← Book details Ajiya A Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 148

Sashe 14

Ajiya A Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

    “Wai Auta bazaki tashi a barcin nan naki ba haka nan. Jibafa lokaci ko kari bakiyi ba, ga ƴan uwanki na jiranki ki rakasu gidan mai gyaran jiki. Suna fara damunki kuma nasan zaki manta da yunwar cikinki ne ku tafi”.
          Kaɗan Maanal ta buɗe idanunta ta ɗan kalla Ammie mai maganar ta maida ta lumshe tare da sake naɗe jikinta waje guda. A yanayin mai barci da yanayin muryarta mai zurfi ta amsa da, “Ammie bana jin daɗi”. Da sauri Ammie ta ajiye abinda ke hannunta ta nufeta. Zama tai a bakin gadon tare da janye duvet ɗin da take a ciki ta ɗaura hannunta a goshinta, da sauri ta janye ta maida a wuyanta. “Ya salam, Manaal kinga tashi muje asibiti jikinki zafi, amma bayan kinyi sallar asubahi ne ma zazzaɓin nan dai?”.
       Hannun Ammien ta riƙo ta rungume a ƙirjinta. Cikin rauni ta furta, “Ammie abinne zai zo, ga kuma ƙirjina yamin nauyi, kwana biyu kenan kullum da safe nake zazzaɓin, shekaran jiya ma da muka taho banda lafiya”.
     Sosai rauni da damuwa suka bayyana a fuskar Ammie. Muryarta har rawa yake wajen furta, “Yaushe ya dawo yimiki kuma Maanal?”.
         “Ammie duka watannin nan da banzo gida ba yanayi. Na ƙarshen nan kwanana uku a hospital ma, hakkin ma ji nake kamar zai dawo”.
    “Ya arrahaman. Amma a watannin nan idan na tambaye ki kuma kita cewa babu damuwa. Haka kika dinga shiga cikin halin nan Manaal amma kina ɓoye min? Shiyyasa tunda naga duk kin sake figewa nasan kin ɓoyemin abubuwa ne. Nikam wannan ciwon naki na tayarmin da hankali, dan ALLAH Maanal ki cirema ranki duk wani abu, itafa rayuwa ɗaya ce, sannan bawa baya kasancewa a cikinta sai da jarabawa dama. Bakiga na haƙura nima na manta komai ba, hakama ƴan uwanki?”.
“ALLAH Ammie babu abinda na sakama raina, kune kuke ganin kamar har yanzu ina riƙe da abubuwa, amma sam ba haka bane ba. Nifa musulma ce, kuma nasan minene rayuwa da ƙaddara. Ki cigaba da min addu'a kawai Ammie”.
“In sha ALLAHU koda yaushe cikin yi muku nake. Kuma Alhamdullah da sauyin rayuwa da UBANGIJI ya bamu mai tazara sosai, idan mukai dubi da baya. Tashi kiyi wanka naima bana maigadi magana ko zamuje wajen mai maganin nan tunda nasa anji daɗinsa”.
           “Amma Ammie shima kuma gashi ya dawo ai”.
    “Duk da haka Manaal, ai kin samu ban iska tunda an samu sassaucin wahalar nan da kike sha kusan na shekaru bakwai”.
         Kanta ta ɗan jinjina cike da damuwa. Dan ita kanta ciwon nan na ɗaga hankalinta, ga shi kusan duk sanda zatai period sai abun ya ƙwaɓe mata da ciwon mara da take fama da shi shima, dan kamar ciwon maran yana zama sanadin tada ciwon zuciyar ne sakamakon tuno mata da abubuwan da suka faru baya da hakan keyi a duk irin lokacin. Har rama take farayi idan akace maka lokacin nan ya matso mata. Dan ita kaɗai tasan irin kalar azabar da take sha a rayuwarta. Duk yanda zata misalta ba lallai a fahimta ba. Shiyyasa idan akace mata haihuwa nada ciwo sai taita mamaki da ganin anya zata kai azabar da take sha a ciwon mara idan zatai period. Itafa nata ma dabanne dana duk wanda ta taɓa sani, ƴan uwanta ma duk sunayin ciwon idan zasuyi prioud ɗin, amma bai kai ko rabin nata ba. Kuma sunayin aure duk suka daina. Ammie tace ita suka gado, dan itama tasha fama har sai da ta haihu sannan. To ita abin nata ya zama biyu ne, ga ciwon zuciya kuma, shiyyasa hankalin kowa ke matuƙar tashi a duk sanda irin haka ya taso musamman akan ita Manaal da nata yafi tsauri.
     Ammie da kanta ta taimaka mata har zuwa bayi bayan ta haɗa mata ruwan zafi. Haka ta daure tayo wankan ta fito sai kuma rawar sanyi. Kasa zaman shafa mai ma tayi ta haye gadon ta sake ƙudundunewa. Dai-dai nan Amaal da Shahidah da Ammie tai kira a waya ta sanar musu suma Baba maigadi magana akan maganin Maanal ɗin dan ɗan uwansa ne ke bata suka shigo ɗakin. Su kansu su Shahidahn duk fuskokinsu sun nuna damuwa. Ƙarasawa sukayi inda Manaal ɗin ke ƙudundune suna mata sannu. Sai kuma Shahidah ta juya ta fita tana faɗin bari na amso maganin dan kamar sallamar Baba maigadin. Ilai kuwa shine, dan babu jimawa ta dawo da magani a gora. Da taimakon Ammie suka bama Maanal ɗin saboda rashin sonta da magani. Tana gama sha kuwa sai amai, dama haka yake mata, sosai tayi aman har ta basu tausayi. Haka suka taimaka mata suka gyara mata jiki ta sake yo wanka ta canja kaya ta koma ta kwanta. Cikin amincin UBANGIJI sai kuma barci mai nauyi sosai yay awan gaba da ita. Ajiyar zuciya suka dinga saki a tare, saboda in sha ALLAHU suna ganin kuma shike nan.
     Barci kuwa tayi sosai, dan bata farka ba sai bayan azhar. Alhamdullah taji daɗin jikin, ta samu ta sake yin wanka Ammie da kanta ta bata abinci, sai da taci sosai dan Ammien nata lallaɓata ga kuma waya da sukai da Nene zata zo gobe in ALLAH ya kaimu ya sake sakata jin daɗi saboda matuƙar son Nene da take a rayuwarta. Ga kuma ƴan uwanta zagaye da ita. Hakkanne ya sake ƙarfafata zuwa bayan la'asar tace suje ta rakasu gidan mai gyaran jikin zata iya. Koda sukace a'a sai Ammie tace suje ai fitar zata saka ta sake jin ƙarfin jikinta ta kuma warware. Da wannan shawarar sukai amfani suka tafi........✍️

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖1️⃣1️⃣

______________

Abubuwan da nake saidawa
Atamfofi
Laces
Shadda
Materials
Takalma
Jakunkuna
Mayafai
Trolley
Sarka da dan kunne
Oil perfumes

Numbers
08034469681
08135142610

Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries

_________
Chapter 14 · 0% Book details