Sashe 84
Ajiya A Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
........A ɓangaren Maanal kuwa bayan fitar Shahidah text ta turama RK dan tana son su ƙarasa maganar da suka fara. Ko minti biyu ba'a cikaba kuwa da tura saƙon sai ga kiransa ya shigo. Kamar bazata ɗauka ba ta dai daure ta ɗaga ɗin tare da saka hans free kawai. Sallama tai masa da sassanyar muryarta da a yau rauninta ya sake fita fili. Shima sai ya amsa mata da tashi sassanyar muryar. Tare da faɗin, “Gani a compound ɗin ku”.
Sosai mamaki ya kama Maanal, harta kasa ɓoyewa sai da ta furta, “Wasa kake amma?”.
Murmushi yayi mai sautin da har taji, “Da gaske nake my queen, dama ina gidan kusan minti goma kenan bana son takura miki ne kawai, harma ina shirin juyawa sai kuma ga saƙonki”.
Ajiyar zuciya Maanal ta sauke, zuciyarta na sake ƙarfafata akan RK ɗin. Tabbas bata buƙatar yin rayuwar aure da kowa. Hasalima bata da burin yin auren kwata-kwata. Amma tasan iyayenta da ƴan uwanta bazasu bari ba. Sai kuma Ajwaad, dole ne ta tabbatar masa da abinda yake ganin bazata iya ba. Zatai auren a cikin zuri'arsa kodan tabbatar masa da wannan Maanal ɗin ta yanzu tafa banbanta da wadda ya sani a baya. Miƙewa kawai tayi ta ɗan gyara hijjab ɗinta na salla da har yanzu bata cire ba, sai ɗan turare data ƙarama jikinta ta fita. Babu kowa a falon dan su Barrah na tare da Abbansu basu dawo gidan ba. Kitchen ta shiga ta ɗauka ruwa a tray da glass cup. A karo na farko ta nufi falon baƙi sannan ta fita compound inda RK yake. Iso tai masa zuwa falon baƙin, hakan sai ya sake bashi mamaki sai dai baice komai ba ya bita.
Koda suka shiga ita ta zuba masa ruwa da kanta sannan ta zauna. A karan farko da yaji ya kasa daurewa ya furta, “Gaba ɗaya sai mamaki kike bani. Gani nake kamar bake ba”.
Guntun murmushi kawai Maanal tai masa. Sai kuma ta kallesa. “Idan kiɗa ya canja itama rawar canjawa take yi ai. Ina son ka san yanzu muna akan gaɓar serious ne”.
“Hakane. Nima hakan nafi so mu kasance ɗin Maanal. Na kuma ji daɗi da godema ALLAH daya kawo mu wannan gaɓar ɗin.”
A hankali ta haɗiye ƴan kwallar data ciko idanunta. “Ɗazun mun fara magana sai dai bamu ƙarasa ba, shiyya nace kazo yanzu dan in sha ALLAHU kamar yanda na sanar maka gobe zan wuce Kaduna.” batare da jiran amsarsa ba ta miƙa masa diary ɗin data shigo da shi a cikin wata kyakkyawar bag. Amsa yay yana ciro sa daga jakan, sai kuma ya ɗan jujjuya shi a cikin hannunsa sannan ya ɗago ya kalleta. Itama shi take kallo, dan haka ta janye nata idanun.
“Na yarda da kai fiye da yanda kake zato. Badan komai ba sai dan wasu dalilai. Sannan kai ɗin koba komai jinin Oum ne. Wadda nake kallo uwa nagartacciya bayan mahaifiyata. Kaje da wannan zaka samu dukkan tarihin rayuwata data shuɗe a ciki, dan in har akwai abinda na rage ban rubuta ba to zai kasance ƙalilan ne, ko kuma baida muhimmanci. Bayan ka gama karantawa zaka iya sake tun-tuɓar Oum dan sake samun gamsuwa. Daga nan sai ka yanke dukkan hukuncin daya dace koyaya ne zan amshe shi. Dan ALLAH in har baka gama karanta shi har ƙarshe ba kada ka kirani a waya, kada kazo kaduna.” daga haka ta miƙe tsaye, shi dai kallonta kawai yace yama rasa abin cewa.
