← Book details Ajiya A Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 148

Sashe 48

Ajiya A Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

     Yau ma Shahidah ce ta ajiyeta a office sannan ta wuce nata aikin, tun a harabar companyn suke gaisawa da mutane har ta shigo. Dama dai tsakaninta da kowa gaisuwar ce, rashin yawan fara'arta da yawan magana ma kesa mafi yawansu ke kiranta da sunan mai girman kai. Ƴan rukuninsu mutum uku ne kawai sukazo, ta gaisa da su taja kujerarta ta zauna. Dama ita kaɗaice mace a cikinsu, shiyayasa daga gaisuwa sai zancen aiki ke haɗata da su. ALLAH kuma ya taimaketa kujerarta itace farkon shigowa, suma ganin yanda take haɗe fuska da kame kanta yasa suke shakkar shige mata duk da wasunsu na kwaɗayin hakan tun ma a ran farko da tazo. Aikinta ta kamayi kawai kamar yanda ta saba, a haka sauran suka iso, kowa yazo zata ɗago su gaisa daga haka ta maida kanta ga aikinta. Kusan eleven ta tashi zuwa office ɗin Director Mustapha. Duk da kallo suka bita, wanda ke zama kusa da ita cikin yin ƙasa da murya yace ma na kusa da shi, “Wato yarinyar nan akwai girman kai wlhy Ema..”.
     Caraf Yaqub da ke facing ɗinsa ya ce, “Ba wani girman kai wlhy, ta dai san kanta ne. Idan mace ta cika faran-faran ace ma ballagaza, idan ta kame kanta ace girman kai. Kufa lura ita kamar yanayintane ma haka, miskila ce kawai”.
     “Tab ai ni kuma bana son miskilar mace gaskiya. Ita mace ko yaya da sauƙin kai tafi daɗin rayuwa”.
    “A wajenka ba.....”
“Oh to kodai santa kake yine wai Yakub”.
       “To laifi ne idan na sota Zaharadeen, naga dai namiji ne ni. Kuma ɗin inda zata amsa muku son nata kuke shiyyasa kuke gulmarta. Yarinya na girmamaku amma bakwa gani. Yanzu da sakewa take cikinmu da surutu da fara'a sai kuma ace ta saki kanta a tsakkiyar maza. Ta kuma kama kanta kunzo kunayi da ita mtsooww!”.
    Ya miƙe ya bar musu wajen. Duk da kallo suka bisa, sai kuma suka kalla juna cikin yamutse fuska. “Wannan guy ɗin na kula fa son yarinyar nan yake”.
       “Oh kai sai yau ka gane, ai na jima da fahimtar hakan. Kuma banga laifinsa ba dan koni ALLAH na ƙyasa”.
     Dariya suka sanya a tare harda tafawa.

    Maanal kam da bata ma san sunai ba kanta tsaye office ɗin Designer Director Mustapha ta nufa. Tana shiga Elevator massage ya shigo wayarta, ƙoƙarin dubawa ta fara yi sai taga Yazeed ne. Nutsuwa tai a karanta saƙon, sai ya zam har elevator ɗin ta tsaya hankalinta nakan wayar, a haka tai ƙoƙarin fitowa batare da duban gabanta ba. A dai-dai lokacin da CEO AA Darma ke isowa ga elevator ɗin Assistant ɗinsa biye da shi. Ya riga ya kawo jiki, kamar yanda itama ta riga ta taho gashi hankalinta ba a wajen yake ba balle taja da baya kawai sai jitai ta bugi abu. A ɗan razane tayi baya, wayarta ta suɓuce ƙasa hakama gilashin idanunta da document ɗin duk suka tarwatse kasa.
     Sosai ta ɗago cikin ɓacin rai dan ganin wanene da wannan aikin bayan ta gama bin kayan da kallo ɗaya bayan ɗaya. Shima sai hakan ya zam dai-dai da tashi ɗagowar bayan ya gama bin kayan da kallo musamman zanen agogon da yay masifar ɗaukar hankalinsa. Wani kalar zubama juna ido sukai kowanne fuskarsa a matuƙar tamke, sai dai na Maanal ɗin ya ɗan cika da ruwan hawaye dan har ƙyallinsu ya nuna. Yanda tai masa ƙiri da idanu sai ka ɗauka zata fara zazzaga masa ruwan bala'i ne, dan tuni AS ɗinsa da wasu da suka zo wajen bayan faruwar accident ɗin duk sunyi kasare cikin ɗunbin mamaki suna son suga mizai faru. Amma mi, a mamakin kowa sai suka ji cikin sanyin murya Maanal ɗin ta furta,
      “I'm sorry Sir”.
    Ta ƙare maganar da rissinar da idanunta harma da kanta cikin nuna girmamawa. Shi kansa wani irin rumtse idanu yay da masifar ƙarfi, sai kuma ya zagayeta ya shige cikin elventor ɗin batare da yace komai ba. Wannan abu ya bama kowa mamaki, hatta da AS ɗinsa daya gama tattaro ma Maanal kayayyakinta. Wannan shine abu na biyu daya faru tsakanin Boss da Maanal ko yace na uku harda kaita gida da sukai jiya. Shi sai ma ya rasa kalar tunanin da zai yi akan al'amarin.
     Sauran ma duk sun ma Maanal sorry, kanta kawai ta jinjina musu da ɗan yin murmushi ta wuce zuwa office ɗin Director Mustapha. Bayan tayi knocking aka bata iznin shiga. Ta gaishesa da girmamawa kamar yanda ta saba yima kowa. Shiko ya amsa fuskarsa da murmushi tare da nuna mata kujera. Kanta ta ɗan girgiza masa da ajiye document ɗin hannunta saman desk ɗinsa.
       “Sir dama na kammala ne shiyyasa nace bara na kawo maka sai ka duba”.
     “Yauwa sister Maanal dama kamar kin san yanzu nake shirin nemo ki, dan ban jima da baro office ɗin CEO ba akan batun. Woow ai sai naga ma kamar waɗan nan sunfi ma wancan ɗin ƙyau”.
      Ita dai Maanal komai batace da shi ba kanta a ƙasa, sai da ya gama santinsa sannan ya sallameta akan ta zama cikin shiri koyaushe za'a iya nemansa a conference room. Koda ta koma saita samu har gulmar abinda ya faru tsakaninta da CEO ɗin taje can. Dan ta wuce wasune nayi batare da su sun farga da ita ba. Kowa bata kula ba har abokan zamanta da wasu ke ɗan ƙus-ƙus ta zauna ta cigaba da aikinta.

