← Book details Ajiya A Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 148

Sashe 80

Ajiya A Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

         Sosai kasancewar su Oum a asibitin ya ɗan ragema Maanal nauyin da zuciyarta tayi. Dan ma hankalin Oum ɗin ya rabu biyu saboda AA. Dan shi ma bayan Doctor ya dubashi sosai sun ɗan kwantar da shi amma yace na yini ɗayan ne kawai. A wannan yanayin Shahidah ta iso asibitin ta samesu. Tayi farin cikin ganin Oum sosai. Kasancewar an hana kowa zama a ɗakin da AA yake dan suna son ya samu barci sosai duk sai suka tare anan ɗakin Maanal ɗin. Sai bayan sallar azhar da AA ya farka Oum ta nufi can. A lokacin ita kuma Maanal ta samu sallama. Koda suka gama tattare kaya zuwa mota Shahidah tasa Maanal gaba tai domin duba AA. Bata so hakan ba, sai dai bazata iya musu da Didinta ɗin ba. Musamman daya kasance RK na tare da su ne.
          RK ne ya fara shiga bayan yayi knocking an bashi izinin shiga. Sai Maanal, Shahidah a ƙarshe. Oum na zaune a kujera, shi kuma AA na kan gadon ya jingina da filo Oum zata fara bashi abinci a baki, sai faman ɓata fuska yake alamar baya son cin abincin ko kuma duk ciwon ne oho masa. Plate ɗin abincin Oum ta ajiye tana kamo hannun Maanal da faɗin, “Masha ALLAHU ƴan matana anyi sallamar dai?”.
          Kai Maanal ɗin ta jinjina mata a ɗan shagwaɓe. Ita kuma tayi murmushi da faɗin, “To Alhamdullah, ALLAH ya ƙara lafiya yasa kaffara ne.”
      Amin RK da Shahidah suka amsa da shi, kafin Shahidah ta maida hankalinta ga AA daketa kallonta. Duk da yasan dama zai iya ganin nata, amma sosai mamakinsa ya bayyana amma ya gagara iya cewa komai. Wannan ba komai bane daga halayensa, dan haka Shahidah bata damu ba, sai dai zafinsa da suke ji tun na shekarun baya akan ƴar uwarsu taji yana taso mata. Komai dawo mata yake kamar yanzu ne yake faruwa. Da ƙyar ta iya dannewa ta tambayesa jikinsa. Karan farko yay ɗan murmusa, irin guntun murmushin nan mai tabbatar da ƙunar zuciya. Tabbas yaga tsanarsa a bayyane akan fuskar Shahidah, hakan na nufi har yanzu suma basu mance komai ba, basu mance abinda ya faru ba suna riƙe da shi a ransu fiye ma da Maanal. Baiga laifinsu ba, dan ko shine hakan zai yi, amma inama zasu fahimcesa kamar yanda Oum ta fahimcesa bayan ya zauna da it.....
        Maganar RK ce ta katse masa tunaninsa, ya ɗan kallesa sai kuma ya janye idanunsa yana jinjina masa kai. Baya son sakama ransa tsanar ɗan uwansa kodan daraja da kimar Oum, amma tabbas zafinsa yake ji, kishinsa yake ji mai tsanani akan Maanal. Ta yanda ya gwammaci ya dinga masa shiru akan abubuwa da dama fiye da yin magana.
     Sai yanzu Maanal da tunda tai masa kallo ɗaya bata ƙara ba ta furta, “Ya jiki?”. Daga haka tai shiru. Shima sai bai amsa ba, ya dai ɗago idanunsa ya kalleta kawai. Yana ƙoƙarin janyewa akai knocking ƙofar. Shahidah ce ta amsa sannan ta bada izinin shigowa. A hankali aka turo ƙofar, yana sanye cikin lallausan farin yadi da yay masa matuƙar ƙyawu, sosai kamanninsa da AA ke a bayyane, ta fuska da ɗabi'u. Sai a shekaru ne kawai suka banbanta da hasken fata. Ɗan ja yay ya tsaya turus yana kallon Shahidah da itama take kallonsa, sai kuma tai saurin kauda idonta. Shima janyewa yay ya maida ga Oum, sai kuma ya sake waresu akan Maanal da itama take kallonsa. Cikin kasa daurewa ya ce, “Oum kinga mi nake gani?”.
     Murmushi sosai Oum ta saki mai ciwo, sai kuma ta jinjina kanta da faɗin, “Na sani Fadeel. Shahidah ce da Lillyn ka”.
     “Wai da gaske ne kenan?”.
   Yanzu kam har sai da hakwaran Oum suka bayyana a waje, sai kuma hawaye suka ciko mata idanunta. Da ƙyar dai ta iya dannewa ta sake bashi amsa........✍️

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖5️⃣1️⃣

______________
Chapter 80 · 0% Book details