Kwanciya ta gyara mata da rufa mata duvet dan ɗakin akwai ac. Batare daya zauna ba ya ce, “Oum naje wanka, jikina duk babu daɗi”.
    Murmushi Oum ta masa, dan kowa yasan Ajwaad da tsaftar tsiya dama a gidan. Idan yana wani ƙalƙalin saika rantse ba yaro bane ƙarami ɗan shekara sha... Komai nashi zaka samesa kwaf-kwaf da kulawa kamar wani babban saurayi maji ƙarfi. Idan Ajwaad yay ado dole ka tsaya kallonsa. Sam bai damu da manyan kaya irin namu na malam bahaushe ba. Dan duk juma'a ma sai ankai ruwa rana da shi yake yarda ya saka. Garama idan Maanal ta saka masa rigima ta ɗakko da kanta tace ya saka sai ya saka. Dan duk da baya so Aba bai taɓa tsamesa a ɗinkin manyan kaya ba. Yanda akema su Fawzan da Babban yaya haka shima ake masa su, shiyyasa ya tarasu tab wadrobe yana ado dasu.
       Yana shiga ɗakin nasu Fawzan Sarkin tsokala ya fara tsokanarsa da dariya. “Ah-ah kaga baban soyayya, kaga Auta na Auta, Besty kuma na Besty. Wai yanzu nan dan ALLAH ko kunya baka ji ba Auta kaje gidan surukai ka ɗakko Lilly? Oh kai wannan wane kalar abin kunya ne haka?”.
     Harara ya ballama Fawzan ɗin yana wucewarsa bayi batare da ya tanka masa ba. Aiko Fawzan ya shiga kwasar dariya har sai da Babban yaya ya shigo ya tsagaita. Koda ya maimaita na Babban yaya dalilin dariyar daya tambaya murmushi kawai yayi shima, dan shi kansa soyayyar autan nasu da Bestynsa na ƙayatar da shi, da. Haka yana musu fata da addu'ar ɗorewa a haka har girma su kuma kasance ma'aurata kamar yanda kowa ke tofa albarkacin bakinsa akan dangantakar tasu.........✍️

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖6️⃣4️⃣

______________

.........Duk suna a d/table suna dinner Maanal ta fito tana faman murzar ido alamar yanzu ta tashi. Fawzan ne ya fara ganinta. Dan haka cike da shaƙiyanci ya furta, “Oyoyo Bestyn Auta, bada kanki a sare kije gida kice ya faɗi. Kaga surukar Oum da Abah”.
     Daina susan idon Maanal tayi ta tsaya tana kallon sa da farko kamar mai mamakin ganin kanta a nan ɗin. Yayinda suma duk suka zubo mata ido suna kallonta musamman Ajwaad. Oum kuwa da Abah murmushi suke yi, hakama babban yaya. Mamy kuwa kamar bata a wajen abincinta kawai take famar ci. Hannu Oum ɗin ta miƙo mata alamar tazo gareta. Da gudu kuwa ta iso ta shige jikin Oum ɗin, sai kuma ta saki kukan shagwaɓa.
        Shi ko Fawzan ya wani tuntsure da dariya yana faɗin, “Oh oh yau naga ikon rabbu surukar Oum shagwaɓaɓɓiya kenan, an dawo zakuma a ɗaura daga inda aka tsaya ko”.
      Rankwashi Oum ta kai masa sakamakon ɗagowar da Maanal tayi cike da taɓara da tsiwa ta ce, “Oum kinga Yaya F ko, kice ya daina ni Babynki ce ya bar cewa suruka bana son sunan”. Yanda tayi ɗin sai da ya bama kowa dariya. Dan shi kansa Bestien nata wani guntun murmushi ya saki kawai ya cigaba da kallonta. Ita ko ta cika tayi fam dan duk zatonta ma surukar wani mugun sunane da ake gudu. Gwalo Fawzan ya mata da faɗin, “Anƙi a daina ɗin, da wani bakinta kamar na tsuntsu”.
      Kuka sosai ta buɗe baki zata sanya, Abah ya saka hannu ya ɗauketa cak yana hararar Fawzan. “Kinga ƙyalesa kinji babyn Oum ɗinta. Kin san dama shi bashi da aiki sai neman faɗa da mutane in dai Fawzan ne. Shiyyasa ma bazanje da shi saudia ba sai ke da bestyn ki kawai”.
    Cike da farin ciki Maanal taima Fawzan gwalo da harara. Sai kuma ta hau murna za'aje dasu saudia ita da Bestyn ta. Da wannan lallashin Abah ya kashe rigimar, ya saka mata spoon a abincinsa sukaci tare...
Chapter 100 · 0% Book details