← Book details Ajiya A Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 148

Sashe 102

Ajiya A Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖6️⃣5️⃣

______________

.......Abah bai samu zama da su Oum ba sai daren yau akan batun daya faru a Giro. Komai bai ɓoye musu ba daya faru A to Z har hukuncin daya yanke akan Fadeel da Fawzan. Sosai tausayin Ammie ya sake baibaye Oum. Dan tamkar ƙanwa uwa ɗaya take jin Ammie a ranta ba maƙwafciya kawai ba. Ɗari bisa ɗari kuma ta bada goyon baya ga hukuncin mijin nasu. Ta kuma yabama dattakonsa. Itama dai Mamy ta jimanta al'amarin ƙwarai da gaske. Akan batun yara kuwa ta nuna kawaici kamar yanda ta saba. Daga ƙarshe ma miƙewa tai tana faɗin, “Wannan maganarku ce Oum, mu ƴan ALLAH ya sanya alkairi ne”. Daga haka ta fice tabar falon.
       Da kallo duk suka bita. Kowanne na sake jin ƙaunarta a cikin ransa daga Oum ɗin har Abah. Mamy abar alfahari ce a garesu, dan suna matuƙar alfaharin shigo da ita cikinsu. Tana da wasu irin nagartattun halaye masu matuƙar ƙayatarwa a zahiri. Oum da Abah sun cigaba da tattaunawa, kafin suma su miƙe bayan sun gama yanke yanda zasu fahimtar da yaran nasu batare da sunga an ƙasƙantar da su Shahidah a idanunsu ba.

      A ɓagaren Mamy kuwa koda ta shiga ɗakinta kasa tsaye da zaune tayi. Ta jima a haka kafin ta ɗauka waya tayi kira. Ba'a wani jimaba kuwa aka ɗaga. Sallama tayi tana kaiwa zaune. Sai kuma ta ɗora da gaisuwa.
       “Yaya mutanen nan ban san mi suke so dani ba. Shike nan ni bani da wani ƙarfin iko akan ƴaƴana ma. Daga mijin har matar kamar tare suka auro ni? Nifa na fara kaiwa gaɓar da zan nuna ma matar nan ina buƙatar ƴaƴana nima. Sai dai ya sakan ko itama tayi zuciya ta haifi nata.......” kuka ya sarƙeta.
     Numfashi aka sauke mai nauyi daga can, kafin cikin isa a furta, “Kamila! Dama wannan shine abinda aka dinga guje miki tun farko. Amma kika kasa fahimta soyayyar mutumin nan ta rufe miki idanu. Daga baya aka sake nusar dake illar sakar mata yaran nan tun suna zanin goyo nan ma kika kasa fahimta ke wai neman soyayyar miji. Ai gashi nan, ƴaƴan da mijin duk suna a hannunta ke baki amfanu da komai ba sai baƙin ciki da damuwa. Kin san wacece Hajiya Fateema kuwa akan mijin nan nata? Dukkan fa bincike sai da nayi a kansu. Akwai matsananciyar soyayya da shaƙuwa a tsakaninsu tun ta ƙuruciya. Tun fa tana ƴar shekara goma sha a duniya aka aura masa ita. Shi ya raineta, gida ɗaya suka tashi, shi ya koya mata komai taya dama kike tunanin zaki shiga wannan gidan ki samu farin ciki? Haihuwa da kike ganin bazatayi ba? Humm irin su Alhaji Aliyu Darma da kike gani ba wannan bane a gabansu....”
        “Yaya ni dai naji. Koma minene dai ya riga ya faru ai. Kawai yanzu ina buƙatar dawo da yarana hannuna kota ƙarfin tsiya. Musamman Ajwaad. Wlhy yaron nan yi yake tamkar ma bai san muna da alaƙa ba. Har tayata kishi yake fa. Dan ALLAH ki taimkeni”.
       “Hummm ai wannan yaron taƙadari ne daga gani. Kuma ba kowa ya busar masa da zuciya ba sai ita. Ga shegiyar yarinyar nan da suke ƙalatar juna ƴar maƙwaftanku, kai na tsani yarinyar nan da uwarta wlhy saboda aminiyar Fateema ce”.
      “Wlhy Yaya na fiki tsanar Asiya. Dan haka koma mi za'ayi sai dai ayin wannan haɗin auren bazai yiyu ba. Sai kace ma ita na haifamin ƴaƴan kenan”.
      “A da'alama kam ita ɗin kika haifamawa. Ba kuma makircin kowa bane sai na Hajiya Fateeman. Kinga idan yaran sun auri ƴaƴan Asiyar ai itace zata cigaba da juyasu ko. Ke wannan fa ƙulline babba wlhy. Amma karki damu zamuyi maganinsu. Kizo ki sameni gobe”.
      “Aunty sai dai weekend. Dan yanzu ina cemasa zan fita zai iya zargin wani abu kin dai sanshi da kaifin tunani. Amma weekend zan tambayesa zuwa kitso sai na zo”.
        “To hakan ma yayi ALLAH ya kaimu. Kidai kwantar da hankalinki”.
    “Humm Yaya kenan, amma in sha ALLAHU zan yi ƙoƙari sai anjima”....

___________★

       SU WAYE SU OUM?.
Chapter 102 · 0% Book details