“Dare ya farayi sai da safe”
A karo na farko ya ɗan ja numfashi ya fesar, sai kuma ya jinjina mata nasa kan yana miƙewar shima. Haka suka fito a tare kamar wasu kurame. Dai-dai nan motar Abdull ke shigowa gidan. Duk tsayawa sukai suna kallon motar har wanda ke ciki suka gama fitowa. Da mamaki RK ya furta, “Abdul-hakeem”. Sai kuma ya juya yana kallon Maanal. Itama shi ɗin ta kalla, tare da faɗin, “Ka sanshi ne?”.
Kafin ya bata amsa Yaseerah ta fito da Huznah, fuska duk facin bandage musamman ɓarinta na dama. Nufarsu RK yayi, dan haka badan taso ba itama tabi bayansa. Duk da Abdull yayi mamakin ganin RK a gidan sai ya danne, sai da suka gaisa RK yake tambayar abinda ke faruwa idonsa akan Huznah. Bayani Abdull yay masa a taƙaice. Kamar RK ɗin zai yi magana sai kuma ya fasa ya juya yana kallon Maanal.
“Inaga ni bara naje, ki musu iso ciki ko?”.
Kai kawai Maanal ta jinjina masa, sai kuma tai masa ALLAH ya kiyaye hanya tai gaba abinta batare da tace ma su Yaseerah komai ba.. Suma komai basu ce ɗin ba suka bita kawai, yayinda Abdull yake ta satan kallon Maanal ɗin. A ransa yana raya aji da nutsuwar yarinyar, gata ƙyaƙyƙyawa da wani skin nata mai ɗaukar hankali da yay ƙaranci ga matan wannan zamanin da suka maida kansu fararen dole da bleaching.....
Gaba ɗaya Shahidah kasa cewa komai tai da bayanin Abdull ɗin. Dan Yaseerah taso su ɓoye amma Abdull ya kware zance ga mijin Shahidah abinsa, dan shi dai namiji ne babu ruwansa. Godiya sukai musu, suma suka miƙe suna musu sallama dan dare ya fara. Dama ita Maanal bama ta tsaya a falon ba ganin kallon ƙurullar da Abdull ɗin ke mata a kaikaice duk da kuwa hijjab ne a jikinta har ƙasa. Ko bayan wucewarsu da Huznah ta shigo ɗakin Maanal bata kulata ba, tanata ma haɗa ƴan abubuwan da zata wuce da su Kaduna ne kawai. Itama Huznah ɗin bata kulata ba tai kiran mamanta a waya. Basu wani jimaba sukai sallama dan ta sanar mata ne kawai zata dawo Kaduna gobe....
_______________★
A Kaduna kam kamar yanda Daddy ya faɗa sunje Kebbi garin Giro asalin tushen su Maanal. Sai dai an samu saɓani tsakaninsu da manyan da ya kamata su gana da su. Dan kuwa an tabbatar musu kakarta da babanta da baffanta sunje Kaduna, wani kuma babban Senator ne ya aiko aka ɗaukesu a mota wai zasuje wajen Asiya daya tabbatar musu yasan a inda take.
Rasama abin faɗa Daddy yay, Dan ya rasa yanda zai fassara zancen musamman akan batun senator da suka ce. Haka dole suka baro garin gwiwa a sage. Basu iso gida ba sai dare, zuwa lokacin kuma kowa yay barci, sai dai hakan bai hanashi zuwa ya sami Ammie a sashensa ba tana jiransa. A kallo ɗaya da yay mata ya fahimci hankalinta a matuƙar tashe yake kuma.......
___________★
Washe gari Shahidah, Maanal, Huznah da yara suka tashi da shirin wucewa Kaduna. Dan yaran ma babansu yaje school ɗinsu ya daidaita komai. Jirgin ƙasa zasu bi, dan haka Uncle Sadeeq ɗin da kansa ya kaisu train station bayan sallar zuhur. Basuyi ko mintuna goma ba suka wuce. Koda suka iso Kaduna Amaal ce tazo ɗaukarsu. Dan ita kaɗai tasan da zuwan nasu sai Hajiya Basariyya. Itama saboda Huzna ne ta sani ɗin.