    Bayan anje break daga massalaci Maanal ta dawo kan aikinta, dan tunda tazo companyn bata taɓa zuwa kitchen cin abinci ba. Kullum da abinda zata ci take zuwa daga gida, dan haka bata taɓa maida hankalinta ba. Tana cikin aikin ta samu kira daga head of design office ana nemanta a conference room. Tashi tai ɗauke da drive ɗin data haɗa abinda zata gabatar ta wuce. Batayi mamakin ganin duk manyan companyn a wajen meeting ɗin ba, dan ta fahimci project ɗin nada matuƙar muhimmanci. Sai da ta gaidasu cikin girmamawa sannan ta zauna a kujerar da aka nuna mata. Kusan zaman mintuna biyu sannan CEO ya shigo AS nashi biye da shi. Dukansu miƙewa sukai domin girmamawa, sai da ya zauna a kujerar da AS ya gyara masa sannan yay musu nunin su zauna. Duk zaman sukayi, ita dai Maanal bata yarda ko inda yake ta kalla ba. Sai da Director Steven ya mata magana sannan ta tashi. Kamar waccan ranar yau ma ta gabatar da sabbin zanenta, tare da bayanai akan yanda zai iya kasancewa. Yau ɗin ma dai kowa ya yaba mata matuƙa, dan hatta shi kansa CEO ɗin a mamakinta ya wani zuba mata ido, ita dai kame kanta ta ƙarayi. Tattaunawar ta cigaba da gudana, musamman ta ɓangaren Head of design and engineering da R&D Director da Sales and Marketing Manager sai shi CEO ɗin dake ɗan saka baki. Sun kwashi kusan awa ɗaya da rabi kafin a tashi, yau kam Maanal ita ta fara fitowa daga conference room ɗin tana sauke numfashin gajiya. Har ga ALLAH ta gaji sosai, dan surutun nan na wahalar da ita matuƙa. Kai tsaye elevator ta nufa. Koda ta fito floor ɗinsu sai ta samu anata ƙus-ƙus, bata fahimci ƙus-ƙus ɗin na minene ba sai da ta ƙarasa group ɗinsu. Sama-sama take tsintar gulmar da su Zaharadeen suke suma, wai wata ƙyaƙyƙyawar budurwa ce tazo neman CEO. Sai dai an hanata shigowa kasancewar yana meeting tana a reseption dan tace ko zai kwana a meeting ɗin zata jirasa. Abinda ya kawo gulmace-gulmacen kuwa securitys da suka hanata shigowa taima tas tare da sanar musu cewar basu san matsayinta bane shiyyasa, to itace matar da CEO ɗin zai aura. Wannan furuci nata shine dalilin ƴan ƙananun maganganun dan kowa dai yasan wanene CEO ɗin akan mata. Hatta hoton dake zagaye da duka offices ɗin companyn kowa yayi gulmarsa ya bari dan babu wanda yasan matsayin mai hoton ko sanin wacece ita. Musamman ma daya kasance bawani gane ainahin wanda ke'a hoton ake ba sam. Abinda kowa ya yarda da shi kawai koma wacece tanada muhimmanci a wajensa. Sai kuma ga ita wannan budurwa tazo da sabon zancen daya ɗauki hankalin kowa.
      Shigowar wani abokin aikinsu sai dai ba'a rukuninsu yake ba ya sakasu maida hankali wajensa su duka banda Maanal da kunnenta ne kawai ke wajen. Cikin gulma yake sanar musu gafa shi can AS na CEO yazo ya shiga da budurwar nan da'alama zancen dai gaskiya ne ita ɗin matar da CEO ɗin zai aura ɗin ce. Duka sosai zuciyar Maanal take yi, sai da ta dinga ambaton sunayen ALLAH da sauri-sauri sannan ta ɗan fara jin dai-daituwa. Daga haka taji gaba ɗaya aikin da take yama fita mata a rai........✍️

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖3️⃣3️⃣
Chapter 48 · 0% Book details